MAMANA CE page 96__100

530 32 3
                                    

*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3


Page 96__100

Da ƙyal ya samu ya miƙe tsaye cikin tafiyarsa mai kama da ta mai koyon tafiya ya nufi ɗakin da Amrah ta shige .

Ko da kana kusa dashi baka isa kaji sallamar saba ,dan ita kanta maganar da ƙyal take fitowa daga bakinsa .

Tana kwance can ƙarshen gadon sai shashshekan kukanta kawai ake iya juyowa saboda ta ƙudundune cikin bargo.

Tsaye yayi cak yana kallonta, baisan abin da zai iya aikatawa ba yanzu kuma ba kwata-kwata, kanshi ya ɗaure zafin tafiyar Ammar na dawainiya dashi ainun , baisan ya damu da Ammar har hakaba sai yanzu da yayi masa nisa .

A baya yaci buri yasha alwashin wannan ranar ta Angoncinsa da Amrah , sai dai tafiyar Ammar da ciwon Amrah ya ruguza masa komi da komi .

A hankali ya share hawayen da suke ta zubowa daga idanunsa, cikin dakiya da sauran ɗan kuzarinsa ya ambaci sunan ta .

"Amrah lafiya kike kuka ranar farin cikin mu ?

A hankali ta rage kukanta zuciyarta na maimaita mata kalamansa .

_Ranar farin cikin mu_ wannan kalma ta daki zuciyarta ainun .

Ta yama  zai furta wannan maganar a lokacin da bata tare da ainihin masoyinta ?

Inama ace bata raye da tafi jin sauƙin abin da ke ranta, babban tashin hankalinta yanda zatai zaman farin ciki da Aiman bayan Ammar na raye .

Ganin ta ɗanyi shiru da kukan yasamu ƙwarin gwiwar zuwa kusa da ita  ya janye bargon cikin tausan kansu ya janyo ta jikinsa ya rungume , wani marayan kuka ya kwace masu su duka kowa da abin da yasashi kukan.

Amrah jinta jikin Aiman sai taji
Gaba ɗaya ta ida karaya, zuciyarta ta shiga kunci da rudu harta fara hango karshen rayuwarta na kusanto ta ainun, kamar yanda Ammar yace ba zai iya rayuwa babu itaba hakan yake gareta bata iya rayuwa mai tsawo ba tare da shiba.

Kuka mai sauti suke  kowa najin ciwo a ƙasan ransa.

Shikam Aiman kukan yau ce ranar da suke jira shida Amininsa amma tazo masu a baibai ba kamar yanda suka tsara abinsu ba, sunci guri mai girma a ranar auren su haka sun tsara komi kan yanda zai birge kowa ya ba kowa sha'awa harma da mamaki sannan ya zama tarihin da bazai goguba a garin Katsina da kewayenta ba , amma komi ya juya masu Ammar ya shammacesa yayi masa abin da bai zataba , duk da yasan cewa shine mai laifi tunda shine  bai damu da bincikar ainihin damuwar Ammar ɗin ba kwata-kwata .

Kuka suke gwanin tausayi kowa da abin da ke cizon zuciyarsa .

Sai da yayi da ƙyal ya lallashi kansa ya zame ta daga jikinsa ya nufi falo.

MAMANA CE Where stories live. Discover now