[ 24/9/2018 ]
🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[ very interesting story ]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®📚
*[ onward together ]*
*{ we give the readers of ours the best out of bests,,our inks are melodious and dropping a kinder lights to readers}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HERT TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIEGE THINK💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔*Slm readers kuyi hak'uri dan Allah naji k'orafinku wlh ba laifina bane, Aufana fa apolo takeyi 🧐 kuman uzuri asata cikin addu'ar samun sauk'i dan taji dad'in suburbud'o maku tyaiping Ehi*😎
*Page 34~35*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Yana cikin amsa wayar kawai saiga wata mota tazo tai parking akusa da shi, kamar ance waiga yana waigawa kuwa idanunsa sukai masa tozali da wata fuska, zaro idanunsa yai cikin tsananin mamaki,,,...
Tabbas abunda idonsa yaganemasa gaskiya ne,Fainus ce abayan mota tareda wasu k'arti uku suna bad'ala San ransu,sauri yai yatada motar ganin sunfara tafiya alamar zasu wuce nan yai sauri yadafa masu baya,,ahankali yake bin bayansu dan karsufahimci su yake bi,tafiya suke har suka iso wani katafaren gida mai kama da hotel amma zahiri ba hotel bane wani gu yasamu yai parking ya sauke glass yana hangosu,fitowa sukai atare d'ayan na d'auke da ita can kuma gefe saiga Marwa tafito tareda wad'annan k'awayen nata dayagansu ranar agidansa suna dariya nan suka tafa sannan suka shiga ciki atare,wajen yanada matuk'ar tsaro sosai dan dai harda jamian tsaro yagani [ police ] da'alamu dai harda Manya acikin harkar,, Yaaa salaam BARKIN'DO yafad'a a bayyane dan dai takaici da mamaki Sun hanasa magana balle motsin kirki nan dai ya tada motarsa yakama hanyar gida,'....
****** *******
Koda tashiga kuwa cikin sa'a ta tarar harta farka tana zaune kan gado, cikin murmushi tai nokin tareda yin sallama, cikin tattausar murya mai kama da muryar mai kuka ta kar'ba mata sallamar nan itakuma ta shigo sannan ta zauna kallonta tai saitaga tabbas dik yanda yarima yafad'amata hakane yarinyace sosai kuma mai k'ananun shekaru,,cikin dabara tafara gabatar mata da kanta ""Gimbiya hunayya nasan bakisanni ba ko"" ta d'aga mata kai alamar eh "murmushi tai sannan tacigaba sunana Aunty Salma yarima yaturoni domin nadinga d'ebe maki kewa inafatar zaki Saki jiki dani muzama k'awaye"" hmm su hunayya kenan sarkin san k'awa tanajin tace k'awa nan tai murmushi sannan tace ""Eh dan wallahi tsoro nakeji nikad'ai tafad'a a shagwa'be"" dariya Anty Salman tai to karki damu ai yanzu gani ko ina taredake har yarima ya dawo kuma zan koyamaki abubuwa dayawa,, kallonta tai tace "Anty salma dan Allah kije dani gidanki karki barni anan ko yarima ya dawo" cikin mamaki ta kalleta tace inje dake kuma hunayya meyasa bazaki zauna anan ba kuma tsoron me kikeji bayan ga yarima,, shuru tai takasa fad'a hhhh tini Salma ta gano inda zancen hunayya ya dosa saboda salma cikakkiyar wayayyiya ce tasan abubuwa da dsma na sirrin zaman aure,murmushi tai sannan tace tashi muje kitchen in koya maki wani abu mai dad'i, tashi tai ta sauko daga kan gadon nan suka fara tafiya kallonta salma keyi ganin yanda take tafiya tana ware k'afafunta kuma tana d'ingishi gaya kuma tafiyar kamar batasan yinta haka takeyi dan k'afar d'aya ahankali take takata,,tsayawa tai sannan ta tsayar da itama tace "meke damun k'afafunki kike tafiya a ware kuma kina d'ingishi" duk'arda kanta tai k'asa takasa cewa komai sai salma tai murmushi dan dai ta fahimci hunayya akwai kunya sosai ga yaranci,,jan hannunta tai suka koma ciki toilet tashiga da ita nantahad'a mata ruwan d'umi masu zafin gaske sannan ta d'akko jakarta tafito da wasu sihirtattun magungunan mata nanfa tashiga gyaran hunayya, wannan na tsarki wannan na tsuguno wannan na girki,,tin hunayya najin kunyarta har tafara sakewa ganin Antyn tata batada wasa,saida taga ta kammala mata komai sannan tasaka tai girki saida ta rufe fuskarta sannan ta shiga ruwan Salma yarancin hunayya birgeta yake sosai aikwa tanad'an murmusawa danma batasan ta rainata ne,bayan tagama komai sannan ta wanke mata sumarta saboda taji warin mayukan da inda tashafa mata nan tasaka had'ad'd'un mayuka ta wanke sumar tass tasaka k'aramin towel ta rufe ta daganan kuma sai tafara koya mata yanda ake amfani da toilet dama dik wani abu dake cikin toilet d'in musamman tsadaddun mayuka da tirarukan da BARKIN'DO yasiyomata,dik saida Salma takoya mata komai Hunayya kuwa dikta haddace komai kasancewar dama hunayya akwai basira rashin samun wadataccen ilimi ne kawai primary ma dakyar ta idata tallan nono da aikatau na gidan sarauta basu barin ta taje makaranta ga kula da Abban ta Allah sarki baiwar Allah hmm,'...
