[ 15/9/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
*[onward together]*
*{we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a kinda lights to readers }*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔*Page 29~30*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Tinda Abba yafad'awa su Inna nanfa Inna tasaka hunayya agaba da gyara ajik'amata wannan a dafa mata wannan,,,..
Kasuwa Inna ta aika aka siyo mata cigeder geder da budurwar kaza sai man kad'e da garin bagaruwa had'e da 'ya'yanta kasancewar sunada man shanu wanda aka tatsa ga saniyar hunayya,,bayan komai yahad'u sai tafara shirin had'a kazar cikin k'ank'anen lokaci kuwa tagama had'ad'd'iyar kazar amare wacca taji man shanu man kad'e cigeder geder garin bagaruwa da dai sauran kayan mata,ana gamawa Inna tasaka hunayya agaba dan taci kazar aikuwa dakyar taci rabinta shima saida tamata jajayen idanu wai ba dad'i,bayan tagama ci tasakata tai wankan lalle lallen hausa fa toh bayan yai wanka sannan tahad'amata ruwan bagaruwa dana lallen hausa tai tsarki daganan kuma sai ta tsefe mata sumarta dikda hunayya akwai tsabta tana kula da kanta sosai amma saida Inna ta wanke sumar tass sannan ta shafeta da man kad'e da man shanu kasancewar su a rugar man kad'e da man shanu sune mayukansu na shafawa dana kitso aikuwa nantake sumar tafara kamshin mayukan,,cikin k'ank'anen lokaci hunayya ta sauya kamar ba ita bace tai kyau sosai daka ganta kasan amarya ce, Lalle Inna tasaka aka mata ja woww zo kuga yanda tsintsar kyau ke bayyana a inda yadace ya bayyana hunayya sai shek'i take dikda k'aramin jikinta dakuma k'ananun shekarunta amma hakan bai hana bayyanar tsintsar kyan halittarta ba,'..
Iyaye mata musani mudaina d'urawa 'ya'yanmu magungunan mata alokacin aurensu wallahi hakan cutardasu mukeyi bcoz indai yarinya budurwa ce to bata buk'atar wasu magunguna ita kanta magani ce akwai matanda Allah ya halitta da ni'ima to idan ba'abarta da iya ni'imarta ba aka k'ara mata da wasu zata iya hallaka bcoz namiji bashida tausayi balle hak'uri musamman a first night,alokacin baya cikin hayyacinsa fa kinga idan ni'imar tamata yawa zai iya hallaka ta saboda haka dan Allah koda zamu basu muyi sese - sese,,sannan musani lallen hausa Yafi komai amfani ajikin 'ya mace musamman budurwa kuma amarya da zamu dinga amfani dashi da munga banbancin mai tarin yawa fiye dana dilka da kurkur ai iyayenmu lallen hausa aka masu gyara dashi ba dilka da kurkur ba Allah yabamu ikon amfani da shawar wari ameen
Daya daga cikin d'inkunanda BARKIN'DO yamata tasaka hmm zo kuga kyakkawar halitta, tai matuk'ar kyau kamar ita tai kanta kai kamar ka d'auketa ka gudu,, around 12:30pm su humair suka iso rugar da wasu had'ad'd'u dalla dallan motoci guda uku bak'ak'e wulik sai shining suke, humair acikin d'aya wacca tafi kwacce kyau sai kuma drivers biyu wad'anda suka tuk'o sauran,,,...
'yar walima humair yasaka akayi wacca tabirge mutan rugar bayan ansha wa'azi sannan aka raba abinci kala kala harda naman rago had'e da Juice da ruwan kwalba,bayan angama kowa ya watse sai sanyawa auren akbarka ake mafi yawa kuma sai yabon kyakkyawan halin BARKIN'DO suke wasu kuma na zagin Abba da hunayya wai kwad'ayine yasa suka ta mak'alemasa had'e da bin bokayi shiyasa har sukai sa'a ya aureta to adaibi ahankali indai kwad'ayine,hmm d'an adam baka iya masa,'...
Bayan angama komai aka fara shirin tafiya nan Abba yatsara yanda za'ayi tafiyar cikin hikima mutum biyu acikin dangin mahaifiyarta hakama mutum biyu daga dangin mahaifinta sai k'awayenta biyu kubrah da kwaine,tsarin yayiwa kowa saboda yakamata kam asan masaukinta bawai kawai abashi ita su tafi ba batareda kowa yasan inda yakaita ba,,bayan kowa ya kimtsa za'a wuce ne sai Abba da Inna suka saka hunayya agaba suna mata hud'ubar zaman aure aikwa hunayya sai kuka take dakyar akarabata da jikin Inna sannan aka sakata a mota suka kama hanyar masarautar JAMNAZ iyayen hunayya sai zuba k'auyanci suke acikin mota wai sunji sanyin AC hhh Lol,'....
