*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*
*NA*
*HAUWAU SALISU*
*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*____________________________________*
07081095452
My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*
My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3*Ina mai baku hakuri kan rashin jina kwana biyu* 👏🏻👏🏻
Page 80__85
Ganin suna neman raunata junansu yasa ta fasa uban ihu !
"Amrah lafiya kina barci kina ihu haka ?
Murtsuke idonta tayi , ta miƙe zaune daga kwancen duk zufa ta gama wanke mata jiki .
"Ummu mafarki nayi marar daɗi wallahi,,
"Anya kina addu'ar barci Amrah ? (Inji Ummu dake kallon Amrah da alamar mamaki)
"Ummu nayi addu'a Allah kawai dai nayi ne ,,
"Shikenan maza kije ki watsa ruwa kizo muyi magana,,
Tun da Amrah ta shiga wankan hankalinta ke a tashe ,domin abin ya tsaya mata a rai ainun .
Hajiya Hindatu lamarin Amrah ya fara sha mata kai ainun, domin yarinyar duk ta bi ta fita hayyacinta, hakan na damunta sosai a rai domin matsayin ɗiya ta ɗauki Amrah ba wai ƴar riko ba.
Amrah kuwa da ƙyal ta samu ta watsa ruwa ta fito ta sanya doguwar riga marar nauyi ta sake hayewa gadonta ta lafe domin tana hutun sallah .
Ummu jin Amrah shiru ta aiko mai aikinta kiran Amrah .
Jiki sanyaye ta nufi kiran Ummun , su kansu ƴan aikin mamakin sauyawar Amrah suke yi kwana biyun nan.
Daidai sashen Yah Aiman ta jiyo sautin muryarsa yana waya sai gaggaɓa dariya yake tamkar wani sabon kamu.
Wani matsiyacin haushinsa ya dira a zuciyarta, tsanar aurensa ke kwaranya cikin jinin jikinta ta ko'ina ,tsiririn tsaki taja ta wuce fuu .
Tun da ta shigo Ummu ke kallon yanda ta rame ta fita hayyacinta kamar wadda ke kwance gadon asibiti .
Cikin kunyar Ummun da ita kanta bata san ta micece ba tace "Ummu gani ance kina kirana,,
Kallon mamaki kawai Ummu ke mata baki buɗe.
"Amrah yaushe kika sauyomin matsayi daga na Uwa zuwa wata mata daban ?
"Shin Amrah na taɓa yanke maki wani hukunci da bai maki daɗi bane da kika sauya min matsayi ?"Allah ya sani da zuciya ɗaya nake zaune dake a matsayin ɗiyata Amrah , ashe ke ba haka bane daga gareki,,
Kuka ya kwacema Amrah na firgita da tashin hankali, cikin gunjin kuka tace...
"Ummu wallahi ba haka bane , ban sauya maki matsayi ba ko kaɗan,,
Cike da ɗaure fuska Ummun tace ....
"To indai ba haka bane miyasa kika boyemun damuwarki ?
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...