BARKIN'DO part 68-69

1.4K 94 0
                                    

[ 19/10/2018 ]

🌷 *BARKIN'DO*🌷

*[ very interesting story ]*

*Story & Writing - By AUFANA*✍

✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
     *[ ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a kinda lights to reader's }*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

*Page 68~69*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Yau saura exam d'aya su hunayya su kammala saidai har yanzu batajin dad'in jikinta maneje kawai take saboda batasan tarasa exam d'inta, hakan yasa take daddagewa wajen bada himma da nuna gwazo dan tafito da sakamako mai kyau,,,...

Yauma dai kamar kullum kwance take akan kujera ga tarin littafai agefenta kamar amafarki taji muryan BARKIN'DO yana shigowa yana kiran sunanta.jasmine..! Jasmine..!! My jasmine...!!! da sauri tamik'e tsaye tafita a k'ofar shigowa sukaci karo da juna aikwa cikin murna ta rungumeshi shima cikin farinciki ya d'agata sama yana dariya, bayan ya sauketa yakama hannunta suka shiga ciki.ruwan sanyi takawomasa yasha sannan tahad'omasa y'ay'an itatuwa irin wad'anda yafiso janyota yai ya zaunar akan cinyoyinsa yana kallonta sannan yatambayeta lafiyarta, dariya tai harsaida fararen hak'oranta suka bayya sannan tace "kaji yarima dama cemaka nai banida lafiya ni lafiyana k'alau" murmushi yai ya lakuci dogon hancinta sannan yace "to shikenan amma lafiyarki itace babban abun tambaya agareni kumani gaskiya acanja man wannan sunan na yarima yakamata nima arad'aman nawa sunan" yafad'a yana kashe mata ido d'aya. Murmushi tai tareda rufe fuskanta "to wanne kakeso" koma wane irine inaso amma fa na love kuma mai dad'i,  murmushi tasakeyi sannan tace "to juya fuskarka ko karufe ta" dariya ya kyalkyala mata sannan yace "to shikenan najuya" rufe fuskarta tai sannan tafad'a "my Nururul k'alb or my NUURR" woww the most beautiful and wonderful name nice gaskiya jasmine kin iya zab'en suna thanks.murmushi tai sannan ta tashi tawuce shikwa yabita da kallo,"...

Uwar d'akinsa ta wuce tashiga toilet tahad'amasa ruwan wanka sannan tafito, bayan tafito sannan yashigo yashiga wankan koda yagama  yashirya yafito harta had'amasa girki ammafa saida tarufe hancinta saboda batasan k'amshin abinci, bayan tahad'amasa komai sannan tazubamasa domin yaci janyota yai domin suci a tare saita zille tagudu d'akinta tak'i ci hakan yabashi mamaki ganin idandai yana gida ataresukecin abinci,, saida yagamaci yafita sannan tafito tacigaba da karatunta,,,...

Kwance take idanunta a rufe tana tilawa kawai saitaji ancungumo wuyan rigarta da sauri tabud'e idanunta domin ganin waye dan sam bataji motsi ko alamun shigowar mutumba, tana bud'e idanunta saitaga marwa ta zazzaro idanunta tana huci kaman zaki idan yana neman nakaiwa baki a dawa, dak'arfi ta cakumota ta d'ogata suna kallon juna sannan tace "wato ke kunnen k'arfe ne dakeko kinzama mayya bazaki iya raubuwa da mijinaba koh to tabbas kuwa kitabba rabuwa dashi shine mafi alkhairi agareki idan bahakaba wallahi saina kasheki saina illatadanginki gabad'aya saboda hakan yazamo ishara agun saura gobe ko ance baiwa tazo ta auri d'an sarki bazatayiba koda kuwa za'abata jajayen rak'uma dubu da dawakai d'ari, tanagama fad'ar haka taciro bulala wacca akai da fatar zaki tafara dukan hunayya ako'inanta duka banawasa ba, dukanta take hunayya kuma sai kuka take tana kwallah ihu da neman ceto itakuma bata fasa ba "tinda bakyaji bara nagyara maki zamanki kisan zama da mijina tamkar kishiga wutane" kuka take tana rok'onta "dan Allah sarauniya kiyafeni kiman rai ni marainiya ce wacca batasan komaiba dan Allah kiyi hak'uri wallahi zanbarmaki mijinki" jin abunda tafad'a yasa ta dakatarda dukan sannan takalleta tace "wato ke marainiya ce koh amma kinsan gado ke marainiya ce amma kinsan yanda ake kwana da miji" wani haushi da takaici taji yataso mata tad'aga hannunta iya k'arfinta tasake watsamata bulalar. Wata iriyar k'ara hunayya tai wacca tai daidai da shigowar BARKIN'DO yanajin k'arar yai sauri harda gudu yak'araso falon azatonsa waccan matsalar ce ta tashi yana k'arasowa saikuma yaga akasin hakan,, marwa yahango tana zabgar abar k'aunarsa kaman jaka itakuma tana ak'asa tarik'e k'afafun marwa tana mata magiya da kuka, dagudu yak'arasa yafizge bulalar sannan ya wankamata mari biyu a jere yak'ara wanka mata wasu biyu dak'arfi yasaka hannunsa yabigeta tafad'i abaya sannan yasaka k'afarsa yayi wurgi da'ita tasake fad'uwa ganin yanda yake dukanta yasa ta tashi tanemi hanyar tsrewa,huci yake ransa dik yab'aci juyowa yakalli hunayya dake zaune a k'asa tana rera kuka d'agata yai cikin b'acin rai sannan yace "har izuwa yaushe zaki fara mayarda martani ga marwa haba hunayya marwa fa mace ce kamar ke kuma mutum ce kamar kowa yakamata kicire da fargaba azuciyarki marwa ba komai bace face abokiyar zamanki yanzufa ke ba hadimarta bace ke abokiyar zamanta ce. Kuma inaso kisani daga yanzu bazan k'ara taremaki fad'anta ba idan zaki sakawa jikinki gishiri kisaka kitashe tsaye ki kwaci y'ancinki kema har taya zaki zauna marwa nafaman dukanki kaman jaka saboda ta rainaki to wallahi tin wuri ki farga kitashi daga nannauyan baccinda kikai dan daga yanzu bazan k'ara taremakiba"  shuru tai tana sauraren fad'anda yakemata har yagama. shima d'in shuru yai ganin yanda take kallonsa diksaiyaji tausayinta yakamashi janyota yai ajikinsa yarungume tareda yin kissing nata a goshi,, hannunta yasake ja yawuce da'ita d'akinsa yagasa mata jikinta da ruwan d'umi sannan yahad'amata tea tasha,"...

