BARKIN'DO part 78-79

1.6K 85 1
                                    

[ 25/10/2018 ]

🌷 *BARKIN'DO*🌷

*[ very interesting story ]*

*Story & Writing - By AUFANA*✍

✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
    *[ ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a kinda lights to reader's }*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW......*✔

  *Page 78~79*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Kimanin wata uku da rasuwar sarki aka fara shagalin bikin su meesha alokacin kuma su MUZAMMIL harsun iya zama ammafa kam akwaisu da fitina sosai,,,...

Wani lokacin idan suka dameta da kuka kuma tana aiki sai tad'akko fillow biyu tamasu goyo dashi taje tacigaba da aikinta suita kuka har bacci yad'aukesu, wani lokacin kuma datamasu wanka take turasu sashen ummi ko sashen hajiya kotabama hadimai mata ahaka harsuka saba yanzu ma basa zama gunta sai idan sunyi kuka akawosu susha nono dasunsha kuma ake wucewa dasu,"....

Yauma kamar kullum Kitchen take tana girki sukuma suna a falour suna wasa saitaji kukan d'aya k'infitowa tai saida tagama aikinta sannan tafito, bayan tafito tad'auki d'aya tafara shayar dashi dikda nono ne abakinsa amma baidaina kukan ba shikuma d'ayan gashi a d'ayan hannunta shima kuma kukan yake nan tarasa yanda zatayi dasu dikansu sunk'i karb'an nono susha balle sudaina kukan,, sakkowa tai ak'asa ta'ajiyesu ak'asa itama ta zauna tai tagumi tana kallonsu,,,...

Kukan suke basu dainaba itakuma tarasa me zatamasu,, norking BARKIN'DO yai har yashigo batasaniba saboda kukan twin's  tsaye yai yana kallon ikon Allah abun nata ga dariya kuma ga ban haushi, duk'awa yai yad'aukesu yafara rarrashinsu saisukai shuu ahankali tad'ago tana kallonsa kallonda tamasa yabashi mugun dariya kamar wata sabuwar marainiya aikwa nan yaiya kyalkyala mata dariya sannan yafita da yaran izuwa sashen hajiya,,,...

          ******  *******

Wata sabuwa inji 'yan ca-ca gidansu gimbiya laila sunzo sunmayarda ita tareda bama mai martaba hak'uri akan abunda yafaru, dole badan yasohakan ba yahak'ura yamaidata saidai Fainus da Marwa har yanzu ba'asan inda sukaiba,"...

BARKIN'DO dasu meesha sam basuji dad'in dawowar gimbiya laila ba saidai sunga sauyi mai yawa agareta dan yanzu har sashen ummi take zuwa kuma idan tanasan abu tanayiwa su meesha magana, yanzukam dikta sauya saidai har yanzu basusake da'itaba saboda sanin halinta dasukayi,,,...

Aranar Thursday ne akai kamun su meesha taro yai taro acan kusa da amare nahango hunayya tasha ado sosai kaman wata budurwa saida kowa yawatse sannan suka dawo cikin gida kasancewar anan ne akayi kamun,, bayan sundawo ne saiga MUDASSIR wata hadima takawoshi ba lafiya sai kuka yake kuma baya rufe bakinsa yawu sai zuba suke,"....

Dasauri hunayya takarb'esa sannan taje tazauna domin tabash nono tana bashi kuma yak'i karb'a tai tai yak'i karb'a, abu kamar wasa saiga bakinsa na zubda jini hankalinta yatashi taisaurin tashi takaisa gun ummi. Nan ummi taduba bakinsa bataga komai ba kankace me jini yab'arke sosai abakinsa sai zuba yake atsorace hunayya takira BARKIN'DO yazo shima yanaganin hakan hankalinsa yatashi dasauri suka d'aukesa akawuce hospital,, dazuwansu kuwa bawani b'ata lokaci akashiga dashi theater hunayya dikta rikice ta rud'e sai kuka take saida BARKIN'DO yarik'eta saboda yanda ta tada hankalinta MUZAMMIL ma kasa rik'onsa tai sai meerah tarik'esa,"...

Saikusan 10:00pm sannan aka gama aka fito dashi d'akin hutu nan Doctor d'in yakira BARKIN'DO office d'insa yana masa bayani,, sunyi aiki dakyar suka ciro abunda yake a bakinsa wani k'arfe ne sukagani acan k'asan harshensa wanda sunyi matuk'ar mamaki sosai kuma dik wanda yai wannan mugun abun to tabbas bashida imani kokad'an k'aramin yaro wanda bashida zinibi bashida laifin kowa saina mahaifiyarsa,, hmm Allah dai yak'ara ahiryardamu ameeen,,,...

BARKIN'DO Where stories live. Discover now