MAMANA CE page 36__39

466 34 0
                                    

[12/01, 6:37 PM] Hauwau Salisu: 🤱🏻🤱🏻🤱🏻 *MAMANA CE* 🤱🏻🤱🏻

                *NAH*

      *HAUWAU SALISU*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________

✍🏻 *Maga_takardan kainuwace*

07081095452

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*Wlh wani Alherin idan anyi makashi yafi gaban kai godiya kai tsaye wlh sai dai kace sauran masoyanka su tayaka mika godiyarka wlh* .

*Hauwau Maman Zee* ( *Name sake*  ) *ina godiya sosai kan dumbin Alhairanki gareni sosai da sosai , Allah yasaka maki da mafificin Alhairi yabaki lafiya wadatacciya tare da Raya maki zuri'a cikin Aminci* 👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

_Jama'a kutayani godiya fa gareta_ ☝🏻

Page 36__37

Kai tsaye shashin Fulani suka tambaya , wata Jakadiya tayi masu I so har kofar falon Fulanin , dai_dai lokacin ne daya daga fadawan Yarima ya kaima Jakadiya sakon Yarima na maganin da zataba Fulanin.
Kallon_kallo sukayi da Amrah tamkar sun gane juna amma sun rasa ta inama suka san junansu ?

Cikin faduwar Gaba Jakadiya ta dubesu kallo guda taima Amrah taji Yarinyar ta bata tsoro , sosai ta ga wani kwarjini da bata taba ganinsa ga waniba a tare da Yarinyar .

Dr Saudat da mamakin yanda Jakadiyar ke ta sunne kai yasata sakin bakinta tana k'are mata kallo, ta dubi da taga fuskarta ta juye zuwa bacin rai kamar wani abu ya faru da su tace "Kanwar Dr miya farune kike cin magani haka tun kafinma muje ga Mamarsu Yariman ?

Cikin Fuskar bakin ciki Amrah tace " Ina ji a jikina Mama tana kewaye da makiyane dan muna sako kai naji warin magungunan Tsubbu na tashi a dakin nan Aunt Saudatu ,,

Cikin 'yar kyarma Jakadiya ta dubeta "Haba Yarinya wacece ke da zaki zo da rana tsaka kiyimana sharri ?

Wani banzan tsaki Amrah ta ja ta afka dakin da take tunanin nan ciki Mamarsu Ammar din ta ke.

Tana zaune kyakykyawar Mace asalin Bafullatana , sai dai kallo guda zakai mata kasan bata cikin hayyacinta , duk tabi ta rame ta fige .

Hawaye suka zuboma Amrah da gudu ta fada jikin Fulani ta saki kuka mai ciwo .
" Garin yaya hakan ya faru da ke Mamarmu ? Ba shakka dukkan alamomin sihiri sun bayyana gareki kamar yanda Abbu yake fadamin zan gani idan akwai sihiri jikin Mutum ,,

"Waye keson ruguza kyakykyawan dangartakanki da Iyalanki Mamarmu ?

I tadai Fulani kallon Yarinyar kawai takeyi bata San abun da akaiba .

Jakadiyace ta shigo tare da wasu tabasu Umarnin fidda Amrah daga dakin da Fuanin ta ke wai bata San ko wacece itaba .

Cikin masifa da bala'i Amrah ta sharama wadda ta fara janyo ta mari fuska ba walwala tace " Nice Amrah matar da Yarima Ammar zai Aura akwai wata shegiyar dake ja danine ?

Idanuwa waje Jakadiya ke kallon Amrah , ( Indai hakane kashinmu ya kusa bushewa da ganin masifaffiyar Yarinyar nan tsab zata bata mata aikinmu dole mutashi tsaye mu raba alakarta da Yarima .) Tunanin Jakadiya kenan tana kallon Amrah idanuwa waje .

MAMANA CE Where stories live. Discover now