[ 12/10/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
*[ ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ ]*
*{ we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious And dropping a kinda lights to readers}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel
*Page 58~59*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Suna fita sai sukabi ta bayan sashen hajiya izuwa lambun mai martaba inda yake shan iska da maraice, waige waige suke saboda karsu had'u da jakadiyar gimbiya laila kwatsam saisukayi kicib'is da marwa tafiya take tana danne dannen waya,, d'agowarda zatayi saisukayi kicib'is da kyakkawar fuskar hunayya,'...
Zazzaro idanu tai tareda nunata da yatsa sannan tace "ke meya kawoki anan....??" ja da baya hunayya tafarayi fuskarta cike da tsaintsar tsoro. Ganin haka yasa marwa tai saurin cafko wuyan rigarta cikin tsintsar masifa "ke bakiji me nace bane dan ubanki" yanayin shak'arda tamata yasa tabuga k'ara mai sauti meesha kasa abunyi tai nan tawuce da gudu ta shadawa BARKIN'DO abunda ake ciki,, isowar BARKIN'DO yai dai dai da marwa ta d'aga hannu zata shararawa hunayya mari saboda haushi da takaicin k'in bata amsar tambayarta da tai. Da sauri yarik'e hannunta tareda jan hunayya izuwa bayansa aikwa saboda tsananin kid'ima da tashin hankalinda take ciki batasan lokacinda ta rungumeshi ta baya ba, huci marwa keyi tamkar kumurcin maciji saboda tsananin masifa wani mugun kallo yamata sannan yace "malama lafiya zaki dakar man mata uwar y'ay'ana to bari kiji wallahi idan kika kuskura hannunki yatab'a fuskarta sainamaki abunda har kimutu bazaki manta dani ba wawiya shashasha mara hankali" kalmarda yafad'a ta matata ita ta tabbatarmata da abunda take zargi. Kutumar ubannan yarima kana nufin B'INGEL matarkace, "tabbas kuwa matata ce kuma uwar y'ay'ana insha Allah..." ai baik'arasa fad'aba tai Kukan kura zata cafko hunayya daga bayansa da sauri yarik'eta tareda watsa mata mari har biyu, dafe wajen tai sannan tace "yarima ni zaka mara akan baiwa mara gata k'ask'antacciya to wallahi bara kaji kayi shirin tarban masifa da balai wanda bashida k'arshe tinda nataso a gidanmu mahaifiyata ita kad'aitake agun mahaifina dan haka wallahi nima nikad'ai zan zauna dakai danni kad'ai aka halicceka danni kad'ai kazo duniya dole dole ka saketa dole tabar gidannan ko nakasheta wallahi" ke shashasha dakata jahila mara ilimi to bara kiji karki k'ara kiran matata da baiwa k'ask'antacciya idan bahaka ba yanzunnan sai nai k'asa k'asa dake wallahi kuma daga yanzu dik abinda yasami matata to kece kuma wallahi zan iya d'aukan kowanne mataki kuma agun kowa saboda kare hak'k'in uwar y'ay'ana. Yana fad'ar haka yaja hannun hunayya suka wuce meesha tabi bayansu,'.....
Wani mugun kallo marwa ke masu ji take kamar ta kashe hunayya saboda tsabar takaici da haushi,kuka tafashe dashi tareda dafe hab'arta tawuce sashen mama. Tana isa mama taganta nantake itama hankalinta ya tashi nan tashiga tambayarta abunda ke faruwa kasa fad'amata tai saboda sheshekar kukanda take saida tad'an sassauta sannan gimbiya laila tasake tambayarta nantafad'amata abunda ke faruwa "kan ubannan wato wannan yarinyar danakegani agidannan ba k'awarsu meerah bace k'arya sukayi aikuwa yau za'ayita tak'are lallai yarima yacika cikakken butulu yanzune lokacinda yadace mununamasa kuskurensa karki damu daina kuka tashi muje fada naji idan shi mai martaba ke d'aurenasa gindin wulak'antaki" tashi tai tana sharan kwallah suka wuce fada,,,...