Bayan Sun gama komai sannan suka fito nan ta gyara mata sumarta sannan kuma ta koya mata yanda zata dinga gyaran jikinta da irin mayukan da zata dinga amfani dasu,saida tasaka kaya sannan tamata make Up hmm zo kuga inda kyau ke zuba kaman ka duk'a ka kwasa hhhh Lol, '...
Bayan Sun gama sai suka fito waje kitchen suka shiga Anty salma taji dad'i sosai ganin yanda BARKIN'DO ya k'awata kitchen d'in da kayan aiki na zamani nan suka shiga store nanma dai komai na buk'ata akwai ya kawo aikwa nan Anty Salma ta zage dantse suka fara girki dik abunda tai sai Hunayya ta rubuta dan gudun mantuwa kuma (dik abunda bata gane yanda ake amfani dashiba saita tambayeta hakan yasa cikin d'an lokaci hunayya tashiga ran Salma sosai tana San mutum Mai halayya irin ta hunayya hakan yasa taci burin taimakon ta iya k'arfinta,,girki kala uku sukai had'e da abun sha juice kala biyu kasancewar hunayya tafara gajiya shiyasa Salma ta kyaleta haka aikwa sai dariya take mata tana cemata raguwa,bayan sun gama sannan suka tsabtace kitchen d'in sannan suka fito falour suka kwanta suna hutawa Salma namata bayani akan sauran girke girken da sunayen abubuwa na girki wad'anda tinda hunayya tazo duniya bata ta'ba jinsu ba balle tasansu,lokacin sallah yayi hakan yasa suka tashi suka shiga ciki domin gabatarda sallah,'....
****** ******
Yana isa gida yawuce sashen hajiya suka gaisa sannan yafito yawuce sashen ummin sa itama yagaidata dikda bawata fira suke ba amma hakan baihanasa idan yazo yagaidata yad'an zauna na wasu mintina sannan yatashi yawuce,,bayan Sun gaisa sannan yafito yashiga d'akin 'yanuwansa,yana shiga yace masu su shirya zasu fita nan suka tambayesa inda zasu ya sharesu yafita abunsa ganin haka yatabbatar masu da yau d'anuwan nasu yana cikin wani yanayi nandai suka shirya sannan suka fito suka samesa cikin motarsa nan suka bud'e suka shiga sannan yatada motar suka wuce,,,....
Meerah fa takasa hak'uri dan haka tasake tambayar BARKIN'DO ""wai yaya ina zamuje ne dan Allah kafad'amana"" hmm...!!!yanisa dad'ina dake sister gajen hak'uri,, hhhh meesha tai dariya aidama nasan ba mai sauke wannan fushin sai meerah gaskiya yaya yakamata kam musan inda zamuje ko surprise ne, murmushi yai sannan yace gun Auntyn ku zan kaiku saboda kusan juna,,cikin mamaki su duka suka had'a baki wajen fad'ar "Auntyn mu" Eh kujira muk'arasa sai muyi zancen acan "OK to bakomai" meerah tafad'a,,,....
****** ******
Bayan sungama sallah suka fito falour suna jiran dawowar BARKIN'DO dan Salma tanaso tawuce gida, suna zaune kuwa saisukaji anyi noking tareda yin sallama atare suka juyo sannan suka kar'ba sallamar,, Laaa Anty Salma kece cewar meerah ""Eh tagwayen mai martaba nice anzo gun amarya to sannunku da zuwa marabanku"" cikin murmushi suka k'araso cikin falon suka zauna sannan suka gaisa da Anty Salma,'....
Zama BARKIN'DO yai sannan yafara magana ""meerah meesha inace idan baku Manta ba kwanan baya nafad'amaku cewar zanyi aure to wannan itace matar ya nuna Hunayya data zuba ido tana kallonsu kuma itace za'bina,,inaso ku taimakaman wajen gudanarda abunda nakeso nayi inafatan zaku taimakaman amatsayinku na 'yanuwana"" kallonsa suke saida ya gama sannan meesha tace ""Insha Allah yaya muna bayanka kuma zamu baka cikakkiyar gudumawa dama ni wallahi basan ya Marwa nakeba sam bata birgeni ga mugwayen halayenta har yanzu bata dawoba da wajen shegen yawonta ba"" dariya sukai su duka nan suka dubi hunayya suka gabatar mata da kansu itama cikin murmushi tamasu barka da zuwa, bayan Sun gaisa ne sukacigaba da tsara yanda abun zai tafi cikin tsari batareda kowa ya ganosuba,,bak'aramin jin dad'i BARKIN'DO yai ba ganin yanda 'yanuwansa suka bashi cikakken goyon baya,,bayan sungama tattaunawa ne Aunty Salma tafito Masu da sihirtaccen girkinda suka had'a nanfa suka baje suna kwasar gara,sunci Sun sha cikin farin ciki da nishad'i sai faman santi suke,'...
Bayan sungama nan suka Fara fira Salma ta lura da yanayin BARKIN'DO da'alamu dai yana buk'atar matarsa dan haka bara subarmasa gidansa,tashi tai tashiga tahad'a kayanta sannan tafito suka wuce domin tafiya gida,nan BARKIN'DO yatashi domin yakaisu, Salma suka Fara saukewa sannan yawuce yasauke su meesha saida yashiga sukai saida safe dasu Ummi da hajiya sannan yafito,'...
Ahankali yake driving wani nishad'i yana shigarsa sai faman murmushi yake kaman wanda akayiwa albishir da aljannah........
*Dan Allah kusaka mommo na saina ummun meenal acikin adduah batada lafiya wlh da nima kaina*😎😢
🏃♀🏃♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life'''🌷🌷
*I.W.A*🖊