MAMANA CE page 44__47

527 32 4
                                    

[12/01, 6:43 PM] Hauwau Salisu: *🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

*MASHA ALLAH*

*Hakika dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai* .

_Allah mun gode maka kwarai da gaske da halin tashin hankalin da muka tsinci kanmu ciki mu kungiyar Kainuwa writer's na na Batan Yarinyar daya daga cikinmu_ .

_Sai dai wannan halin da muka samu kanmu ya bayyana mana masoyanmu sosai da sosai , dan munyi mamakin yanda muka dinga samun sakonnin jaje da Addu'a tako ina daga duniyar marubuta .wanda tasirin Addu'ar yasa muka dace da Yarinyar cikin koshin lafiya_ .

_Muna godiya gareku masoyanmu sosai da sosai 🤝🏻🤝🏻_


Page 44__45

Cikin sauri Ammar ya shirya har ya fito ya dubi kanshi , ya ga bai kamata ya je da shigar kananan kaya ba , yanajin ya kamata ace ya je mata a Yarimansa yanda ta ke mashi kirari a waya tai mashi a fili . Gama wannan tunanin ke nan yai hanzarin komawa ya kira Fadawan yace ayi mashi shirin Sarauta mai kyau cikin sauri .

Mamaki ƙarara a fuskokinsu amma ba damar magana , haka suka tattara natsuwarsu sukai mashi shiri na musamman wanda su kansu basu taba yi mashi wanda ya burgesu ba kamarsa .(to yaushe ma ya ke bukatar kayan sarautar balle suyi mashin ?)

Tun da ya fito Fadawa da Bayin gidan ke kallonsa , cikin sassarfa abun da ya ƙara basu mamaki (ko da yaushe cikin izzarsa da takama yake tafiya )amma gashi yau fuskarsa ba komi ga wata sassarfa yanayi ya nufi Sashen Mai martaba Sarki.

Shima kanshi Sarkin tun a sallamar Yariman ya fahimci akwai sauyi tare da Yarima yau , hakan yasashi dagowa ya dubi Yariman , "Masha Allah ,, itace kalmar da Sarki ya furta a zuciyarsa , tabbas komi ya Kusan zuwa karshe .

Cikin sakin fuska da natsuwa ya zauna ya mika gaisuwarsa kansa kasa ya rasa ta yanda zai sake baiwa mahaifin nasa hakurin abun da ya wuce .
Tsab Sarkin ya fuskancesa yasan miyake nufi sarai,

"Yarima ko dai mun samu Sirika ne ?

Kara sunne kansa ƙasa yayi , "zan dai je gidansu Abokina Dr Aiman ne ,,

Cikin fara'a Sarki yace "Harma ku gaisa da Amrah daga nan ko ?

Shafo keyarsa yayi ga alama baida ta cewa ,

Daga nan gun Fulani ya nufa itama tamkar hadin baki sai da ta tsokanesa kan wannan kwalliya da ya caba sashi gun Amrah .

Dai_dai kofar dakin Jakadiya Hanne yaji sautin muryoyi tamkar ana fada ko gardama , har zai wuce yaji muryan Sarkin Fada na cewa "kin san Allah daga wannan bazan kara zuwa dakin nan ba, haba kin tsufa amma dan jarabar tsiya ko da yaushe sai kice sai nazo na biya maki bukata bayan wahala kawai nakesha ba wani dadi ?

Jakadiya "ka san Allah Sarkin Fada ko dai ka aureni ko kuma kullum kazo nan karage mun zafi inba hakaba Ni zan tona komi wallahi ,,

Cak Ammar ya dakatar da tafiyarsa ya kara natsuwa dan fahimtar in da maganar tasu ta nufa ,

MAMANA CE Where stories live. Discover now