MAMANA CE page 76__80

523 31 1
                                    

*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3



_Allah na gode maka da ko da yaushe kake haɗa Ni da masoyan gaskiya da gaskiya_ 🙏🏻🙏🏻🙏🏻

_Yau kam bansan irin me zance ba Allah abin ya taɓa raina_  😥😥😥😥😥😥😥

*Nagode Nagode Nagode* 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻



Page 76__80

Hawaye masu zafi suka zubo mashi, bai damu da gogewa ba ko ganin Fadawansa a gun ba , burinsa ta rama marin tace ta yafe masa kawai .

Amrah komi ya tsaya ma ta gadai ranai da ta daɗe tana jiran zuwanta , tazo ɗin amma ba ta zo ma ta a daidai ba, ta na jin tamkar ba itace ba .

Da Amrah tasan shurunta na ƙara razana razanar nan zuciyarsa da ta jima da yanke masa hukuncin da duk tai niyya.

Cike da tashin hankali ya ɗago jajayen idanunsa ya kalleta, "Halimatu ki taimaka mun kada sonki ya ida illatar da rayuwata pls kimun afuwa ,,

Basu ankara ba suka ga ya dafe kirjinsa ya fara tari tamkar zai suƙe , jini ya biyo bayan tarin ya yanke jiki ya faɗi gun a sume .

Wata ƙara Amrah ta saki itama ta zube gun a sume .

Cikin tashin hankali Fadawan suka fara kikiniyar taimakonsu amma tsit kake ji .

Sun yanke shawarar kwasarsu dan su nufi asibiti kenan Amrah ta farka .

Cikin kuka ta riƙe hannunsa.
"Bai kamata ka hukunta zuciya ta hakaba , nasan ni ɗin mai tarin laifukace gareka Ameer , amma sai ka duba amincin zuka tanmu kaimun lamunin dauwama tare da kai ,,

Adam da kukansa yafi na sauran yace .
"Kiyi hakuri Gimbiya mu kaishi asibiti zaman haka tamkar ƙara nesan tashi da rayuwarsa ne,,

Ɗau ! Amrah ta dauke shi da mari , tamkar mahaukaciya ta cakumo rigarsa .

"Na rantse da Allah ko da kowa zai mutu ya barni jikina na bani Ameer bazai taba barin Halimatu ba,,

Ta sake shaƙe mai wuya gam. Sannan ta rushe da kuka ,

"Nayi nadamar jan ran da naima Ameer hakan yasa na kasa yafema kaina ,,

Tarin da ya fara ne yasa ta afkawa kanshi a haukace .

"Na faɗa masu baka tafiya kabarni daman , saboda da kai kaɗai na ke iya rayuwata Ameer ,,

Cikin karfin hali na gasken gaske ya fara share mata hawayen fuskarta .

Da gudu su Adam suka nufeshi da nufin kamashi .

Cike da tsawa Amrah ta dubesu "kar wanda yazo kusa damu ko anfaɗa maku wani abu ne ?

MAMANA CE Where stories live. Discover now