Kasancewar basu taso da wuri ba yasa sukai dare sai kusan 8:30pm sannan suka iso masarautar JAMNAZ direct gidan ta suka wuce bayan sun iso ne humair yakira BARKIN'DO a waya ya shaida masa isowarsu,,hmm zo kuga aljannar duniyar da aka zubawa gidan ai tsaye nai nasake baki da ido harda hanci ina kallo saida mommo na *SAINAH* ummun meenal tace "dota rufe bakin hakanan sannan nai murmushi nashiga ciki domin d'auko maku rahoto,,humair ya bud'e k'ofar gidan sannan suka shiga nan nima nabi bayansu,,tsarin gidan yayi sosai 3bedrooms ne sai 2 falours kitchen d'aya anzubawa gidan kaya sosai komai ansaka babu ne kawai babu kuma komai anyi Mach colour Porpple and White colour ne,,d'akinta aka wuce da ita anan aka barta tareda k'awayenta sukuma iyayenta aka wuce dasu nasu d'akin nanfa suka dinga zuba uban gida danci su ta'ba wannan su latsa wancan,'...
Around 10:00pm BARKIN'DO yashigo koda yashigo kuwa hunayya da k'awayenta na kwance ak'asa suna ganin BARKIN'DO kuwa sukai saurin tashi suka gaida shi sannan suka fita,binsu tai da kallo sannan tace ""to ina zaku kuma ku barni"" basu ko tsayaba balle su kar'bamata, suna fita BARKIN'DO yarufe k'ofar nan gabanta yafad'i dimm....!!! a tsorace ta tashi tsaye amma sai takasa cemasa komai kuma sai kallonshi kawai take,,cikin murmushi yafara takowa ahankali izuwa gareta nan tafara ja dabaya ahaka har ya datseta da gado da sauri ta runtse idanunta cikin tsoro da fargaba,dariya yai tareda fad'in "Matsoraciya to bud'e idon koh" ahankali ta bud'e idanunta taganshi tsaye agabanta yana murmushi hannunta ya rik'a suka zauna sannan ya kalleta cikin murmushi yace ""meyasa kike tsorona ??"" shuru tai batace komai ba "ko kinfara mantawa dani ne kokuma kin daina so na ne" d'agowa tai takallesa tai murmushi amma batace komai ba "Côme on my Jasmine nine fa yarimanki pleace ki saki jikinki mana" kallonsa tasake yi sannan tace yariman Marwa dai,,jin abunda tafad'a nan take walwalarsa ta sauya can kuma ko meyatina saikuma yai murmushi sannan yatashi tareda mik'arda ita tsaye,, toilet suka shiga sukayo Alwala sannan suka fito nan yajasu sukai sallah raka'a biyu bayan sun gama ne yadafa goshinta yamata wata addu'ah mai d'an tsayi ganin tafara jin bacci harda lushi da idanu alamun dai baccin yazo yasa yakora masu da wasu addu'oin sannan suka shafa,,tanajin bacci amma kuma takasa hawan gado ta kwanta shikuwa baima kula da abunda take nufi ba nan yajanyo wata leda daya shigo da ita ya bud'e yace taci nanfa tace bazata ci ba ita a zatonta irin wacca Inna tai mata ce agida dan haka bazata ci ba yai yai tak'i ci dan haka yakyaleta,'...
Bacci takeji sosai amma tsoro da fargaba tahanata hawan gado ta kwanta BARKIN'DO ya lura da yanayin da take dan haka dakansa ya d'auketa izuwa ya kwantarda ita aifa nan tasaka masa ihu ba shiri ya sauketa sannan yace kwanta kiyi bacci toh ina ai wallahi takasa hawan gadon jikinta 'bari yake sosai zuciyarta sai dukan uku uku take ganindai babu sarki sai Allah yasa takwanta ak'asa ammafa dik ta k'udundune jikinta kamar maijin sanyi shi abun nata ma har dariya take bashi shareta yai, bacci 'barawo batasan lokacinda ya saceta ba,,wanka yashiga yai sannan yafito yacanja kaya izuwa na bacci sannan yakashe fitilar d'akin nan yazagayo ahankali ya d'auketa yamayar a kan gado sannan shima yahau gadon,'...
Ahankali yafara ciremata kayan dake jikinta tin wad'anda aka kawota dasu ne bata canja ba,,kamar amafarki takejin ana rabata da kayan jikinta.......
🏃♀🏃♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life '''🌷🌷
*I.W.A*🖊