🌷 *BARKIN'DO*🌷
*[very interesting story]*
*Story & Writing - By AUFANA*✍
✨✨ *Devoted to - ALL FULANI'S IN THE WORLD*✨✨
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*📚®
*{ onward togather }**Page 7~8*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Yau Kwanansu uku da zuwa BARKIN'DO yagaji da zama yacewa humair sufita sud'an zaga gari,,,.......
Wata ruga sukaje maikyau mai tsari tabirge BARKIN'DO sosai gaitatuwa wajen yai sanyi sosai gwanin birgewa,, ga fulani kowa na aikingabansa, tafiya suke suna firar yanayin rugar can kawai sai BARKIN'DO yahango yarinyar dake kula da 'bangarensa ita da 'yaruwarta sunad'auke da tuluna aka da'alamu dai daga rafi suke,, murmushi yai yakalli humair yace ""humair mubi yarancan muga gidansu"" mamaki ne yakama humair saidai ba halin magana saboda yasan halin d'anuwannasa,, binsu kuwa sukai har tarabau da 'yaruwarta tacigaba da tafiya suma sukaci gaba da bibiyarta,'...
Wani d'an k'aramin gida sukaga tashiga mai d'auke da bukka {RUMFAR HAKI KO YAYI }guda biyu anzagaye gidan da kara,, bayan ta shiga suka sai BARKIN'DO yace su wuce shidai humair yasakashi a duhu amma bai tambayesa ba suka wuce,, sun jima sosai suna shan iska tareda kallon rugar dakuma yanayinta tareda mutan cikinta,,,...
Sanyin La'asar yasauka yayinda yanayin rugar kuma ya canja yafi na d'azu dad'i yanayin kuwa bak'aramin birge BARKIN'DO yake ba yai kwance abunsa yana shak'ar iska maidad'i,, humair yakalles yace ""d'anuwa da'alamu kanajin dad'in yanayinnan"" murmushi yai yace "Eh rugar tamin dad'i sosai tabanai sha'awa"" shima murmushi yai yace bara naje nasamomana abun ta'bawa nasanka dasan Mangwaro, dariya yai yace kai danamaka godiya kuma nasaka maka albarka shima dariyar yai sannan yawuce,'...
BARKIN'DO na kwance saiyatashi juyowarda zaiyi kawai daiyaga yarinyar nan maigyaran 'bangarensa tana tafiya Mai had'e da gudu gudu kuka take sosai da'alamu ma koganin hanyarda take tafiya batayi tashi yai dasauri yabita cikin sa'akuwa yacimmata harsuna nema su kauri juna, tsayawa tai cakk tana kallonsa da mamaki d'aure fuska yai sannan yatambayeta ""meyafarune kike kuka lafiya...?? "" dakyar taiya bud'e bakinta cikin hausarta mara kyau tace ""Abba nane bashida lafiya gashi kuma maganinsa yak'are inatsoro kar yamutu najegun maisayarda maganin yak'i yabani harnakai nono kasuwa nasayar"" hmm....!!! Yanisa sannan yace inayake abban naki, yana gida tabashi amsa kai tsaye shikenan muje wajen maisayarda maganin nan suka wuce mutane sai kallonsu ake da'alamu dai itama arikice take dole ce kawai tasakata yin tafiya dashi,, tafiya suke har sukakai shagon nan yafiddo kud'i yamik'a masa sannan yabata maganin suka wuce,'...
Cikin sauri take tafiya saboda tasan halinda tabar mahaifinta har suka iso gidan, iso tamasa wato yashigo ciki nan yashiga dakansa yad'agasa yabashi magani tareda fura sannan yamaidashi yakwantar sai kallon BARKIN'DO yake haka itama kallon nasa take,,,...
Humair yadawo amma baiga BARKIN'DO ba nan yaciro wayarsa yakirasa yafad'amasa inda yake mamaki ne yakama humair to mekuma yakaisa can baiwarganta ba yaje gidan ita tafita tamasa iso yashigo ganin abundake faruwa yasa baiyi maganaba shima yazauna, '...
Alhmdllh yasamu sauk'i har bacci yad'aukesa ganin haka yasa BARKIN'DO yace humair yatashi su wuce gashi kuma magrib takawo jiki,, har k'ofar gida tarakosu sai godiya takewa BARKIN'DO,,lokacinda zasu wuce yacemata gobe kartazo aiki tabari har mahaifinta yaji sauk'i nan tashaida masa idan har batajeba to tabbas zatayi laifi kuma sarauniya zatai mata hukunci mai tsanani,, ransa ya'baci sosai baisake cewa komai ba yawuce humair yabibayansa suka wuce,'....
Around 8:00am suka kammala aikinsu tatsabtace ko'ina sai k'amshi ke tashi d'ayar kuwa tajera abinci kala kala sunyi zaune suna jiran fitowar BARKIN'DO,, har kusan 9:15am baifito ba gashi tanasan taje gun mahaifinta sai 10:30am sannan yafito nan suka duk'a suka kwashi gaisuwa cikin tsintsar ladabi irinta shuga da mabiyansa cikin sakin fuska yakar'bamasu tareda tambayarta jikin mahaifinta tashaidamasa yaji sauk'i,,,....
