MAMANA CE page 131__end

772 45 2
                                    

[05/03, 8:27 PM] Hauwau Salisu: *🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

*Dan Allah Kuyi haƙuri kwana biyun nan sai a hankali ne* 👏🏻👏🏻👏🏻

Page 136__140

Gaba ɗayan su jikinsu yayi sanyi ƙalau dan basu da tabbacin farkawar ko ɗaya daga cikin majin yatan nasu.

Abbu banda hailala babu abin da yake yi , sai yanzu yake nadamar ƙin yarda da shawarar mai ɗakinsa Ammu , da ya aminta Amrah ta auri Ammar da yanzu basu shiga cikin damuwa ba, hakama da yanzu su Ammar ɗin suna cikin kwanciyar hankali ƙilama an samu ƙaruwar iyali .

Ammu tayi iyakar ƙoƙarin ɓoye damuwarta amma abin yaci tura daka ganta kasan tana cikin damuwa mai tsanani .

Saura awa biyu lokacin da Likitocin suka ambata ya cika amma babu wanda ya farka daga cikinsu .

Gaba ɗayansu iyayen suka nufi masallacin asibitin suka fara jera nafilfilo Abbu ya dage iyakar iyawarsa da saninta yana ta kwararo addu'a suna ansawa da ameen.

Dr Anam kansa na kife kan table ɗin dake office ɗinsa , babban tashin hankalinsa shine basu da tabbacin idan akai masu musayar zukatan zasu miƙe domin bai taɓa cin karo da ciwon zuciya mai tsanani irin nasu Ammar da Amrah ba . Sake ɗago kansa yayi ya sauke akan agogonsa saura minti talatin cif lokaci yayi ba wani alamar nasara,  hawaye suka zubo masa masu ciwo , tabbas zai yi rashin ɗan uwa kuma aboki sannan ƙasar Nijeriya ma zatai rashin babban Likitan zuciya wanda babu shi a cikinta .

A galabaice ya fice daga office ɗinsa zuwa masallacin asibitin shima yabi layinsu Abbun dan ya sadakar Yarima Ammar sai wani ikon Allah kuma zai tada kafaɗunsa shida masoyiyar tasa Amrah Aliyu .

Dai_dai sanda agogon ya buga cikar wa'adin idanun Ammar suka fara buɗewa suna lumshewa a hankali , sai dai da tsiya ya nemi budesu don ganin gaskiyar abin da suke masa gizo .

Wannan karan da duk wani ɗan sauran kuzarinsa ya wage idanun nasa suka sauka akan gadon , tana kwance shambal kamar gawa bata numfashi ko kaɗan .

Cikin wani karfin da yazo masa na bazata ya yunƙura ya miƙe zaune idanunsa akanta fatansa kada ace mafarki yake yi .

Cikin rashin karfin jiki ya isa inda gadon yake ya ƙura mata idanunsa da suka ƙara girma dan azabar ramar da yayi .

"Halimatu !
"Halimatu !
"Halimatu !

Ganin bata san yana yiba ya sashi fara yamutsa gashin kansa , idanunsa suka koma ƙanana dan azabar firgita , (kar dai ace ta mutu ?)tunanin da ya faɗo masa a ransa kenan.

Hannunta ya kama yaji jijiyar na bugawa a hankali , ai da sauri ya fara duddubata kafin kace me ya fara ƙoƙarin ceto rayuwarta cikin ƙwarewa, yana yi yana ambatar sunanta cikin halin shauƙi da bege .

MAMANA CE Where stories live. Discover now