BARKIN'DO part 11-12

1.9K 99 0
                                    

[11/8/2018]

🌷 *BARKIN'DO*🌷

*[ very interesting story]*

*Story & Writing - By AUFANA*✍

✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚𶢮
      *{onward togather}*

*Page 11~12*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Bayan ta kammala tafito ta tarardashi à falo yana waya,, zama tai tajirashi haryagama sannan yajuyo yakalleta cikin sakin fuska sannan yace ""Hunayya harkin kammala""   tace "Eh"  OK  ""hunayya bakomai nakeso namaki magana akaiba Hunayya inaso nasanarmaki ne da sak'on zuciyata""   kallonsa tai cikin rashin fahimta shima ya lura da hakan danhaka yacigaba da magana ""Hunayya tin ranarda idanuna sukai tozali da kyakkawar fuskarki naji kinkwanta man arai naji inasha'awar zama dake,, Hunayya bazan 'boyemaki ba Inasanki inasanki kuma inasan kasancewa dake amatsayin matata uwar 'ya'yana""    jin maganar tai tamkar saukan aradu dasauri tad'ago kanta tana kallonsa cikin tsantsar mamaki da tsoro ""yarima kasan kuwa abunda kake fad'a""  tabbas nasani cewa nai inasanki ko bancancanci nasokibane,,  bahaka nake nufiba karfa ka manta had'in aurenkune yakawoka wannan k'asar kai dakuma 'yaruwarka Marwa to taya zanyi gaggancin amincewa tayin soyayyarka,,wallahi kuma basona kakeba yarima dakanasona tabbas bazaka furta man wannan kalma ba, shin kasan halin sarauniya Marwa kuwa idandai har nabari wannan maganar gafita awaje bansan makomataba watak'il ma shine zaizama sanadin barinmu duniya kokuma amana korar kare ni dakuma mahaifina,, narok'eka karufaman asiri idandai har dagaske sona kake,,,....

Ransa yayi mugun 'baci nantake idanunsa suka canja launi izuwa ja cikin kakkausar murya yace ""har izuwa yaushene zakudaina jin tsoron Marwa itafa ba ubangiji bace kuma ba mala'ikar zaran rai bace bataisa takasheba kuma bataisa ta rayar ba tabbas yiwa shugaba biyayya wajibine amma tsawaita tsoronsa aibune saboda zai iyacutardakai,, Hunayya inasanki kece za'bina rok'ona dan Allah kidaure kikar'bi soyayya namaki alk'awarin ganin bayan mulkin kama karyanda Marwa da mahaifiyarta keyi awannan masarautar""    jin maganarsa yasa tad'ago dasauri daga durk'ushenda take tace dan Allah yarima dagaske kake murmushi yai yagyad'amata kai alamun Eh  ""tabbas idandai har zaka kawo k'arshen wannan zalincin nikuma namaka alk'awarin kasancewa dakai har k'arshen rayuwata,, raina da dikwani abu dana mallaka zan iyabadashi idandai har zaisa mutanen wannan k'asar sumasu 'yancin kansu mudawo sakakku masu 'yanci da iko""   duk'owa yai daidai fuskarta yana kallonta hargoshinsu na neman yahard'e sannan yace ""kenan kin amince da tayin soyayyata""  d'agowa tai suka kalli juna dasauri ta tashi tawuce tana dariya had'e da rufe fuskarta da tafikan hannayenta,, saida takai k'ofar fita ta tsaya tace ""Eh na'amince kazo kaga gida kaga Abbana dik abunda yacemaka shikenan""  tana fad'ar haka tawuce abunta,, wani dad'i da tsintsar farinciki yaji ya rufeshi yafad'a kan kujera yana tsalle kamar k'aramin yaro saida yagama murna sannan yawuce ciki,'.....

Bayan taje gida tafad'awa mahaifinta yanda sukai da BARKIN'DO dafarko shima yak'iamincewa amma dataimasa bayanin Alk'awarin da yamata idan dai harta'amince ta auresa sai yaji dad'i yai farinciki sosai kuma yace ya amince,,,...

Araund 4:00pm BARKIN'DO ya shirya tsab cikin shiga mai kyau yafito yashiga gun humair,, wayam baigansa can yaji alamun yanacikin band'aki danhaka yawuce abunsa,'...

Rugarsu Hunayya ya dosa yayinda d'an aiken sarauniya Marwa ke binbayansa batareda yasan dashiba haryazo gidan,, Sallama yai tareda shiga zaune take tana dafa madara abbanta kuma yanabama dabbobi abinci,, Jin sallamarsa yasa sukajuyo domin ganin mai sallama tana ganinsa taiwani k'ayataccen murmushi tareda juyawa tacigaba da aikinta,,  Abba kuwa cikin sauri cikin murna yataso ""à à yarimane atafe haka maraba barka da zuwa""   cikin murmushi yace "Eh Abba nine wallahi" nan yadurk'usa yagaidashi suka gaisa sannan abba yashimfid'amasu tabarma suka zauna,, BARKIN'DO ya d'ago da kansa yace ""Abba nazone batun maganarda mukai da Hunayya"" murmushi yai sannan yace "Eh hunayya tafad'aman dik yanda kukai dafarko na tsorata kuma nak'i amincewa da manufarka amma daga Baya dataman bayanin komai na amince saidai haryanzu yarima inatsoron sharrin Marwa da mahaifiyarta dan Allah mu 'boye wannan maganar har izuwa lokacinda komai zaizo k'arshe""    d'agowa BARKIN'DO yai yakallesa yace Abba kudaina Jin tsoronsu kuma insha Allah namaku Alk'awarin ganin bayan wannan mulkin zalincin da'akemaku,, shikenan Allah ya taimakeka yace ameen,, Hunayya ta kammala dafa madara nantasaka sikari sannan tad'obo a kwarya takawowa Abba da BARKIN'DO,aikwa BARKIN'DO yasha sosai saboda yaji dad'inta sosai,,,....

BARKIN'DO Where stories live. Discover now