[22/02, 1:12 PM] Hauwau Salisu: *🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*
*NA*
*HAUWAU SALISU*
*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*____________________________________*
07081095452
My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3*Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun* !
*Dan Allah masoyan Haupha ku sakamnun Name Sake ɗita addu'ar Allah yaba ta lafiya tana cikin halin rashin lafiya kwance Hospital tayi Bari😢 ya Allah ka bata Lafiya ka azurta ta da wasu rayayyu masu albarka Ameen* 🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Page 106__110
Duk abin da ke faruwa Aiman bai saniba barcinsa kawai yake duk daren duniya zai janyo ta jikinsa ya rungume yaita sheka barcinsa hankalinsa kwance .
Ita kuma Amrah tun tana tunanin Aiman zai nemi wani abu daga gareta harta daina, zai dai yagalgala ta yayi wasa da ita son ransa, ta saba kwarai da lamarin yanda ko da yaushe yana manne da ita indai yana gida , sai dai hakan na ƙara ƙarfin gwiwar ƙara yanke wa da sake ganin Ammar musanman da kullum sai tayi mafarkinsa cikin mummunan yanayi mai ban tausayi mai tsayawa a rai, hakan yasata fara azumi dan nema mashi ɗauki kan lamarin da yake ciki .
Duk tabi ta rame ta fita hayyacinta ainun ga can cikin zuciyarta tana jin kunar da ke ƙara ramar da ita .
Aiman ba ƙaramin tashin hankali yake shigaba duk sanda ya dubeta ji yake tamkar bai riƙe alƙawarin da Abbu yabashi kan Amrah ba .
Yayi duk wani abin da ya kamata kanta amma dai still bata canza zaniba ga ta dage sai wani azumi take ya rasa ko na miye ga yana yawan kamata tana kuka innaya tambayeta tace ai tana tuno Dr Saudat ne .
Kamar yau ya fita gun aiki ya barta tana kwance duk tayi fayau da ita.
Tana ganin ya fita ta miƙe zumbur ta ruga wani ɗaki wanda bata shigarshi sai Aiman bai gidan take shiga ta kulle kanta ta barbaza photon Ammar tana kallo tana kuka cikin shauƙi da kewa bata samun natsuwa sai ta fara rairo baitukan waƙa na bege da kewar masoyinta take a kullum kamar yanzu da take raira baitukan cikin zubar hawaye kamar haka ....
_Sai wata rana masoyi na barka_ .
_Ni da kai ayau mun bankwana_ .
_Ammar masoyina ban so mukai rabuwa ba_ .
_Ƙaunarka ta shige raina bazan mantaka ba_
_Ammar rabin raina kazo kai mun ɗauki_.
Ta dage tamkar wata mahaukaciya sai kuka take tana jero baitukan waƙa.
Yana ta kiran wayarta dan zai aiko ta bashi wani file da ya manta ɗakinsa amma bata ɗaga kiran wayarsa ba hakan yasa natsuwa ta gaza fita daga zuciyarsa yaji hankalinsa ya tashi kardai ace ciwonta ne ya tashi yau kuma .
YOU ARE READING
MAMANA CE
Fantasylittafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har s...