          *******  ******

Gimbiya sailuba ta aiwatarda dikkannin abunda boka yace tai kuma dika dakanta tai bawanda tasaka akaimata aganinta maganin yafi aiki idan tai dakanta dan ita aduniya ba abunda tatsana kaman kishiya shiyasa bata k'aunar gimbiya jidda mahaifiyar su BARKIN'DO,,haka itama marwa ta aiwatarda nata tsafin tabama dodon tsafinsu jinin hunayya yasha. Yaasalaam kai mutane tsoron Allah yai k'aranci azukatanmu Allah ka shiryardamu tafarki madaidaici ameen, "...

          **********

Tin dukanda marwa taiwa hunayya har yanzu bata k'ara lafiya ba kusan kullum cikin zazzab'i take saidai sam tak'i yarda kowa yasani ahaka har tasamu suka k'arasa exam d'insu, aranarda suka kammala kuwa ansha bikin bidiri komai sunyi na murna harda anko sunyi wasanni sosai aranar ne kuma hunayya tabayyanarda cewa BARKIN'DO mijinta ne ba yayanta ba aikwa harda malamansu sunyi mamaki sosai balle kuma k'awayenta da class mate d'inta, saida aka kammala komai sannan BARKIN'DO yazo yad'auketa suka wuce gida. Ranar saitazamowa Hunayya tamkar ranar akace gata a aljannah tareda NUURR d'inta farinciki take zallah, kwana biyu da kammala exam d'insu BARKIN'DO yahad'amata k'asaitacciyar walima sannan yabata kyautar dalleliyar mota sabuwa gall, murna da tsalle agunta ba'amagana dan adaren ranar saida tashayardashi zazzak'ar zumarta amatsayin tukuici,,,...

Wata ranar Saturday ne suna zaune a lambun ummi hunayya na a gefe tai shu saboda k'arfin hali kawai take badad'in jikinta takejiba. Kallonta BARKIN'DO yai yace taje d'akinsa na sashen marwa tad'akko masa phone d'insa badan tasoba dakyar ta'iya cemasa "toh" sannan ta tashi tawuce saboda kwanan nan haka kawai takejin yana damunta batasan yayo kusa da'ita saboda tirarensa ne bataso hak'k'insa ma dakyar takebashi dandai yazamemata dole ne,, ahankali tak'arasa cikin falour taduba bataga kowa ba sallama tai sallamar tasakeyi nanma shuru hakan yabata amsar bakowa danhaka kawai tawuce d'akinda taga kamar shine na BARKIN'DO tanufa cikin sa'akuwa shine k'arasawa tai aciki tafara duba wayar acan tahangota kan pillow, tana d'akkowa tafito tawuce tana fita marwa nafito tahangota tafita,,,..

Tana zuwa tabashi phone d'in tawuce sashenta saboda zazzab'inda takeji.tana isa tad'akko magani tasha tanasha kuwa dik ta amayardashi kankace me zazzab'i mai k'arfi yarufeta kwantawa tai tad'an huta,,,...

Har bacci yafara d'aukanta saikuma taji kaman motsin mutum a falour.k'arfin hali tai ta tashi domin taga waye turus tai ganin.......


🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀'''Muje zuwa'''

'''AUFANA for life '''🌷🌷
   *I. W. A*🖊

BARKIN'DO Where stories live. Discover now