[12/01, 6:20 PM] Hauwau Salisu: 🤱🏻🤱🏻🤱🏻 *MAMANA CE* 🤱🏻🤱🏻🤱🏻
*NAH*
*HAUWAU'U SALISU*
___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation___________________________________
07081095452
*May Allah distance U from shame & failure, destroy every evil plan against U & Ur loved ones, protect U from known & unknown enemies, May Allah (SWT) support you & your family with His Love, Kindness, Mercy, Blessings & Forgiveness... May you continue to enjoy Allah's Rahmah, Ni'imah & Protection till Yaumul Alkiyamaah, Ameen Ameen. Jumma'a Mubarak.*
Page 9
Kai tsaye side dinsa ya nufa , kan doguwar kujeran dake parlourn ya fada. yanajin wani mugun ciwon kai , ga yunwa nadamunsa, amma baijin zai i ya saka komi a bakinsa ,
Sukansu fadawan nasa kowane a tsure yake , sunsan duk taje ta dawo kansu bala'in sa zai sauka,
Zumbur , ya tashi zaune cikin bacin rai ya kwada masu kira ,
Bawanda gabansa bai fadiba , jin kiranda Yarima yai masu dajin muryansa akwai damuwa tattare da bacin rai.
Suduka, suka gurfana a gabansa . kowa na ambatar sunan Allah a zuciyarsa ,
Da wani rikitaccen kallo yabisu daya bayan daya , fuskarsa ko kadan babu alamar rahma ko rangwane .
Sadda kawunansu suke suka ci gaba da bashi hakuri , duk da basusan abunda yafaruba amma sunada tabbacin yau sun shiga tara gun Yariman .
Saida ya tabbatar da kallonsa ya gama tsinka masu 'yan hanji sanan yabude baki da kyal yai magana.
"Yaushe Ameer ya fara shaye shaye ?
"Ubanwa yaga Ameer na shaye shaye ?
,,Da akwai likita kusa ya auna jininsu tabbas zaiga yanda ya hau over .
Cikin bacin rai ya mike "daga yau bazaku sakema Ameer karyaba , Na rantse da Allah saina dandana maku kwatankwacin bacin randa kuka jefa zuciyata kwana biyu .
Datse dakin yai da makulli ya koma kan kujerai ya kwanta "zamu dauwama daku a haka har sai kunfadamun ubanda yaimun kazafi gun mai martaba .
Kunfi kowa sanin halina banasan karya da makaryaci "Adam yai gyaran murya, alamai akwai abunda yake son fada.
"Inajinka Adam "
Cikin rudewa da tashin hankali Adam yace "Allah huci zuciyar ka , bada cikinmu bane ,
,,To daga cikinsu uban waye ?" Ranai da akai abun naje zan wuce kofar dakin mai martaba naji Waziri nabashi labarin yanzu Isah , Direbansa yadawo daga aiken da yaimasa GRA yaganka tsakiyar titi a buge harma wata yarinya na tsokanarka .
Wani uban naushi yakaima glass din kusa dashi , ya tarwatse ,
Cikin daga murya yace "Ku kaominshi nan amma kutabbatar dashima ya bugun da kyau .
,,Sudai fadawa ganin sun tsira suka nufi kofa, bakuna cike da godema Allah sun fita tarkon Yarima .
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...