MAMANA CE page 28__31

545 36 0
                                    

[12/01, 6:28 PM] Hauwau Salisu: 🤱🏻🤱🏻🤱🏻 *MAMANA CE* 🤱🏻🤱🏻

                *NAH*

      *HAUWAU SALISU*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________


07081095452

Page 28__29

Falon yayi tsit bakajin komi sai sautin kukan Anbody. Mahaifinta da Mahaifiyarta na zaune sun zuba mata idanuwa ransu bace , musanman mahaifinta .

"Nagaji da yawo da kike gotai gotai babu Aure Badiyya , ya zama wajibi yau ki fadamin wanda kike so idan ba hakaba tabbas nizan zaba maki wanda naga ya dace dake ,,

Tasake rushewa da kuka , "wallahi Daddy ina da wanda nakeso duk tsawon shekarun nan ,,

Sai time din Mahaifiyar ta kalleta "Au da kina da wanda kike so amma dan shashanci baki gabatar dashi anyi komi an wuce gunba ?

Itadai kukanta kawai takeyi tasan ko mutuwa zatayi Dr Aiman bazai taba takowa inda takeba da sunan soyayya , yariga ya fadamata soyayyaisa tun tana jaririya ya reni abunsa akanta ya fara akanta ya gama,  taje gaba shikam baida ra'ayin auren Babbar yarinya yafi son karama ,

Yanzu ita ya ya zatayi da kaunarsa datakeyi ?

Uban ya daka mata tsawa "Shidin waye Ubansa da zaiki ki ? Miyake takama dashi wanda Ubanki baidashi ? Shin baki fada masa kedin 'yar babban gida bace ?

Wani kukan yazo mata sabo dal 😭

"Daddy yandafa kake takama da Dukiya haka shima mahaifinsa yake tutiya da Dukiyar , a gefe gudama sainace shima Dukiyarsa takai taka koma tafi taka Daddy , yanda kake Babba a garin Katsina haka shimafa yake Babba,,

Su dukansu suka zuba mata idanunsu , "To baida sunane shidin ? (Fadar mahaifiyarta)

Cikin sharben kuka tace "Sunansa Dr Aiman dan gidan mataimakin Governor fa shine na jima ina kaunarsa Daddy ,,

"Wallahi sai dai ki mutu babu Aure da ki Auri dan dan wannan Shegen Mutumin Badiyya ,,

Nan da nan bacin ransa ya ninku fiye da farkon zamansa gun , itakanta mahaifiyar ta razana da jin wanda 'yar tata ke kauna tasan ko sama da kasa zasu hade Alh . bazai taba yarda 'yarshi ta auri dan gidan Alh Shafiu ba ,

Wannan karan Badiyya tsaida kukanta tayi ta zubama Daddyn nata idanuwa alamar karin bayani ta ke bukata daga garesa .

Cikin fuskar bakin ciki da takaici Alh . Nasir ya fara bata labarin abunda ya faru wasu shekaru can baya da suka wuce .

Kasancewata ba Uwa ba Uba na tashi gaban wata Goggonace wadda Allah bai mata koda digon tausai bane a ranta , ni kaina tasha fadin badan batada Da bata da Jikaba da bazataga tsiyar da zata sanyata rukona ba , haka na tashi da dadi ba dadi har nayi wayau na gama primary nawuce secondry amma sainaci bording school wanda hakan ya konama Goggo ranta sosaima dan ina mata talla ba laifi , badan tasoba ta hadamun abunda taga dama na wuce makarantar , acan ne na hadu da Muhmd shine Abokina na farko sai dai yafini kokari nesa ba kusaba hakan na matukar konamin rai dan dai banda yanda zanyine kawai gashi Abokina dan haka duk yanda muke shiri da anyi jarabawa naga ya fini maki to hankalina bai kara kwanciya harsai an kwana biyu na manta sannan zan saki jiki mukoma kamar da , duk da yana kula da yanda nake sauya masa idan mukai jarabawa amma sai ya nunamin baima gane wane hali nake ciki ba .

MAMANA CE Where stories live. Discover now