EPISODE SEVEN&EIGHT

349 43 2
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-       
               
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:7&8

 
  Rayuwar ƴanci da jin daɗi suke gudanarwa haka Juda ta fara wayo har ta kai shekaru uku iyayen ta na bata kulawa daidai gatan su basu hana mata komai duk nisa da tsananin abu muddin ta ce tana so haka zasu nemo mata shi,kakan ta sarki kam yana bata wata irin kula da kariya kamar yadda ya ba ɗiyar sa mahaifiyar Juda a shekarun baya da take ƙarƙashin ikon sa..
  Juda na da shekaru uku a duniya Hadara ta kuma samin wani cikin da ya zo ma ahalin da sabon yanayi dan tun da ta sami cikin nan babu daren da zai zo ya wuce ba tare da tayi mummunar mafarki game da abin da ke cikin ta ba abin nan na ɗaga mata hankali tun bata bari a sani har ta kasa riƙema kan ta ta sanar da mijin ta Artemas daga bisani suka sanar da mahaifin Hadara wato sarki.
  Jin haka sai sarki yayi wata doguwar tafiya ya tafi dan nemo masu mafita wanda yayi dace dan an ba shi sihiri mai ƙarfi da zai kare abin da ke cikin Hadara duk da dai abin ba wai mai ɗorewa bane amma yin hakan shi ya fiye masu alkhairi dan kuskure guda ɗaya aka samu toh cikin nan na iya ɓarewa,..
  Shan magungunar sihire sihiren tayi sannan ta bi ƙa'idojin da aka ce ta rinƙa  bi toh da haka dai ta sami sauƙi sai dai fah tun sun iya ɓoyewa har watarana aka kawo masu farmaƙi da hari ɓakatatan daga masarautar Ottoman ƙarƙashin odar sarkin masarautar Ottoman wato Baal-Hamon dan ya daɗe yana biɗar wannan abin mamaki ya daɗe yana bibiyar rayuwar masu ɗauke da juna biyu dake ƙasar sa kaf amma sam bai sami abin da yake biɗar ba sai kawai watarana ya saka mallamin sihirin sa Aberald (The great Wizard)dake zaune nan cikin masarautar tun zamanin kakanni da kakannin sarkin dake kan mulki yanzu da haka,shi ya haɗa siddabarun sa ya bankaɗo ƙasar Babylon inda a nan aka san cewa abin da sarki Baal-Hamon ya daɗe yana yunwar samu yana nan a ƙasar kuma babu nisa dan haka ana iya samin abin ko ta halin yaya,toh ranar da aka kawowa ahalin Artemas wannan hari suna kan hanyar su ta zuwa kasuwancin su cikin babbar kasuwar ƙauyen kawai sai suka ga mutani fuskokin su rufe da baƙaƙen ƙyalle ko kafin su yi wata yunƙurin har sun riƙo hannun Hadara kafin Artemas yayi wani abin sun ɓace ɓat da ita aka neme ta aka rasa...
  A ranar cikin baƙin ciki suka ƙarasa ranar dan ko ta ko'ina an bincika ba'a same ta kaf ƙauyen nan babu Hadara babu labarin ta wannan abin ya ɗaga hankalin mahaifin ta sarki da ɗiyar ta Juda wacce take faman tambayar inda aka kai mata mamar ta ita a dawo mata da mamar ta,haka dai ta rinƙa ƙiriniya tana kuka har bacci ya ɗauke ta sai mahaifin ta ya saɓa ta a kafaɗa ya kama hanyar dajin da zai sada sa da hanyar kasuwar da aka ɗauke Hadara a nan ne ya shimfiɗa Juda a tsakar kasuwar ya rinƙa bin ta da wasu irin ruwa masu sanyi ƙalau haka ya zagaye ta tas sau huɗu yana yayyafa mata ruwan nan kuma bata farka ba sai ma jan numfashin da ta yi ta cigaba da baccin ta,ko da ya gama zagaye ta sai ya ja gefe ya tsaya kimanin sakanni sai wani irin hadarin hayaƙi ya fara tashi daga jikin ta hakan ya saka sa miƙewa tsaye da kyau yana mai ware idanun sa dan son ganin eh abin da mahaifiyar sa ta bar mai yana hawa kan hanya...
  A haka har hayaƙin ya ɗauke wurin ya washe kamar babu abin da ya faru a wurin sai ya cicciɓe ta ya tsaya tsaye ya rinƙa wasu waƙe waƙe(incantations)babu jimawa sai ya ga an ingizo Hadara daga inda babu tsammani sai ya janyo ta ya rungume ta yana kiran sunan ta,a rikice take sanar da shi abin da ta gani wanda hakan ya ɗaga mai hankali har suka dawo gida sannan ya sanar da sarki abin da ya faru wanda wannan shine dalilin sarki na kuma zuwa can kudu maso yamma ya kuma karɓo wasu siddabarun dan ya rantse maƙiyan sa ba zasu ga bayan sa ba dan dama tun shekarun baya akwai babbar al'amari tsakanin masarautar Ottoman da ta Babylon kuma a ganin sarki,ana so a yi amfani da cikin Hadara ne a rama duk wata ƙurar da ya ɗan lafa bayan ya tashi a shekarun bayan nan....

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now