Wucewa yai zuwa yin breakfast dasauri taje tad'auki plate domin zubamasa abincin,, murmushi yai yana kallonta cikin nutsuwa take aikinta komai nata abun birgewa ne jin tafiya daga k'ofar shigowa yakatse masa kallonda yake mata,, tafiya take cikin isa da k'asaita irin ta masu mulki har tak'araso sannan tai sallama cikin fara'a yarinyar ta juyo dasauri ta zube tana kwasan gaisuwa ko kallonta bataiba balle takar'ba mata,, zama tai tareda kar'ban plate d'inda ke hannun yarinyar dasauri ta mik'amata tareda wucewa k'urya domin k'arasa aikinta,,ko ba'afad'aba kunsan sarauniya Marwa ce,'...
Abinci tasaka masa ta ajiye agabansa har tak'are abunda take baice daita uffan ba ganin haka yasa ta matso kusa dashi sannan tace ""yarima ga abincin nan agabanka gimbiyarka tazubamaka"" sai alokacin yad'ago yakalleta sai faman murmushi takemasa shikuwa bala'in haushi take basa,, wanke hannunsa yai sannan yafara cin abincin tareda yin basmala cikin nutsuwa yakeci har yakammala tazuba masa ruwa ya wanke hannunsa sannan yasha ruwa nan yakalleta cikin d'aurewar fuska yace ""nagode zanshiga ciki inasan nai wanka"" baijira tace komaiba yawuce abunsa tsananin 'bacin rai yabayyana afuskarta takasa cewa komai kawai ta tashi tawuce cikin gida rai à 'bace,, d'akin mahaifiyarta tawuce tana shiga tafad'a jikinta tana rera kuka ai bashiri tashiga rarrashin ta tareda abundake faruwa ganin daga 'bangaren BARKIN'DO tafito nantake tafad'amata abunda yake mata tin lokacinda yazo,, wata dariyar mugunta gimbiya sailuba tai sannan tad'ago Fuskarta tana kallonta tace ""yarinya share hawayenki kamar kin auri BARKIN'DO dik abunda yake maki barnidashi kawai dasannu zanyi maganinsa saina sakashi yasoki fiye da gyatumarsa sonda ko uwarsa takirasa idan kikace karyaje bazaijeba"" dariya tai cikin farinciki tace ""wallahi shiyasa nake k'ara sanki umma na kina shareman hawayena akodayaushe"" itama dariya tai nan sukacigaba da firarsu,,,...
Around 4:00pm BARKIN'DO yashirya tsabb cikin shiga Mai kyau shigarda bazakace d'an sarki bane ko jinin sarauta bane amma dai dakagansa kasan d'angaye ne,, d'akin humair yawuce kodayaje haryanzu bacci yake kawai yafito yarufemasa k'ofa yawuce abunsa,'....
Rugarsu yarinyar yawuce direct gidansu yawuce,,,..
Sallama yai yashiga gidan,, zaune take akusa da abban ta tanabashi fura yanasha suna fira k'awarta na gefe itama furar takesha,, jin sallamarda akayi ne yakatse masu fira yarone yashigo yace ""ance wai anakiran yarinyar gidannan"" cikin mamaki tace wake kiranta yaron yace ""wani d'an birni ne"" tanajin haka tagane ko waye tacemasa kace tanazuwa,, juyowa tai domin yiwa abban ta da k'awarta bayani saboda tasakasu à rrud'u nan tashaidamasu cewa Yarima ne,, tsoro da fargaba suka tattaru acikin zuciyar mahaifinta dakuma k'awarta badon komai ba saidon tsoron halin gidan sarautar DUMNAH,,,....
Tashi tai jiki ba kwari tafita fuskarta ba walwa aranta takecewa ""Allah ka kareni daga sharrin sarauniya marwa da mahaifiyarta dandai wannan bawan Allah na neman sakani a masifa"" ahaka tafita tanata zancen zuci har tak'arasa nesa dashi ta tsaya batareda ta kallesaba kuma fuskarta ba walwa tai masa sallama,,,...
Cikin sakin fuska kuwa ya amsa sallamarta yai tsaye tareda hard'e hannayensa gu d'aya yana kallonta,, tasha kwalliya irintasu ta fulani,, janbaki ne ja tasaka à lips d'inta na k'asa à nasaman kuwa tasaka bak'i sannan tai d'igo d'igo na bak'i, kayanda ta saka dikda sunsha tsufa amma tawanke abunta tass hakama takalmanta dik tawanke tass sai kyalli take da k'amshin tirare mai dad'ingaske,,,...
Saida yagama k'are mata kallo sannan yace ""yajikin abba fatan yasamu sauk'i"" Eh yajisauk'i tabashi amsa kaitsaye ""to alhmdllh Allah yak'a bashi lafiya""
Tace ameeen...!!!
Dagowa yai yana kallonta yayinda itakuma kanta yake à k'asa yace ""kozan iya shiga nagaidashi"" dikda bataso yin fara'a ba amma yanayin maganarsa saida yasa tad'an murmusa sannan tace masa Eh bismillah, '...
Ita tashiga gaba shikuma yanabin bayanta harsuka shiga,, gidan tsab tsab yasha shara ko'ina tsab dikda bawani gidan kirki bane kuma bawasu kayan kirki ne acikinsa ba amma dai tashare ko'ina,'....
Wata 'yar kyamusasshiyar tabarma ce tad'akko ta shimfid'a masa ya zauna sannan suka gaisa da abbanta......
🏃♀🏃♀🏃♀'''Muje zuwa '''
'''AUFANA for life '''🌷🌷🌷
*I.W.A*🖊