*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*
*NA*
*HAUWAU SALISU*
*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*____________________________________*
07081095452
My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3*Ya Allah gamu gareka da dukkan lamurran mu* 🤲🏻🤲🏻
Page 66__70
Gaba dayansu jikinsu yayi sanyi duk sun sadda kawuna ƙasa , kowa da abin da yake tunanowa a zuciyarsa.
Daidai nan Amrah ta shigo da sallamarta .
Daram ! Gaban Anbody ya faɗi gata gidansu marai kunyar yarinyar nan matsayin mai neman gafara ko ya zata kaya masu ?
Sannan ta wani ɓangaren ta taɓa iske Dattijon tai masa kashedin ya raba Amrah da Aiman dan itace zata mallake shi , idan ba haka ba to zatai amfani da dukiyar mahaifinta ta ladabtar dashi .Momyn Anbody kam tiryan_tiryan ta ke hango ranai da taje gunsa da buƙatar ya shiga ya fita ya haɗa auren Baby da Aiman , ya taƙarƙare ya yi ma ta nasiha ya bayyana ma ta abin da ta ke shirin yi bai da kyau sannan tana da zunubi mai girma .
Ita kuwa ta runtse idanu tai mashi rashin mutunci ta zageshi tas tace kuma indai akwai Bokaye a duniya sai ta haɗa auren Baby da Aiman in yaji labari yayi bindiga ya fashe .Ƙara sun kuyar da kanta ƙasa tayi tana mai jin nadama na ratsa gabban jikinta , musanman da ta tuna abin da yace ma ta bayan ta gama ci masa mutunci " Hajiya sai dai kiyi haƙuri domin shi aure nufin Allah ne babu wani Boka da ya i sa ya ƙulla shi in dai Allah bai nufi za'a yi shiba ,,
Lokacin watsa mashi harara ta yi tace "Idan Bokan yazo haɗa auren ka hanashi alaranma uban musulunci ,,
Suna cikin wannan hali Amrah ta shigo dakin bakinta dauke da sallama .
Tsaye tayi ƙiƙam tana ƙare ma mutanen wajen kallo , ganin fuskar Abbu da alamar damuwa yasa tai wurgi da wayar hannunta ta nufesa hankali tashe
"Abbu lafiya ?
"Mi ya faru ne na ganka a damuwa ?Abbu sadda kansa ƙasa yayi cike da damuwa .
Kamar wata zakanya haka ta shaƙo wuyan Anbody ta kwaɗa ma ta mari.
" Wane ganganci da wauta ya sa da ki da gidan nan ?" Akan iyaye na zan iya komi , in nace komi ina nufin komi wallahi,, ta sa ke wanke ta da mari lafiyye , sai sannan Abbu yayi ma ta tsawa ta sa ke ta zuciyarta na ƙuna da ƙuncin rashin zuwanta kafin zuwan Anbodyn gidansu .
I ta dai Momyn Anbody ko ba'a faɗi ma ta ba tasan wannan jarumar yarinyar itace Amrah da ke sama ƴar ta hawan ruwa har ya shafe ta ya shafi Daddyn Anbody .
Ban da harara babu abin da Amrah ke wurga ma Anbody , i ta kam tun da Amrah ta shaƙe ta sai taji tamkar numfashin ta zai dauƙe ba ki ɗaya , yarinyar har mamakin karfinta ta ke , daman can abin da yasa kenan ba ta bari sui abin da zai sasu haɗa jiki tasan kunya zata ji .
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...