MAMANA CE page 49__50

511 30 0
                                    

*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

*Wattpad Hauwausalisu*

Gmail_*__Hauwausalisu407@gmail.com*

Facebook *___Hauwa'u Salisu*

_Kuyi mun afuwa ycn kwana biyun nan sai hakuri kawai da godiya ga Allah_ 👏🏻👏🏻👏🏻

Page 49__50

Kallon natsuwa Abbu yabi Aiman dashi , ko bai bayyana mashi komi ba ya fahimci kwana biyu yaron sam baida natsuwa, ko bai zo gunsa ba yayi niyar zuwa garesa dan jin damuwarsa .

Cikin tsananin ladabi Dr Aiman ya dubi Abbu ya sadda kansa ƙasa.
"Abbu daman akwai wata alfarma da nake nema gunku ,,

Abbu ya kallesa fuska dauke da murmushi yace "Ina sauraren ka Dabto ,,
Sai da murmushi ya kubce ma Dr Aiman din jin Abbu ya tuno baya (Wai Dabto )

Daman yayi hakan ne dan Aiman din yasamu kwarin gwiwar fadi mashi damuwarsa cikin sauki .

"Abbu daman na jima ina son Amrah to amma ban san ko kun yi mata miji ba " (ya kai karshen maganar cikin tashin hankalin kar dai an bada ta kauyen su )

Abbu hamdala ya fara yi don shi daman yana addu'a Allah ya cida Amrah da Ammar ko Aiman din .

Ya taba tun karan Tsohuwa da maganar tace ya dakata ba yanzu ba , ashema Allah da nashi ikon komi a saukake zai zo .

Jin kirin da Abbu yayi ba ƙaramin tada hankalin Dr Aiman din yayi ba , yana jin idan har Abbu bai bashi auren Amrah ba to shida aure sai a kiyama idan anayi .

Gyaran muryan da Abbu ya yi ita ce ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi duk zufa ta gama wankeshi .

"Amma dai kaban mamaki Aiman , ban taba tunanin wannan ce damuwar kaba , ai Amrah kai din mai kawo mijin aurenta ne ko da kai baka santa ,

"Ina son ko bayan raina ka zama jigo majin ginar rayuwar Amrah , domin ina ji a jikina Amrah na tare da wata ƙaddara wadda ban san ko wace iri bace , dan haka na baka Amanar Amrah tun daga yanzu har zuwa daukewar numfashin dayanku.
"Aiman ka dauki Amrah tamkar wata Ƙawarka , ko Kanwarka sannan kuma matar ka , idan kai hakan Zaka ji dadin rike Amanar ta da nabaka , na baka Amrah Aiman duk sanda yayi ma a daura maku aure kai da ita , Allah yayi maku Albarka ya baku zuri'a masu albarka,,

Ajiyar zuciyar samun natsuwa Aiman ya yi ko shakka babu yanzu ya ji natsuwa tagame duk ilahirin jikinsa .
Cikin farin ciki yaima Abbu godiya ya nufi gida cike da fara'a .

Hajiya Hindatu na zaune parluor taji an an rungumeta ta bayanta , cikin farin ciki yace "Ummi I'm happy wallahi yau Abbu ya gama yimun komi tun da ya magance mun damuwata , Ummi Abbu ya ban auren Amrah ,,

Sakin baki tayi tana kallon Aiman din.
"Daman akan Diyata Amrah ka shiga damuwa har kasamu a damuwar muma ?
"Amma dai gaskiya naji dadin hakan Diyata dai ta ciri tuta kenan ,,
Ban da yaƙe babu abun da Aiman ke yi , Abbansu na tsaye na jinsu , shima abun yayi mashi daɗi ainun domin hada zuri'a da mal Aliyu alheri ne babba .

MAMANA CE Where stories live. Discover now