[ 11/10/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
*[ ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ ]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious And dropping a kinda lights to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel
*Page 56~57*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Wata rana ne hunayya tadawo daga exam da misalin 6:00pm ta tararda k'ofargida a bud'e sab'anin yanda ta barta a rufe, k'arasawa tai ciki ahankali.tana isa cikin falon tai tsaye cakk tareda zazzaro dara daran idanuwanta saboda abunda tagani,,,...
BARKIN'DO ne kwance a k'asa cikin wani yanayi mai ban tausayi sai juyi yake yasaka hannayensa duka biyu yadafe mararsa,, da sauri tak'arasa ta ajiye jakardake hannunta a k'asa sannan ta duk'a tareda tallafo fuskarsa ta d'ora kan cinyoyinta cikin tsananin tashin hankali take tambayarsa "yarima meke damunka meya sameka ne" kasa cemata komai yai saifaman juye juye yake. Hanakalinta yatashi matuk'a tarasa yanda zatayi gata rik'e dashi kawai sai faman kwallah take tana kuka tana kiran sunansa,ganin abun bana wasa bane ciwon bashida alamun sakinsa yasa ta tashi tad'akko wayarta cikin kid'ima hannunta har rawa yake dakyar tasamu tai dialing number d'in humair. Yana d'agawa kuwa batajira yace komaiba danko sallamarda yaimata kasa ansamasa tai saboda kid'imewarda tai "humair ka taimakeni dan Allah kazo ka kai yarima asibiti gashinan kwance ba lafiya dan Allah kazo karyamutu humair" jin abunda tafad'a dakuma lurarda yai yanda take maganar alamun abun bana wasa bane yasa yai gaggawar zuwa, kamin yazo saida yad'akko family doctor nasu sukazo a tare,, koda sukazo haryanzu dai abun baikwanta ba nan suka kamasa suka tadashi izuwa uwar d'akinsa injection doctor d'in yafara masa saboda yasamu yai bacci ganin yagalabaita sosai. Bayan yamasa injection sannan yamasa gwajen gwajen fitsari da jini nantake yagano matsalardake damunsa,"....
Kallon humair doctor d'in yai sannan yace "humair hala yarima yasami matsala da gimbiya ne...??" kallon mamaki humair yamasa sannan yace "aa har yanzu suna a tare amma me kagani ne hala" a bincikenda nai yanuna man yarima yana fama da matsalar ciwon mara konace d'aurewar mara. Hakan kuma yana faruwa ne agun mazanda basuda aure kuma masu tara sha'awa batareda sun biya buk'atarsu ba, kuma sainaga yarima nada aure hakan yasa nai mamaki dahar yakamu da wannan cutar bayan kuma yanada matarsa,, hmm...!!! humair yanisa "hakane nikaina nayi mamakin hakan amma yanzu dai mubar wannan zancen har yasamu sauk'i" ok badamuwa namasa injection yasamu bacci ga wannan. Yamik'a masa wata takarda "aje anemomasa wad'annan magungunan idan yatashi sai abashi yasha insha Allah zai sami sauk'i zaiji sauk'in ciwonda marar kemasa" karb'a humair yai suka fito atare, koda suka fito harsu meesha sunzo hunayya kuma har yanzu kuka take saida su humair suka fito yafad'amata yasami sauk'i sannan tad'an kwantarda hankalinta, '....
Bayan humair yafita sannan suka shiga. Kwance yake har yanzu yana bacci,,,...
Saikusan 7:30pm sannan humair yadawo haryanzu kuma BARKIN'DO bai farka ba, zama humair yai har kusan 9:30pm ganin dare yayi yasa yad'auki su meerah suka wuce gida, suna fita hunayya ta tashi tai sallah sannan ta dawo ta zauna kusa da BARKIN'DO tana kallonsa cike da tausayinsa. Tana nan zaune har bacci b'arawo ya saceta,,around 11:00pm BARKIN'DO ya farka ahankali ya juyo sai yaga jasmine d'insa a kwance gefensa d'ayan hannunta mak'ale da nasa. Murmushi yai ahankali ya duk'o ya sumbaceta a goshi cike da k'aunarta,, ahankali ya yunk'ura ya tashi sannan ya janye hannunsa daga nata toilet yawuce yahad'a ruwan d'umi yai wanka sannan ya d'auro alwala yafito nan yafara ranka sallolinda ake binsa, bayan yagama sannan yakashe hasken d'akin yahau gado ya kwanta tareda janyota ajikinsa ya rungume sannan yajanyo blanket ya rufesu asuba tagari,,,...
Da safe ma yarigata tashi saida yai alwala yafito sannan ya tadata, mamaki tai sosai ganin tabarshi a kwance amma harya rigata tashi yai alwala kuma shine tabari a kwance ba lafiya.tashi tai tashiga toilet tad'auro alwala sannan ta dawo yajasu sallah,, bayan sungama ne takallesa tamasa barka da safiya sannan tamasa sannu da jiki nan ta tashi tashiga kitchen tahad'amasa tea sannan ta b'allo masa maganinsa yasha kamar yanda humair yace,, bayan yasha ne tashiga kitchen tahad'amasu sukaci,'...
A yauma sunada exam 11:00am amma ganin BARKIN'DO bashida lafiya tace bazatajeba saida yai kamar yanayi sannan ta shirya tawuce,'...
****** ******
Yau kimanin kwana hud'u kenan Alhamdulillah BARKIN'DO yasami sauk'i sosai hunayya kuma ankusa kammala exam yau saura biyu sugama,,,..
kwance take akan kujera tana tilawa saigasu meesha sunzo sukace ta shirya sufita yawo, bataso hakan ba taso yau takaratu sosai amma tinda sunzo bazatace bazataje dole ta tashi tacanja kaya suka fita,, sunsha yawo sosai harda gidansu nasreen saida sukaje daga bisani sannan sukawuce gida,'...
Zaune suke a falon hajiya sunashan fira saiga meesha tashigo tace hunayya taje BARKIN'DO na nemanta bataso tashiba saboda tanaso tak'arasa jin labarinda hajiya ke basu dole badan tasoba ta tashi tafita,, hunayya na fita saiga marwa tashigo ita da fainus sundawo daga shegen yawonsu. Kallon juna su meesha sukai tareda sauke nannauyan ajiyan zuciya "Alhamdulillah Ala kulli halin" meesha tafad'a a fili meerah kuwa murmushi kawai tai,, kallon marwa sukai sannan sukace "sannu da zuwa sarauniya" cikin isa da k'asaita da takarb'a masu shima dakyar. Harta zauna a falour saikuma ta tashi tashiga uwar d'aki tanashiga meesha ta tashi da sauri tafita, tana fita taje tafad'awa BARKIN'DO dawowar marwa hunayya hankalinta ya tashi sosai nan yace suwuce sashen ummi kamin yazo,,,....
Suna fita sai sukabi ta bayan sashen hajiya izuwa lambun mai martaba inda yake shan iska da maraice, waige waige suke saboda karsu had'u da jakadiyar gimbiya laila kwatsam sai sukayi kicib'is da marwa tana tafiya tana danne dannen waya,, d'agowarda zatayi sai sukayi kicib'is da kyakkyawar fuskar hunayy........
🏃🏻♀🏃🏻♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life '''🌷🌷
*I. W. A*🖊