MAMANA CE page 51__52

482 33 0
                                    

*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

Gmail👉🏻 *Hauwausalisu407@gmail.com*

Wattpad👉🏻 *Hauwausalisu*

Facebook👉🏻 *Hauwa'u Salisu*

_Ya Allah kai mana maganin abun da bamu iyawa 🙏🏻_ 🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Page 50__51

Sarki ganin sun yi shiru cikin alamun sanyin jiki ,ya sa shima nashi jikin yayi sanyi .

Abbu ne ya yi karfin halin yin magana "Wato Ranka shi dade munji dadin maganar ka kwarai da gaske , sai dai wani hanzari ba gudu ba , Yarinyar mun riga mun zaɓa ma ta Ɗan'uwansa (Aiman ) matsayin Miji gare ta , tabbas ba dan hakan ba da munfi kowa farin cikin wannan lamari"

Allah Sarki !

Tun da Abbu ya fara magana hankalin Sarki ya tashi ainun don ba ƙaramin so ya ke ma Amrah ba, ya so ƙwarai ta zama mata ga Ammar .

Haka dai suka rabu fuskar kowa ba dadi .

Bayan tafiyar su Abban Aiman ya dubi Abbu "mi zai hana mu ba Sarki wannan damar tun da bama lallai bane ita Amrah tana son Aiman din ba ?
Murmushi Abbu yayi "Da Ammar da Aiman duk daya ne , dan haka kama bar wannan maganar"

Ita kan ta Ammu da ta ji maganar sai da ta yi mitar dama an bashi dan ya jima ya na son ta ,,

Kallon mamaki Abbu ya yi ma ta , " yaushe ya fadi maki yana son ta ban da labari ?

Labarin shakuwar Amrah da Ammar din ta bashi tas.
Ya jin_jina lamarin ƙarshe ya yi fatan Allah ya sa hakan ya zama alheri garesu ,,

Fulani ma da Sarki ya bayyana ma ta yan da sukai hada hawayen ta don tana jin Amrah sosai a cikin zuciyar ta.

Abun duniya duk ya bi ya dami Momyn Anbody domin dai Anbody ta kafe kan cewa i tafa ta fasa auren Dr Aiman harma ta sami wani tsohon saurayin ta ya dawo sun dinke .
Da ta furta hakan sai Daddyn ta ya ya fadi ƙasa numfashin sa ya sarƙe ya dinga jijjiga yana zubar da kumfa ta bakinsa .

Hakan ya san ya Momy garzaya wa gun Malamin ta don ya warware kullin da akai masa .
Sai dai ya tabbatar ma ta da cewa "ƙullin mai wahalar warware wa ne cikin sauki ,sai dai ta je ta san dubarai da tayima yarinyar akai auren kawai ,,

Ba ƙaramin razana ta yi da jin kalaman Malamin nata ba .

Haka ta dawo gida hankali ta she har tana jin wani abu mai kama da nadama na ratsa zuciyarta .

_Anbody_

"Hello kai wai raina mun hankali zaka yi ne ko ko ?

''Sati ke nan da baku aiki amma ba wani motsi dan iskanci ''

"Allah dai ya taimaki Hajiyata aikin ki muna cikin sa , matsalai Yarima bai gari amma yana dawowa komi zai normal ''

Wani matsiya cin tsaki ta ja '' Ya maganar shegiyar yarinyar nan Amrah , kun dace kuwa da i tan?

MAMANA CE Where stories live. Discover now