Dashigarsu kuwa batajira komai ba tafara balbalin masifa "yaudai asiri yatonu abunda aka jima ana b'oyewa dankarmusani to yanzu munsani saura naji daga gareka" kallonta mai martaba yai cikin rashin fahimta "gimbiya laila mekike nufi banfahimceki ba" inasone nasan ko da'amincewarka ne akewulak'antarda y'ar y'ar'uwarka shinwai ko dasaninka ne BARKIN'DO ke yanda yagadama a gidannan. "har yanzu gimbiya ban fahimceki ba kifito fili kiman cikakken bayani nafahimta" BARKIN'DO yasake wani auren na biyu kuma saboda tsabar wulak'anci yarasa wadda zai aura sai baiwar Marwa mai mata hidima itace wannan yarinyar dasu meesha kezuwa da'ita gidannan a matsayin k'awarsu saboda tsabar rainin wayo,, jin kalmar k'ara aure da mai martaba yaji yasa ya mik'e daga kishingid'enda yai cikin tsananin b'acin rai "k'arin aure" kalmar yasake maimaitawa cike da mamaki "yanzu Abdul har yayi girmanda zai aiwatarda abu batareda sanina ba" to ai yanzukam dai kagani kuma kaji aini da harnad'auka kasani kyalemu ne kawai kayi. Hmm...!!! yanisa "bakomai ba laifinsa bane amma nasan abunyi" d'aya dagacikin hadimandake kula da fada yakira yace yaje yakiramasa ummi da BARKIN'DO suzo yana nemansu yanzu nan a fada,,,...
Koda sak'on yaisarwa ummi innalillahi wa'inna ilaihi rajiun tafad'a acikin zuciyarta sannan taceda d'an aiken gatanan zuwa,, mai martaba na tsaye a tsakiyar fada sai kai kawo yake acikin fada mama da marwa kuma suna zauna akan kujera, sallama ummi tai cikin nutsuwa sannan tashigo tsaye tai a bayan mai martaba sannan tace "gani nazo domin karb'a kiranka" ahankali yajuyo fuskarsa a murtuk'e bako alamun fara'ah a tattare dashi kallonta yai sannan yace "gimbiya jiddah dik irin abunda kuke k'ullawa ke dakuma d'anki yazo yasameni wato har kunyi kwarinda zaku aiwatarda hukunci batareda sanina ba" kallon mamaki tai masa saboda sam bata fahimci ma meyake nufi ba balle tasan amsarda zata bashi ""mai martaba banfahimci me kake nufi b.... batako k'arasa ba gimbiya laila tai saurin cewa. "Munafuncinda kuke k'ullawa ke da y'ay'anki kin d'aurewa BARKIN'DO gindi yak'aro aure dankawai bakyason marwa y'aruwarsa kintsaneta baki k'aunarta kinrasa yanda zakiyi da'ita shiyasa kikasakashi ya auromata baiwarta saboda kicire haushinta dakikeji" murmushi ummi tai takasa cewa komai saboda tasan ayanzu kotai magana ba yarda mai martaba zaiyiba dama laifin d'a na uwarsa ne,'...
Shuru mai martaba yai kamin yace "ina shi Abdul yake koyafi k'arfin karb'a kiranda namasa ne "aa baifi k'arfi ba yawuce gidansa ne da matarsa" gidansa mai martaba yasake maimaita kalmar "EH" ummi tafad'a baisake cewa komaiba yajuya yashiga d'akinsa yafito. Wayarsa ce yad'akko nantake yai dialing number d'in humair yana d'agawa baijira yace komaiba yace "humair dik inda kake kazo yanzinnan ina jiranka" yana fad'ar haka yakashe wayar,, dikda BARKIN'DO yashaida masa abunda ke faruwa amma sam baid'auka abun yai zafi har haka ba dama irin wannan rana ne yakeyiwa BARKIN'DO gudun tazo saboda yatabbatarda idan tazo bazatazo da dad'iba saidai yaga shi sam baiwani damuba,'...
Humair na isowa nan mai martaba yasaka a gaba dik saida yabashi labarin komai tin had'uwar BARKIN'DO da hunayya har izuwa aurensu. Tabbas zuciyarsa tad'an raunana saidai kuma a fili yanuna sab'anin hakan nan yace humair yashirya suje can gidanda hunayya take,, mota uku sukacika dan harda ummi dasu meesha mama da marwa jakadiya da sarkin gida sai shugaban tafiyar mai martaba,,,...
******* *******
Zaune suke yana rarraahinta saboda har yanzu takasa kwantarda hankalinta sai kuka take tanacemasa yamaidata gida kada marwa tamata illa marwa muguwace karta illata mata dangi bataso laifinta yashafi danginta saboda marwa batada imani dik abinda tafad'a kuma tai alk'awari saita aiwatardashi,, rarraahinta yake cikin salon so dakuma k'auna tayanda zata kwantarda hankalinta,,,....
Norking d'in k'ofa sukaji anayi dasauri cikin tsoro dakuma fargaba hunayya ta mik'e tsaye ta lab'e a bayan BARKIN'DO jikinta har b'ari yake saboda tsananin tsoro.......
🏃🏻♀🏃🏻♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life '''🌷🌷
*I. W. A*🖊