[ 12/9/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®
*[ onward together ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a Kinda lights to readers}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔*Page 25~26*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ahankali yak'arasa ciki sannan yazauna daidai kanta,,ahankali yaduk'o daidai kunnenta cikin tattausar murya mai kama da rad'a yafara mata magana ""Jasmine d'ina tashi muyi fira kinji"" jin dadda d'ar muryarda ko Acikin bacci tajita tasan ko tawace yasa tad'ago ahankali cakk tahad'a ido dashi dasauri ta d'auke idonta akan nasa sannan ta tashi zaune,,,...
Kallonta yake cikin tausayi kwana d'aya kacal amma dikta rame tayi bak'i dara daran idanunta sun canja launi izuwa ja saboda tsananin kukanda tasha tabbas rashin mahaifi bak'aramin bak'in ciki neba,,ahankali yagyara zamansa sannan yakalleta cikin tausayi ""Jasmine dan Allah kirage wannan damuwar kada kijawowa kanki wata matsalar musamman rashin cin abincinki dan Allah kidaure ko kad'an ne kici wallahi Sam banajin dad'in ganinki cikin damuwa kidaure ko kad'an ne kici kinji my Jasmine"" kallonsa kawai take har yagama maganarda yake batace uffan ba saima kwallarda ke zuba daga idanunta ganin haka yasa yatashi yafita Jim kad'an saigashi yadawo hannunsa rik'e da plate na abinci da gorar ruwa,, zama yai akusa da ita sannan yad'ibi abincin da hannunsa yakaima abaki sai tajuya fuskarta tak'i kar'ba 'bata fuskarsa yai yanda yara keyi idan zasuyi kuka shima shi yai zuwa kuka, abun dariya yabata harsaida tad'anyi murmushi ganinshi babba amma yana abun yara,shima murmushin yai sannan yamik'amata abincin batakoyi musu ba takar'ba,, taci saidai ba sosai ba sannan tasha ruwa,'...
Yaumadai sai kusan 8:15pm sannan su BARKIN'DO suka baro rugarsu hunayya, around 11:00pm suka iso gida yauma dai Marwa shuru ba ita ba labarinta haka yai shirin baccinsa ya kwanta,'...
Da asuba bayan yadawo daga masallaci yakoma gado yacigaba da baccinsa saikusan 9:30am sannan yafarka, yana farkawa yashiga toilet wanka yai sannan yafito yashirya cikin ciga maid'aukan hankali farar shadda ce galila mai tsadar gaske riga da wando dakuma babbar riga wacca tasha aikin hannu bak'i sai takalma rufaffi suma bak'ak'e da hula bak'a, yai matuk'ar kyau abunka da bafulatanin mutum kyakkawa k'irar maza sai kayan suka kar'besa sosai,,falour yafito sai zuba uban k'amshi yake,koda yafito yatararda hadimai sun kammala masa breakfast nan yazauna cikin sauri yayi break d'in yanagamawa yashuri Keys d'in motarsa yafita,,d'akin humair yawuce haryanzu yana nan yana sharan baccinsa aifa nan yadinga damunsa harsaida yatashi yashiga toilet, wanka yai sannan yafito yana fitowa yai tsaye cakk yana kallon BARKIN'DO cikin mamaki murmushi BARKIN'DO yai sannan yace "malam lafiya ka k'ureni da ido kamar yau kafara ganina" dariya humair ya kyalkyale da ita sannan yace ""wallahi a iya rayuwarmu zan iya k'irge adadin kwanakinda kata'ba rangad'a ado irin wannan,kaganka wai ko ranar d'aurin aurenka da sarauniya bakai irin wannan adon ba kuma kanasane da gidan makoki zamuje ba gidan biki ba,gaskiya d'anuwa yakamata kaje ka canja wannan wankan is too much gaskiya"" kallonsa kawai yake har yagama surutunsa "Malam kashirya muwuce dan Allah kana 'bata mana lokaci" hmm...!!! kawai humair yace nan shima yashirya sannan suka fito,,cikin gida suka wuce sukai barka da safiya sannan suka fita, yauma dai kamar jiya kowa tashi motar yashiga sannan suka kama hanyar rugarsu hunayya,'....
Yauma kamar jiya saida BARKIN'DO yayi siyayyar abinci kala kala buhu buhu catin catin na taliya da dai sauransu sannan suka wuce,,,...
Around 12:00pm suka isa nan BARKIN'DO yasaka aka dinga jidar buhu buhu na shinkafa da sauran kayanda sukazo dasu ana shiga dasu cikin gida aikwa Abba modibbo sai faman godiya yake yana sanyawa BARKIN'DO albarka, bayan angama sannan suka zauna zaman makoki,, kimanin 2:30pm bayan sun dawo daga sallar azahar BARKIN'DO yasaka aka kira masa Abba modibbo yanasan suyi magana,'..
BARKIN'DO na zaune akan tabarma Abba modibbo yai sallama sannan ya zauna cikin sakin fuska nan suka k'ara gaisawa BARKIN'DO ya d'an duk'arda kansa k'asa alamar ladabi ahankali yafara magana cikin tsintsar biyayya ""Abba dama nakiraka ne domin muyi magana akan Ni dakuma Hunayya"" to yarima inajinka meke faruwa ne..?" ""murmushi yai yace ah lafiya k'alau daman tin Abba na nan akwai alk'awarin aure atsakaninmu munyi magana dashi akan bayan angama bikina da Marwa zaayi namu da Hunayya to saikuma wannan k'addar tazo ta afku shine bakeso dan Allah idan ba damuwa anjima idan anrufe zaman makokinnan kamin a watse sai ad'aura aurenmu"" hmm...!!! Yarima dik nasan da zancenda kukayi saboda d'anuwana baya 'boyeman komai nasa kamar yanda nima bana 'boyemasa komai nawa kuma naji dad'in hakan sosai saidai yarima zaka iya auren 'BINGEL kuwa kaga ita yarinyace k'arama mai k'arancin shekaru sannan koda ma ace auren zaayi yakamata kad'an bamu lokaci saboda mu shirya ""Abba dik ka daina wannan zancen batun k'arancin shekarunta ai ni naganta nace inasanta ba ita taganni tace tanasona ba,ina kwad'ayin auren hunayya ne saboda nasharemata hawayenta dake zuba inada burin maye mata gurbin iyayenta nayi alk'awarin zamemata uwa,uba,dakuma yaya insha Allah, sannan batun shiri kuma karka damu ni nashirya komai tin daga kan sitirarta ta sakawa har izuwa makwancinta komai na shirya buk'atata kawai ku amince"" shikenan yarima na amince Allah yabaka ikon rik'on amana yabaku zaman lafiya ya kareku daga sharrin shaid'an la'anannen Allah nan suka amsa da ameen,'....
Around 3:30pm aka rufe zaman makokin Abba Baffajo Allah sarki rayuwa kenan ubangiji kasa mucika da imani ameen, bayan anyi ardu'oi izuwa ga marigayi Baffajo sannan aka d'aura auren BARKIN'DO da hunayya akan sadaki mafi tsoka naira dubu hamsin tareda raba alawa da dabino,d'aurin aurenenda yasami shaidar mutane da dama ciki kuwa harda limamin rugar bayan angama d'aurin auren ne su BARKIN'DO suka kama hanyar gida BARKIN'DO cike da farinciki da jin dad'i,'..
Saidai fa dik wainarda ake toyawa Hunayya bata saniba hakama su Inna basu saniba.......
🏃♀🏃♀'''muje zuwa '''
'''AUFANA for life '''🌷🌷
*I.W.A*🖊