MAMANA CE page 7__8

740 43 0
                                    

[12/01, 5:59 PM] Hauwau Salisu: 🤱🏻🤱🏻🤱🏻 *MAMANA CE* 🤱🏻🤱🏻🤱🏻

       *NAH*

*HAUWAU'U SALISU*

___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

___________________________________



07081095452

Page  7

Tana zaune taji yakamata taje gun matar gidan ta ganta mai Allura yace mata Umminsace wai,

Tana gama tunaninta ta mike da gudu ta nufi side din Hajiya Hindatu tana kwada sallama tun kafin tashiga parlourn ,

Hajiya Hindatu na zaune tana kallon tashar Zee Aflam sun sako film din *three idiot*  dai dai gunda Amirkhan zai anshi haihuwar yayar Kareena khapoor , ya leka cikin mayafin da aka rufeta kenan yaga ko kan Dan yafara fitowa ,

Cikin mamaki da al'ajabi Amrah ta isa gaban TV ta dungure masa kai ,

,,Babba dakai ashe baka da tarbiyya sai kattin kunnuwan kawai ?

Ku kuma kunata kallonsa kungaza hanasa leka mata Nigeria ta ko? Ta maida dubanta kan sauran Abokansa dake gun ,

Hajiya Hindatu dariya ta kamata sosai wanda harta dafe cikinta wannan  yarinya da abun dariya take ,

Dr Aiman da shima fitowarsa kenan da nufin yaje ya gaida Umminsa yatafi gun Dr Ammar yaga shigowar Amrah dan haka yatsaya yaga abunda yakawota ,

Shima dariya ta bashi sosai kodayake da larabci suka fassara film din ba hausaba kilan data gane haihuwace zatayi ba  rashin tarbiyya akeyiba ,

Jin dariyar Hajiya Hindatu yasa Amrah juyowa ai kuwa da gudu ta nufi gunta tafara jan hannunta yauwa,dan Allah kimasa magana kinga yanata leka mata Nigeria tanata kuka bataso itakam da tarbiyyarta sauran daine basu da ita ,

Shafa kanta Hajiya Hindatu tayi tana murmushi ,, miye Nigeria kuma ?

Rufe fuskaita tayi ai Kakatace ke fadamin nan ( ta nemi hankada zanin  Hajiyar waita gwada mata ) Nigeria ce nan dan haka ake boyeta rashin tarbiyace kesa ana wasa da ita ko kallonta ,

Hajiya Hindatu tai dariya ta ce lallaikam kaka ta fadi gaskiya amma sakarmun zane kokema leka Nigeria  zakiyi ?

Cikin jin kunya ta rufe fuskaita tana murmushi ,

,bafa lekawa zanba gwada maki kawai zanyi dan dayan sunan bai faduwa ,

Haka kawai Hajiya Hindatu taji yarinyar ta kwanta mata aranta jitake dama ita ta haifeta  yarinyar nada abun mamaki gata da gani bata da wasa ,

Nace Hajiya tambayi Ameer kisha labarinta😳🏃🏻‍♀

Dr Aiman ganin dramai tasu bamai karewa bace yasashi idasowa gunsu yana fara'a ,

Da gudu ta kamo hannunsa ,, mai Allura naita nemanka bangankaba tun jiya  naima dundunka tunda Abbu bai warkeba har yanzu bai gani ka duka kawai( taita kokarin dukar dashi dantai masa kullin abayansa )

Dariya yai mata ,,dakata kiji ai ban gama bashi maganiba balle kicika alkawarinki kaina Baby ,

Yatsine fuksa tayi ,,nifa Babyn nan baganeta nakeba Amrah nasan Abbu nakirana ehe,
Hajiya Hindatu tai murmushi gaskiya kadaina tunda bataso kadinga kiranta da sunan da bataso daga yau ,

MAMANA CE Where stories live. Discover now