*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*
*NA*
*HAUWAU SALISU*
*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*____________________________________*
07081095452
My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3_Haƙiƙa Ina godiya gareku masoyana ƙwarai da gaske 🙏🏻🙏🏻_
Page 56__60
Tashin hankalin da Momyn Anbody ta shiga ko a jikin Anbody, domin yanda ta ke ji ɗaukar fansar ta yafi komi a tare da i ta yanzu.
Hasali ma hango ci bayan ta ta ke duk sanda Momyn ta buƙaci ta nemo soyayyar Aiman karo na barkatai ta ke yi ,domin Abakar ba ƙaramin nuna kulawa da soyayya ya ke ma ta ba , matsalan sa guda ce matsiyaci ne bai da komi amma i ta wannan bata dauke shi matsala ba tun da tana da kuɗinta hakama Daddyn ta tinjim ya ke da kudin.Ko da ya ke idan ta kalli Daddyn nata ba ta jin daɗin ranta sam.
Amma har ga Allah ba zata sa ke banzar da rayuwar ta ba dan ta na neman tsari da abin da ta aikata a baya .
Momy ta sa ke dubanta, "Baby yanzu ba zakiyima mahaifinki wannan alfarmai ba ? Karfa ki manta daga ni har ke shine jigonmu , sannan dashi muke duk wata ƙarya,,
Ajiyar zuciya Anbody ta yi ta dubi Momyn "Momy ki gane ba zan taɓa samun Aiman ba domin alamar karfi tana ga mai ƙiba,,
Ta share hawayen idan ta "Momy Allah kaɗai yasan adadin gun Bokayen da kika je kan lamarin auren nan ,to nima haka ne ban san adadin Mazan da na kwanta dasu ba dan cikar burina, amma karshe Aiman ya gayamun maganar da ta dasamun haƙurin aurensa kuma na haƙura don in samu Allah ya yafemun laifukan da na aikata a baya ,yanzu a bu guda ya rage shine mufara bincike ina malamin ya ke dan neman waraka ga Daddyn,,Cikin hawayen baƙin ciki Momyn ke kallon Anbody .
"Yanzu kina so ki shaidamun kin sai da mutuncinki a banza kenan Baby ?
"Duk san kuɗina bana bari a taɓa mutunci dan shine mafi girma agun mijinki ranar ku ta farko ,,
Ta fashe da kuka "kin de ji haushin wannan baƙin hali da kika aikata ,tabbas kema taki nadamar na tafe a gidan auren ki,,
Cikin kuka Anbody ke roƙon kar Momyn tai ma ta baki .Duk maganar da suke yi ba wadda Daddyn bai jiba .
Hawayen nadama da takaici suka wanke mashi fuska ,Hakika ya aikata kura_kurai masu girma a rayuwarsa , ya ci hakkin jama'a da dama dan gina kansa , ya cutar da mutane da dama dan ɗorewar farin cikinsa ,yau gashi in da rayuwa ta kaisa.
Taƙamarsa son kuɗi sai ya auri wadda ta fishi son kuɗin,
Ahankali ya fara tunanin rayuwar sa ta can baya .Tuna baya shine roƙo.
Tun sanda ya fara harkokin sai da taba (wiwi) ko da yaushe cikin taka tsantsan ya ke da ma'aikata musanman da Abokinsa ne shugaban ƙungiyar yaƙi da miyagun ƙwayoyi, ya sha samunsa a sirri ya yi mashi faɗan sana'ar miyagun ƙwayoyin da yake , ya kawo jari mai tsoka ya bashi dan samun wata sana'ar amma bai ganin akwai sana'ar da ke kawo kuɗi sama da ta tabar.
Dan haka ya ke biris da shawaran Abokin nashi ya ƙi daina fataucin miyagun ƙwayoyin.
Sanadin haka sukai baran_baran da Abokin nashi , hakan bai dameshi ba sai da ya samu labarin aje aikin Abokin nashi wanda yasan dan shi ya aje aikin .(mahaifin Aiman kenan)
Daman ance rana dubu ta Ɓarawo ɗaya ta mai kaya .
Kwatsam aka kamashi tare da kaf kayansa a taƙaice ya zama matsiyaci na gaske har ya fara zuwa kasuwan nin ƙauyen katsina yana samun dako da sauransu,
Mal. Saminu shine dattijon dake kulawa dashi duk ranar Alhamis idan ya je cin kasuwar Batsarin . dattijon yana awon hatsi sosai dan shike sauke mashi lodin kayanshi idan yazo daga ƙauyen su mai suna Sararraki .wasa_wasa Mal. Saminu ya amince dashi har ya fara bashi tsaron kayanshi idan zai je wani gun.
Sannu a hankali ya fara zuwa da yaronsa Aliyu duk da yaron ƙarami ne sosai , ana cikin haka ya shammaci Mal.Saminu ya haɗa baki da wasu masu son zuciya yayi cinikin kaf hatsin mal.Saminu .
