EPISODE FIFTHY ONE&FIFTHY TWO

195 20 0
                                    


EPISODE:51&52

SOME DAYS AFTER
Tun bayan barin sarauniya Zinaida masarautar Ottoman babu wani kwanciyar hankali tattare da Sultan dan ya rasa ta ina zai faro abubuwan dan kuwa ƙarya ya sharara ma sarakan nan saboda ba ainihin abin da ya faru ba kenan,ainihin abin da ya faru daban ne da wannan labarin da ya koro ma mutanin nan kawai kare kan sa yayi daga rage ƙimar sa da martabar sa a idanun sa..
A kullum,sai ya tafi sashen ɗiyar sa ya ƙare mata kallo,kallon da shi kaɗai ya san manufar sa dan tunda yake tare da ita bai taɓa jin irin wannan strange feelings ɗin ba da a kullum in ya tuno sai ya ji kamar ana tsaga ƙirjin sa..
Ko a yanzu ma sashen nata ya nufa yayi tsaye yana kallon ta daga window yadda hadimai ke hidima da ita wurin gyara mata sumar kan ta da goge mata jiki da haɗin kayan gyaran jiki dan haka take duk dare sai an ƙyalƙyale mata jiki kafin ta kwanta..
Hango sa tayi daga inda take zaune sai tayi saurin tashi tana mai sallamar hadiman akan su tafi zata neme su in ta gama magana da mahaifin ta..
Takowa ta yi har ta iso gare sa tana mai yi mai murmushi da ya saka sa ƙara jin ta a jikin sa,shima matso ta yayi suka zo daf da daf sai ya rage tsawon sa ya sunkuyo yana mai ɗora mata sumba a gefen kuncin ta alamar yabawa kyawun ta..
Murmushi kawai ta iya mai,dan ta lura a ƴan kwanakin nan sam bata ganewa mahaifin nata daga ya tsare ta da ido,sai ya tasa ta gaba im tana bacci ya rinƙa kallon ta yana murmushi har ta buɗe idanun ta su yi ido huɗu da juna..
Buɗe mata hannuwar sa yayi ta ƙaraso ta faɗa jikin sa tana mai sakar mai murmushi haɗe da fiddo abin dake ran ta
"Baba na wai me ke damin ka ne a ƴan kwanakin nan duk ka canza kamar ba kai ba a kullum sai dai ka tasa ni gaba kana kallo na ko in ina bacci ka zuba min ido kana kallo na kana murmushi,shin me ke damin ka ne wai Baba na ko dai zuwan wannan baƙon ne mai suna Irad ya sa ka kasa natsuwa ka aiwatar da ayyukan ka na masarautar ka"?ta mai tambayar tana mai kai duban ta gare sa ta kafe sa da ido dan itama same abin da ya faɗi ma su sarakan nan shi ya faɗi mata dan sam baya son ɓacin ran ta bai son abin da zai takura ta kuma baya so tayi abu ba cikin hayyacin ta ba shi yasa ma ya mata ƙaryar..

