MAMANA CE page 53__,55

462 32 0
                                    

*🤱🏻🤱🏻🤱🏻 MAMANA CE 🤱🏻🤱🏻🤱🏻*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

_Ya Allah kai mana gafara ka ƙara mana imani kai mana katangar ƙarfe tsakanin mu da maƙiyanmu 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻_


Page 52__55

Cikin matuƙar ɓacin rai Amrah tai wurgi da wayar ta , cike da fushi ta ce '' Na rantse da wanda ya halicce ni Ammar kayi kaɗan na duƙa ma ka , asali ma kai nake jiran ka kawo kanka gare Ni cikin ƙasƙan da kanka , Ni kuma cike da gadara na kaɗama mari biyu kyawawa san nan zan samu sa i da a cikin zuciyata ''

Hawayen baƙin ciki da tsanar Ammar suka bayyana a fuskar ta .

Walida da Ummi basu yarda da tsanar da Amrah ke ma Ammar ba sai yanzu . Tsabar baƙin ciki fuskarta har wani ja_ja ta ke yi .

Walida tai ƙarfin halin dafa kafaɗar ta "Haba sis ba girman ki bane kina irin haka da Ɗa namiji ba . Idan ba damuwa zan so sanin waye wannan mai kasadar da ya saka wando guda da ke ?

Ajiyar zuciya Amrah ta samu da ƙyal ta yi ,abun da ya sa Ummi miƙa ma ta goron ruwa mai sanyi dan ta jiƙa maƙoshin ta .

Sosai ta sha ruwan , san nan ta zauna fuska cunkushe tace .
"Wani gaye ne da na tsana tun ina ƙarama , sannan nayi alƙawarin daukar fansar laifin da ya aikata ga re Ni duk runtsi duk wuya shine yau dan ya ɗauki karuwa ƴar iska ya Kira Ni wai na je na bashi hakuri ya yafe mun ,,

Su duka suka zuba ma ta ido dan tamkar wata mahaukaciya haka ta juye , dan haka basu samu damar yi ma ta fanfo ba har sukai ban kwana .

Ba ƙaramin daɗi Anbody ta jiba jin dawowar Ammar da  abun da sukai ma juna .

Ta sake lasar takobin haɗa su ko da zasu mace a ranar .


Kowa da kowa ya hallara Sarki kawai ake jira ya fito san nan a ga hukuncin da za'a yanke ma su Sarkin Fada ,ko da yake Jakadiya tsabar laulayi ya sa dole a ka Kaita ta ga Likita wan da acan aka tabbatar da shigar ciki na wata huɗu jikinta ;su kansu Likitoci sun yi mamakin ganin Tsohuwa da ciki har na wata huɗu duk da ba abin mamaki ba ne Halittar Allah .

Jakadiya na zaune fuska cike da tarin nadama da kunya ga cikin ta har ya ɗan fara turo rigar ta . A hankali ta ke share hawayen da suke zubo ma ta .

Tambura da kirarin da ake shi ya ba kowa tabbacin zuwan mai_martaba Fadar .

Ba ƙaramin mamaki  sukai ba da suka ga Yarima Ammar bayan Sarkin .

Basu Sarkin Fada ba hatta sauran Fadawan gun sai da hantar su ta kaɗa , musanman da suka ganshi ran nan ga alama ba daɗi balle rangwame .

Ba su ƙara razana ba sai da suka ga ya je ya hakimce kan karagar mulki ya na mazurai .

Wani ciwon ciki ya turniƙe Jakadiya wanda ba ta taɓa jin irin saba tun da ta ke duniya .

MAMANA CE Where stories live. Discover now