[12/01, 6:24 PM] Hauwau Salisu: 🤱🏻🤱🏻🤱🏻 *MAMANA CE* 🤱🏻🤱🏻
*NAH*
*HAUWAU SALISU*
*بسم الله الرحمن
الرحيم*
___________________________________*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________07081095452
*TA'AZIYYAR RASHI GA GIDAN MARUBUTA*
*Allah Ya jiƙan Mahaifin Abubakar Auyo da Mahaifiyar Sa'adatu Vocal.*
'''Allah yasa sun huta yasa aljanna ce makomarsu baki daya'''
*Nima ya jikan *HAJIYARMU* *yasa ta huta ya kai haske a kabarinta Ameen**
😢😢😢*Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ke rayawa da kashewa , ina matukar farin ciki da nishadi yanda kuka anshi wannan book nawa da hannu biyu har banda ikon daga kafa gun typing saisu Haleey anmun ciwon baki 😜*
Page 12 __13
Ya yun kura zai tashi kenan , yaji karamai wayar da ya anshe gun Isah na tsuwa , dan ba ringing take ba kara take marai dadin sauraro .
Ba tare da wata shakkaba. yai picking call din yaki magana,
Waziri da hankalinsa ke tashe bai bari yaji koda gaisuwar da Isah ya saba yimasaba yafara magana.
" Kada ka kuskara ka ambaci sunana gun Ammar kai dai kasan yanda kai ka kwaci kanka gunsa .
Yaci gaba " kafi kowa sanin sirrin da Na jima ina boyewa a masarautar nan dan haka ka iya bakinka .
Azabace nasan kunyi ido hudu da ita dan Ammar mugune takadari dan haka nake San kammala aikina kansa ta hikima da tuggu ba sai nasha wahala ba .Ganin yanata zuba amma Isah bai tanka masaba sai ya dubi wayan . yafara kiran sunan Isah amma still Isah bai maganaba ,
Tsuru yayi yana kallon wayan gaba daya jikinsa zufa ta wanke sa .
Yana niyyar kashe kiran yaji kamar ana magana . dan haka ya sake kan gata a kunnensa idanunsa kuru kuru tamkar ya ci babu .
"Jira nake ka gama bayaninka Waziri .sannan nabaka amsa kasan magana bata dami Yarima Ammar ba . ko dan bai da burin ganin bayan Kowa ne ?
Dif Ammar ya kashe wayar .
Da gudu Waziri ya fada Bathroom ya saki zawo . shi kadai yasan iyakar tashin hankalin da ya samesa a yau .
Yasan halin Yarima sarai dan haka yake komi a natse sarkin Fada shine ya bada gurguwar shawaran fadama Sarki Yarima Na shaye shaye daga fadin magana . to ai ga irin ta nan komi ya kwabe ya gane komi .
Da kyar Waziri yasamu cikinsa ya dan saurara masa ya fito bai tsaya bi takan fadawan da ke gaidasaba ya nufi gidan Sarkin Fada nadinsa a hannu .
Sarkin Fada Na zaune yana nazari da tunanin hukuncin da zasu hakikance sai anma Yarima a Fada dan su jefa Yarima a tozarci. abunda zai sashi fushi da Sarki ,shima Sarkin yai fushi da shi .daga karshe suyi baran baran. har su kuma su samu damar ai watar da kudirinsu.
Ganin Waziri a wannan hali ya saka Sarkin Fada a rudu dan baiga shigowar saba zamansa kawai ya gani gabansa da fuskai tashin hankali .
Da yake shima cikin tunani yake sai ya ga kamarma biyo Wazirin a kayi dan haka ya afka dakinsa da gudu ya datse .
Waziri ganin hakan ya sake sakashi a rudani shima ya bi bayansa yana "karda muyi haka fa tare muke shirya komi.
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...