MAMANA CE page 71__75

443 35 16
                                    

*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

Page 71__75

Amrah da tun da ya tunkaro su ta ji ya bala'in birgeta kayan sun karbi jikinsa sosai.
Buɗe kofar bai sa Amrah ta motsa daga in ta ke ba , shi kuma buɗewar da yayi yana nufin kowa ye cikin motar ya fito waje .

Sarai ta fahimci mi ya ke nufi ,dan ko tsaki yayi tasan mi tsakin ke nufi ,balle wannan da ya bayyana buƙatarsa fili .

Shi kuma i yakar ƙuluwa ya ƙule dan ya tsani rainin hankali irin wannan, ba ma girmansa bane cikin mutane ai mashi hakan .

Cike da ɓacin rai ya dunƙule hannu ya tarwatsa gilas din motar ta baya .

Cikin razana Anbody ta yunƙura ta fice daga motar ta zube gabansa cikin kyarmar murya zata fara bashi hakuri .

Sai time din Amrah ta dade da 😎 fuska haɗe ta dakama Anbody tsawa .

"Mi zan gani haka Sister ?

"Tun da ya nuna mana shiɗin matsiyacine dan an daki waccan akwalai motar ta sa shine ya zo yana cika yana batsewa ya rama ,,

Ta i sa gabansu cikin takun jan hankali ba annuri ko kaɗan a fuskarta .

Saukar muryanta ya haddasa masa mutuwar jiki , lokacin da yai arba da fuskarta kaɗan ya hana shi sulalewa ƙasa.

Wata jar doguwar riga ce jikinta fuskarta ba wata kwalliya ta caɓa ma ta ba dan haka sai tayi wani kyau na daban.

Cike da tsiwa ta i sa gab da shi , "ka ce wannan hanyar kuma aka koma ?

"To na rantse da Allah sai ka biya motar can da ka ɓata ,,

Kowa gun sai ya yi tsit ,fadawa suka sauke kawunan su ƙasa.

Anbody ta sha mamakin Amrah , tasan daman yarinyar ba ta da sauƙi ga ruwan rashin kunya amma batai tunanin abin nata ya kai har ta i ya yima Yarima Ammar haka ba .

Shi dai kallonta kawai ya ke yana jin suya a zuciyarsa ko shakka babu kaunarta zata zama sanadin mutuwar sa.

Bai ce ma ta kala ba ya shige motarsa ya jawo ta ya tare ma ta hanyar da zata wuce ,

Ya dube ta kamar bai san magana yace "Na rantse da Allah ko zaki wuce ta nan sai kin ban hakuri har ƙasa yarinya ,, ya sa aka fito masa da kujera ya kame bisa yaci gaba da latsa wayarsa .

Ganin haka i ta dubeshi da fuskar shanu tace "ina taya mu murnai kwana kan titi Yarima Ammar ,,ta shige motarta ta kunna kiɗa.

Abin sai ya ba mutanen da suka fara taruwa gun mamaki dan kowa yasan waye Yarima Ammar a  kaf garin, to i ta kuma wacece da har ta ke ja da shi haka ?

MAMANA CE Where stories live. Discover now