MAMANA CE page 1__ 4

2.5K 93 3
                                    

[12/01, 5:20 PM] Hauwau Salisu: 🤱🏻🤱🏻🤱🏻 *MAMANACE* 🤱🏻🤱🏻🤱🏻

                   *NA*

          *HAUWA'U SALISU*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

07081095452





*Bismillahirrahmanirrahim*

_Dukkan godiya da yabo su tabbata ga Allah ubangijin talikai ,tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad ( S A W )_


*SADAUKARWA*

'''Wannan littafi mai suna *MAMANACE*  na sadaukar dashi ga *HAJIYARMU* ( ~HJY ZAINAB SALISU _ABDULLAHI_ FUNTUA~ )
Allah ya kai ladar gareki yasa kin huta , tabbas munyi rashinki rashinda bazamu taba cikesaba fatanmu addu'anmu can yafi maki nan *Hajiyanmu* duk Wanda yakaranta book dinnan yanuna min godiyarsa ta hanyar mata Addu'a nagode.'''

Page 1




Titi ne lafiyayye wanda manyan motoci kebi da 'yan sumogal din Shinkafa ,

Titin ya ratsane ta wani kauye mai suna SARARRAKI wanda duk motar da zata wuce dole saitabi takan titin .

Cikin matukar gudu yake tafiya daga can tsakiyar titin ya hango wata mace tayi tsaye a tsakiyar titin tana tafiya tamkar batasan taka kasa .

Hon yaketa mata ta kauce ta bashi hanya amma ina ko a jikinta ga alama dadin hon dinda yake mata takejima.

Cikin bacin rai ya taka burki gab da ita a zuciye ya fito motar ya shakota ta bayanta .
Dai dai wannan lokacin ita kuma wata yarinya 'yar kimanin shekaru Tara tana daga can tsallaken titin tanata dago hannu alamar magana take ma matar .

Ganin ya rikema matar hijab yasa yarinyai rugowa da gudun tsiya dan ta iso gun, sai dai kash  ta makara .

Cikin zafin rai ya kwashe matar da mari ya kara kwasheta da mari ya saka kafarsa yai ball da ita kan titin ya tofa mata miyau a fuska ya juya cikin takama da isa ya shige motarsa .

Ganin abunda yafaru yasaka yarinyai daukar dutse sai jikai tasss ta fashe mashi glass din gaban motar .

A razane ya kalli matar yaga ko itace , abun mamaki tana yanda ya barta sai hawaye daketa zuba kan cukuikuyayyen hijabinta .

A kyamace yasake kare mata kallo ,,ya salam ya furta .

Hakan yai dai dai da jin karai fashe masa glass din bayan motar kuma .

Wannan karon fitowa kawai yayi a zuciye yana kallon yar yarinyar datai masa wannan barnai .

Cikin kuka ta duka ta kama matar tana share mata hawayenta ta goge mata miyanda ya bata mata fuska .

Bai jira komiba ya fincikota ya daga hannu da niyar wanketa da mari sai dai dole ya fasa danjin wani masifaffen zafi daya ziyarci kwanyarsa .
Iyakar karfinta ta kama fatar bayan hannunsa saida ta jita a bakinta sannan ta saki .

Yana cikin halin fita hayyacinsa ta kallesa ta murguda masa baki ,,kai dan bunni nima mamanace wannan dan haka na rama mata muguntar da kai mata .

Kafin yai wani yunkuri taja hannun uwarta sun kwasa da gudu sunbarsa duke rike da hannu jini sai zuba yake .

Binsu da kallo yai harsunsha wata karamai kwana sun bace masa .

Girgiza kansa yai tabbas saiya dau fansar abunda 'yar iskai yarinyai can taimasa duk daren dadewa saiya koya mata hankali daman banzayen kauyawan nan tamkar jakkuna suke ai .

MAMANA CE Where stories live. Discover now