BARKIN'DO part 76-77

1.6K 88 0
                                    

[ 24/10/2018 ]

🌷 *BARKIN'DO*🌷

*[ very interesting story ]*

*Story & Writing - By AUFANA*✍

✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
     *[ ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a kinda lights to readers }*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW......*✔

  *Page 76~77*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Dasafe bayan yayiwa yaran wanka hunayya ma tayi sarki ya'aiko abashi twin's suyi fira meesha dariya tai tace "sarkifa naji da yarannan nashi" bayan angama shiryamasu sannan meesha tad'aukesu takaimasa,,,...

Kwance take tana hutawa falon nata kuma cike yake dake da mutane aunty salma ma tazo tana zaune kusa daita tanamata fad'a batasan cin abinci yanzuma farfesun kayan ciki ne tamata amma ko rabinsu bataciba "haka ake jego hunayya ciki baicikaba taya yaran suma zasusami isahsshen ruwan nonon dazasusha bafa yaro d'aya bane biyu wallahi kimaida hankalinki idanbahaka ba kuma su zasuyi k'iba kekuma kiyita ramewa, maza tashi ki k'arasa cinyesa sannan kishan kunu" b'ata fuska tai sannan ta tashi takarb'a tacigaba da ci, batako k'arasaba kuwa saigasu anmayardasu suna kuka wata uwar harara tawatsa masu su dakuma meerah dake d'aukedasu meerah kam mezatayi banda dariya "aikinga abunda nake fad'amaki kuma yanzu kikafara gani wallahi gwarama ki mayarda hankalinki kisan kugirka" cewar Aunty salma. Batareda ta cinye farfesunba ta tashi tawanke hannunta tasha ruwa sannan tazauna Aunty salma tamik'o mata d'ayan takarb'a, dakyar taciro nonon daga brez d'inta saboda cikardasukai gashi kuma rigar tamatseta nan takai masa abaki yanakai bakinsa yacafka yafara tsotsa dasauri tacire nonon tana zaro idanu kallonta Aunty salma tai sannan tace "ke lafiya miye haka...?"  shagwab'e fuska tai kamar zatayi kuka "Aunty wallahi zafi naji" dariya abun nata yabata kamar takyakyata saikuma tasha kunu saboda tasan halin yarintar hunayya "ahaka zakiyi hak'uri kuwa harsu k'oshi maza bashi abunshi yasha malama" bayanda ta'iya saboda taga fuskar Auntyn tata bawasa haka tasake kaimasa abaki shikwa yaron yacafki abunsa yacigaba da tsotsa,, nikwa nace yaro yiabunka gada kayi agun gyatuminka hhh Lol, "....

Haka yacigaba da tsotsa tanata faman rintsar idanu kaman tai kuka saboda zafin tsotsar datakeji, bayan yasha sannan aka karb'eshi aka bata d'ayan tacigaba da bashi shima amma saida tacanja masa d'ayan nonon,,,...

Aranar ummi tace amaida hunayya sashen hajiya saboda rawar kan da BARKIN'DO keyi kar aje ayi abun kunya, kai BARKIN'DO bakada dama wallahi harda jegon kuma bazaka hak'uraba hhh Lol,, kwana hud'u da haihuwa mutan masarautar RUGA suka k'araso inn da Abba modibbo k'awar hunayya kwaine da 'yan uwan mahaifiyar ta sai 'yan uwan su Abba mata biyu. Aranar farinciki agun hunayya baya misaltuwa saboda tai missing 'yanuwanta sosai musamman k'awarta kwaine nan kwaine taita bata labarin abubuwan arzikinda BARKIN'DO yamasu a rugarsu wad'anda suka matuk'ar bata mamaki saboda kosau d'aya baitab'a fad'amata ba yacimakata alk'awarinda yai lokacinda yaganta yanaso kuma yace zai aureta, yasaka anmasu titi har cikin rugarsu ko'ina anyi titi sannan yaginamasu makaranta ta primary da secondry  wacca ke had'e da islamiyya yanzukam ilimi saidai idan bakasan yi sannan dik wani haraji da ake karb'a ahannunsu Abba yanzu andaina yahana kuma yahana zakkarda suke badawa idan sunyi noma yahana ladar shekara da mata kekaiwa amasarauta ta tatacciyar zuma nono dakuma madara, dikdai wani zalinci da'ake masu a da yanzu andainasa yanzukam rayuwa suke mai cike da jin dad'i kamar yanda mutanen kowacce masarauta suke rayuwa ba takura yanzuma har sunfi wata masarautar,,,...

Murna da farinciki sunhana hunayya cewa komai saima kwallan farinciki datake zubarwa nantak'ara tabbatarda lallai tai sa'ar miji sosai irin mijindakeda wuyar samu a wannan zamanin,, batak'ara tsinkewa ba saida taje gaidasu Abba taga irin sitirardake sanye ajikinsu dakuma su kansu yanda sukai fresh bakamar da ba, bayan tagaidasu tamasu sannu da zuwa ya hanya nantazauna sunad'an tab'a fira anan ne inna ke k'ara fad'amata irin alkairanda BARKIN'DO ke turamasu tareda cewa tamasu godiya idan yashigo suma zasuyi masa sannan tak'ara damata hud'ubu irinta uwa da y'a akan tabimijinta tacigaba da masa biyayya Allah yabasu zaman lafiya yak'ara had'a kawunansu ameeen,"....

BARKIN'DO Where stories live. Discover now