BARKIN'DO part 13-14

1.8K 126 0
                                    

[12/8/2018]

🌷 *BARKIN'DO*🌷

*[ Very interesting story ]*

*Story & Writing - By AUFANA*✍

✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚®
       *{onward togather}*

*Page 13~14*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

K'arfe 4:00pm zasu wuce hakan yasa tin 10:00am akafara shirye shiryen tafiyarsu
Nan BARKIN'DO yasaci hanya yawuce rugarsu Hunayya domin suyi bankwana,, baisaniba ashe hadimin Marwa wanda tasaka yamata bincikensa yanataredashi amma sam baisaniba kasancewar Sam baibari yasan shi yake bibiya ba,'....

Tafiya yake yana gaisawa da mutanen rugar kasancewar yasaba da mutane, sosai har yak'arasa gidansu Hunayya yaron yana bibiyarsa,,,....

Baiwanijima sosai ba yafito saboda yasan ananiransa,bayan yafito ne hunayya tafito domin yimasa rakiya,, tafiya suke gwanin birgewa sunashan firarsu mai dad'i saidai fa itakam tacemasa kunya takeji dariya yai yace ""aikuwa yau saikin rakani har fada""  zaro idanu tai tace kacedai nakai kaina k'abari idan marwa taganni dakai ai wallahi Allah ne kad'ai yasan abunda zataman,, 'bata rai Jin ta ambaci sunan marwa ta kula da hakan danhaka takawar da zancen,,sunyi nisa sunatafiya ganin akwai nisa sosai kamin takai gida yasa yace takoma hakanan kud'i yaciro masu yawa habata amma tak'i kar'ba yaiyai tak'i kar'ba saida yajefardasu nan yajuya sannan tad'auka,, hartajuya tafara tafiya yakira sunanta tajuyo yace ""my hunayya I love you very much I love you with all my hert,, inasanki sosai ki kulaman da kanki har izuwa lokacinda zan dawo gareki""  dikda batajin yarenda yamata amma sai tai k'ok'ari tahad'asu da hausarda yamata nantake tafahimci abunda yacemata murmushi tai tace ""karka damu zanyi yanda kace insha Allah ubangiji yamaidakai lafiya kuma nima Inasanka sosai""  tanafad'ar haka tajuya tawuce da gudu wai taji kunya hhh Lol""  dariya yai cikin jin dad'i yajuya yawuce cikin tsananin farinciki, '...

Suna wucewa hadimindake bibiyarsa yafito daga ma'boyarsa yana jinjina kai Alamundai yaji dikkanin zancensu,juyawa yai yawuce abunsa,,,.....

Dazuwansa yawuce yasake wanka yacanja kaya izuwa shigar manyan sarakuna hhh sarautar ta motsa kenan,, Shiga yai ta azo agani mai tsantsar birgewa dakagansa kasan jinin sarauta ne,, bayan yashirya yafito dayake kowa yashirya fada sukawuce akayi bankwana sarki yamasu godiya tareda fatan sauka lafiya hmm su Marwa saiwani zak'ewa BARKIN'DO take ganin yanad'an sakemata fuska azatonsu aikin boka ne yafara aiki hmm Allah yashiryardamu ameen,'....

Har gun motoci sarki da iyalansa suka rakasu saida motocinsu suka tashi sannan suka koma gida,,,...

Tafiyarsu BARKIN'DO da kimanin 1hour saiga hadimin nan dake bibiyar BARKIN'DO yazo lambun Marwa yawuce kaitsaye kasancewar a irin wannan yanayi ne take shan iska,, a zaune take hadimanta namata fifita amma tanaganinsa atafe tai saurin tashi a tsaye,, k'arasowa yai ya durk'usa akasa sannan yace ""Allah ya jima da ran sarauniya yaudai naganomaki gaskiyar abunda ke kai yarima gidansu 'BINGEL""  cikin zak'ura tace kafad'aman inajinka  ""Allah yahuci zuciyar sarauniya tabbas yarima soyayya yake da 'BINGEL saboda agabana yau yafurta mata kalmar So itama tafurtamas.....""   baik'arasa ba tacakumo rigarsa cikin tsananin masifa dik ta firfito da idanuwanta a waje tace ""ka tabbatarda abinda kafad'aman gaskiya ne""   yanayin shak'arda tamasa yasa yakasa magana ganin haka yasa dole tasakesa sannan tace ""kaje kakiraman bahago sannan kacemasa yazoman da k'arfafan hadimai guda takwas maza kuma yazo da bulalarsa ta jikin dorina maza yai sauri inajiransa""  dasauri yatashi yawuce baifi 10minutes da fita ba saigasu kuwa sunzo saifaman huci suke kamar zaki idan yanajin yinwa,, kubiyoni kawai tacemasu tashiga gaba suna binbayanta,'....

BARKIN'DO Where stories live. Discover now