Da ya ke sai anbi ta daji ake wucewa ƙauyen su sai ranar kasuwar suka tare motar akori kurai da tayo lodin hatsin mal.Saminu wanda ya ba waɗan can shi suka sallamesa ya koma gida ya fara sana'ar saro gwanjo da kudin dan suna da dama sosai ,har Allah yasa aka fara damawa dashi a sahun masu kudin Katsina.
Yanzu ina zaiga Mal. Saminu ya maida mashi dukiyarsa ko dan ya samu warakai ciwon da matarsa ta siyo mai da kuɗinsa ?Cikin kulawa da fara'a Amrah ta yaye bargon da ke lullube da Fulanin .
Daram ! Gabanta ya faɗi dan ganin fuskar wanda ke kwance kan gadon ,Dan tsorace ta furta Ammar !
Sai kuma ta maze ganin ya sa ki baki hanci dasu idanuwa yana kallonta.
Cikin tsiwa tace "mi zan gani haka namiji da suna Hajara?
Sai time din ya dawo natsuwarsa,Ta sa ke murguɗa ɗan ƙaramin bakinta "Daman inasan magana dakai mai cike da kashedi na musamman ,daga rana irinta yau karda na ƙara ganin kiranka a wayata in dai ba kalaman ban haƙuri zaka kira dan ka fadamin ba ,
Ta sa ke kallonsa ta taɓe baki ,
"Naga duk ka rame ka ƙwanjame ko dai ta fara ƙaramane Ammar uban izza da gadara ?Banda huci ba abin da Ammar keyi ,ko tantama baiyi ba sanda ya ganta har ga Allah yasa haƙurin tazo bashi har ya tafi duniyar tunanin yanda zai gama yaƙunata kafin ya yafe ma ta laifin ta.
Ganin sauyin yanayin sa yasa Amrah saurin ja da baya nufinta ta arce daga ɗakin, sai dai ta makara dan jinta tayi riƙe gam a hannunsa ,
A gadaran ce ya dubeta da fuskar shanu yace "Yau zan maganin rashin kunyarki Halimatu , sai kinyi nadamar sanina a rayuwarki,,
Mutsu mutsun kwace kanta daga gareshi ta keyi amma ta kasa hakan yasata nufar hannunsa da nufin gartsa mashi cizo.
Cikin zaro idanuwa ya kalle ta kafin ya turata ta faɗa kan kagon.
"Daman samun nasaraiki kenan ki ciji mutum da wasu ƙananan haƙoran ki kamar na maciji,,
Tsabar tsiwa sai da ta maida mai raddi.
"Ga ra dai ni ai ban taɓa wage bakina kan titi naima ƙanwata kukaba"Mikewa tsaye yayi ya fisgota ya haɗa da bangon ɗakin ya matseta .
"Kinyi wautar jayayya dani Halimatu kuma zan nuna maki kuskurenki ,,Gatsina mai baki tayi "zamu dai ba juna wahala dan kana mun kan kara zanma na itace wallahi,,
Dalle ma ta bakin yayi da yatsa "ki kula da kalaman ki kaina ,,
Tureshi ta fara yi amma ko gezau dan haka idan ta ya fara rena fata .
Sai dai tanajin ko shaƙar da zai kasheta yayi ma ta bazata iya rusuna mashi ba .
Dan haka ta takura ta wage baki zatai ihu .
Kawai ji tayi ta ka sa shaƙar numfashi ya doɗe ma ta hanci da baki .Cikin ikon Allah sai ga Fulani ta faɗo dakin.
Amma ganinta baisa Ammar ya saurara ma Amrah ba , sai ita Amrah data dinga yafuto Fulani da hannunta .
Fulani mamakin Ammar ya hanata matsawa daga inda ta ke ,ga alama dai faɗa suke amma sai murmushi ya ke kamar wanda ke cikin farin ciki .
Tsawa tayi masa sannan ya rabu da ita ya juya da nufin fita ,komi ya tuno ya juyo yace "Na rantse duk sanda zamu haɗu in dai kikai mun rashin kunyar da kika saba saina sa ki kuka ,,
Ya fice abun sa.Tun da ya shigo ɗakin yake ganin abubuwan ban mamaki da al'ajabi wanda suka ɗaure mashi kai game da Abokin nasa .
Yabi bangon ɗakin ya zane da harafin H shin miyake faruwa ne ?
Yasha faɗi mashi saboda tsanar da yayima Halimatu Tantiriya ko kalmai H baiso yaci karo da ita gun rubuta magani but why ya zane ɗakin da kalmai H ɗin ?
Hango wani ƙaramin littafi yayi mai daukar hankali saboda adon sa , cikin sanyin jiki ya miƙa hannunsa da nufin daukar littafin ,"Karka kuskura ka daumin book Aiman,,
Cikin Wata razana ya juyo ya kalli Ammar ɗin ,sa ke zaro idanuwa yayi cike da mamaki .
Da hannu ya nunasa "Ammar ka ......Ko mizaice ?
Yaya Daddyn Anbody zai kasance ?
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...