*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*
*NA*
*HAUWAU SALISU*
*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*____________________________________*
07081095452
My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*My Wattpad 👉🏻 *Hauwa'u Salisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3*Saƙon gaisuwa gareku kainuwa writer's 🥰🥰*
Page 86__90
Cikin sanyin jiki Amrah ta koma ɗakinta fuskarta ɗauke da tarin mamakin wannan saƙon Ammar da aka bata .
Kan gado ta faɗa ta ɗan yi shiru kafin tai zumbur ! Ta miƙe ta buɗe jakar hannunta na rawa .
Wani matsiyacin leshi ne sai walƙiya yake, cikin sauri ta janyo shi cikin jakar , kamshin turarensa ya mamaye hancinta , shaƙar ƙamshin turaren taci gaba dayi hawayen da batasan ko na miye ba sukaci gaba da zubo mata .
Alamar wasiƙa taji dan haka ta aje ta fito da ita , sai time ɗin taga wasu riga da wando masu kyau ga alama na barci ne , ba ƙaramin birgeta sukaiba ko ba'a gaya mataba an kashe iyayen kuɗi kafin a mallakesu .
Cikin fargaba ta warware waƙisar dan ba ƙaramin faɗuwa gabanta ke yiba tunda taga wasiƙar dama kayan baki ɗaya.
Tsira ma rubutun ido tayi , tamkar ta lashe dan kyan rubutun , (Ana cewa rubutun Likitoci bai da kyan gani to itakam yau ta ƙaryata hakan) fara karanta wasiƙar tayi kamar haka .....
Assalamu Alaiki ya hasken idaniya ta.
Zanso in fara da baki haƙuri dan nasan cewa shine kaɗai abin da zan iya baki a yanzu .
Halimatu tabbas na yarda da maganar hausawa in zakai kiyayya kayi mai dalili sannan kayita kadaran kadahan,
A yau na wayi gari cikin wani mummunan yanayi jin cewa gobe zakiyi aure , auren kuma tare da Abokina aminina wanda banda wanda yakaisa kaf faɗin Abokaina.
Halimatu jin hakan yasa hankalina tashi zuciyata karaya tunanina kaucewa numfashi barazana .
Sai dai ƙarshe na gane bazan iya rayuwa dakeba waje guda gari guda matsayin matar Abokina ba .
Halimatu ni yanzu na wuce ince ina sonki , ko ina ƙaunarki hakan duk yazama karya , sai dai ince ina rayuwane dan sonki da ƙaunarki , Halimatu nasha wahala da gaske kanki domin kece mace ta farko da ta shige rayuwata batare da sanina ko sonaba .
Halimatu ina son kiyimun alfarma guda biyu dan Allah .
Alfarmar farko itace kiyi haƙuri ki rayu da Cikin farin ciki karki zama mai son kai garesa dan Allah , idan kikai haka tabbas nasan da gaske kina sona da san abin da nake so .
Saboda banda banbanci da Aiman indai wajen ganin farin cikin rayuwar kine Halimatu .
Alfarmar karshe itace idan kinji labarin rasuwata dan Allah ki dinga sakani cikin dukkan addu'ar ki , saboda ina da tabbacin bazan iya jure rashinki ba har rayuwata ta daidaita tai tsawo .
Halimatu bansan Aiman yasan da labarin soyayyar mu ko bayan raina ki zama mai sirrinta ta gareshi .
Halimatu idan kun samu zuri'a ina neman alfarmai ku saka sunana dan nasan ko na rayu to banda rabon aure a wannan duniyar mai cike da ruɗani da tashin hankali .
Halimatu ina sonki hakan yasa na tanadi waɗan nan kayan gareki dan ki sakamunsu ranar aurena dake sai dai ban saniba ashe ƙaddara ta riga fata dan haka gasunan kisasu ko yanzu Halimatu ke ɗin ta musanman ce garemu daga ni har Aiman da iyayenmu.
Hakama ƙananan kayan na tanadesu ne dan ki sakamunsu ranar farkon daren aurenmu , hmm ba komi haka Allah ya ƙaddara ke ɗin ba rabona bace ashe zan yi fatan mu haɗe can inda babu mai rabamu ,
Karshe ina mai ƙara baki haƙuri da abin da ya faru tun daga farko har zuwa yanzu , domin nasan cewa bazan jure rayuwa babu keba .
Halimatu duk inda nake kina cikin zuciyata ,dan haka ki rayu cikin aminci da farin ciki ,
San da zaki gama karanta wannan saƙon na tsufa da barin wannan kasar baki ɗaya.
Daga masoyinki Ammar (Ameer).
Tana zuwa karshen takardar ta fasa ihu ta koma ta zame kan gadon ba numfashi .
Anbody da shigowarta kenan gidan taji ihun Amrah dan haka ta faɗa ɗakin da gudunta .
Ba ƙaramin girgiza yayiba da ta gama karanta wasiƙar cikin kuka take maimaita "an cuceku amma kune silan komi ,,
Sai lokacin ta lura da yanda komi na ɗakin ya ke ɗauke da pic ɗin Ammar da Amrah na Aiman ɗin ma baida yawa .
Tabbas rayuwar soyayyar su akwai ban mamaki da tausai .
Haka ta haɗa kayan ta adana ta ruga ta kira Ummu dan ta ga halin da Amrah take ciki .
Da gudu aka nufi hospital ɗin su Aiman da ita .
*AIMAN*
Ya sha mamaki san da ya buɗe kayan da aka bashi wai inji Ammar !
Ba ƙaramin mamaki yayi ba ganin kayan ciki ba , shadda ce mai sunan sadda taci uban aiki na gani a yaba , tare da takalma agogo hula harda su glass da turare .
Ihun daɗi yayi kafin yace "Yaro kana kashe Ni da takunka ,,
Yana cikin zumuɗi na ganin kayan wata guntuwar takarda ta faɗo ƙasa .
Cike da farin ciki ya fara karanta abin da ke ciki .
Zumbur ! Ya miƙe "wallahi baka isaba Ammar akan me zakaimun haka ?
Sake karantawa yayi a fili ..Yaro ga kayan nan ina fatan sunma kyau ?
Ga amanar Halimatu nan gareka idan ka ɓata mata rai ban yafe ba .
Karshe ina baka haƙurin rashin tsayawa gun biki dan yau tafiya ta kamani zuwa wani waje .
Sai wata rana Amini na gari .
"Haba Ammar mi nayima kaimun haka ?
Da gudu ya fito da nufin zuwa gidansu Ammar ɗin yaga an shigo da Amrah tamkar gawa.
Tsaye yayi ƙikam ya rasa ina zashi ?
Amrah zai duba Ammar ya subuce mashi koko ?
Idan ya tafi kuma waye zai duba masa Amrah a halin da take ciki ?
To ku tayashi dubawa dai , miya kamata yayi ?
*Taku Haupha* ✍🏻✍🏻✍🏻
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...