Girgiza mata kai yayi yana murmushin dai sai ya amsa mata da
"Princess,i don't know what got into me but i have this strange,unusual feelings that something,,something forbidden will be happening any moment soon,i get scared and i feel insecure i also want to secure you my princess did you understand me"?gyaɗa mai kai tayi tana murmushi..
"Baba na,amma wannan yaron,,mai suna Irad,ni fah tsoron sa nake ji,sai ka ga ya zo min da sassafe wai in tashi in yi ibada,toh me hakan ke nufi"!!
Hankalin Sultan ne ya tashi dan yana gudun kar yayi asara ba tare da ya sami nasara ba dan in har asirin sa ya tonu na bayyanuwar gaskiyar abin da ya faru tsakanin Irad da shi kafin ya aminta ya taho masarautar toh kuwa zai kwashi abin kunya shi kuma ba haka yake so ba..
"Princess,kika ce yakan ce da ke ki tashi kiyi ibada"?nodding mai kai tayi sai ya ɗan share zufar da ya faso mai a goshin sa ya dube ta ya ce
"Toh me kike masa in ya ce da ke hakan"?ɗan yamutsa fuska tayi kamar ta ga abin ƙi ta ce
"Ce masa nake ba zan yi ba kuma ina ruwan sa da ni"a ɗan razane ya dube ta yana cire ta daga jikin sa ya ce
"No princess,no,,ba haka zaki na ce mai ba,next time in ya ce da ke haka nan sai ki ce da shi toh zaki yi in ya so bayan tafiyar sa sai kiyi banza da maganar nasa okey"?ɗan shiru tayi har sai da ya kuma maimaita abin da ya ce da ita sannan ta ɗaga mai kai tana faɗin
"Na ji Baba na zan yi hakan"ɗan murmushi yayi kafin daga busani ya raka ta ta koma ɗakin ta shi kuma ya nufi sashen sa yana mai tunane tunane kala kala har dai ya kwanta da cikin sa yana ajiyar zuciya sai ya ji an fara shafa mai jiki..
Baya buƙatar sanin ko waye dan ya san Dacey ce sai ya daɗa kwanciya yana mai cigaba da sauke ajiyar zuciya..
Cigaba da shafa mai bayan aka yi sai ya tsinci kan sa da yin wata magana da ta zamo sirrin sa
"Dacey na rasa natsuwa ta ban san ya zan tunkari al'uma in nuna masu shirka nake yi ba,ban san ya zan yarda in karɓi defeat ɗin nan ba,na ɗauka ina iya yin komai ba tare da taimakon kowa ba aahe ba haka bane,i turned the world revolving around me and this is the time that the eclipse rises and turned towards the sky,then the sky shines it hot and sarcastic heat on me,am scared,i don't wanna loss my child i don't wanna loss princess"!!!.ɗif sai ya ji an daina shafa sa an tashi tsaye,abin da yayi sanadiyar Juyowar sa kenan..
Tozali idanun sa suka yi da wata daban daga wacce yake tsammani,a firgice ya tashi yana gyara rigar sa yana faɗin
"What are you doing in my casino?whatt"??da ihu ya ida maganar wanda sai da ya saka Calva matsawa da baya tana faɗin
"My king,forgive me but i swear i never came here with this intention all i wanted was to surprise you with this,,this massage and nothing else"!..
Wani irin tsawa ya daka mata yana mai ce da ita
"Ni na saka ki?ni na ce ki shigo min sashe na har cikin makwanci na?ni na ce maki ina buƙatar tausar ki Calva?yaushe na fara haka da ke?sannan me kika ji"?jiki na ɓari ta amsa mai da
"Babu abin da na ji sarki na babu na rantse da mulkin ka"!!wani irin kallon banza ya aika mata da shi sannan ya nuna mata hanyar fita..
Ƙafa na ɓari ta bar sashen nasa ta nufi nata sashen leaving him all alone standing like an idol cike da mamakin Calva,lallai dole ya san na yi da Calva in ba haka ba toh sirrin sa zai gama fallasuwa...
Fita yayi ya iso babbar falonsa na karɓar baƙi ya zauna yana huci rai a ɓace ya aika aka kirawo mai masu kula da shigi ficin sashen sa..
In less than four minutes suka jeru a gaban sa suna mai kirari..
Kuma aikawa yayi ya ce a kirawo mai mai kular mai da kayan yaƙin sa dan yau hukunci mai tsauri zai yi..
Jin haka sai da gaban su ya faɗi sai dai suka waske suna danne fargabar su dan kar laifin nasu ya ƙaru(laifin da basu san ko menene ba)..
Nan ma ba'a jima ba aka taho mai da wani irin jibgegen wuƙa,wuƙar da yake amfani da ita duk shekara in za'a tafi gasar yaƙin sarakai,har wa yau babu wanda ya san sirrin dake cikin wuƙar nan sai shi abin sa dan sau da dama in har ya kai ma mutum hari da shi,toh fah sai dai wani ba wannan ba,ya bar numfashi kenan..
Cikin tsoro da firgici suka hau Kallon junan su suna haɗiyar yawu dan basu san laifin su ba sai dai sun san a yau sun yi bankwana da duniyar..
Tashi tsaye yayi yana mai gyara riƙon wuƙar nasa a lokaci ɗaya yana jujjuya wuƙar,dan bai cika ɓata lokaci wurin yanke hukunci ba,take yake aiwatarwa..
Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya yana kallon reaction ɗin su na tsoro tsantsa sai yayi wata muguwar murmushi sannan ya soƙi na farin da wuƙar,..
Faɗi ƙasa wanwas yayi yana zubar da jini,haka ya rinƙa bin su ɗaya bayan ɗaya yana soƙin su da wuƙar nan har sai da ya ƙarar da su a na ƙarshen ne ya ɗan ja lokaci dan ya sanar da shi laifin su sai ya fara ba Sultan haƙuri amma ina shima ya soƙa mai wuƙar, dukkan su kwance suke a ƙasa matattu,sai sannan ya aika aka kirawo masa Calva..

Jin kiran nasa me ya saka ta jin faɗuwar gaba amma haka ta tashi ta biyo ɗan aiken dan kar ta aikata wani laifin..
Ko da suka iso ɗakin saukar baƙin Sultan,sai da Calva ta ji faɗuwar gaba amma ta ɗan kama kan ta ta matso Sultan tana mai yin ƙasa da kan ta haɗe da faɗin
"Ga ni na zo gaban ka Sultan,me kake buƙata daga gare ni"!!?ɗibar ta yayi ya zubar sannan ya ce
"Darasi da ishara na kirawo ki ki gani kuma na tabbatar ya zuwa yanzu kin san ma'anar wannan isharar da nayi"?sarai ta gane inda ya dosa dan haka ta jijjiga kai tana mai ce da shi
"Idan na fallasa ko siffar murmushin ka ne Sultan,ka raba min kai na da jiki na"..
Kallon ta yayi sannan ya bata damar tafiya sai dai fah a ran sa ya san duk kusancin sa da Calva dole alaƙar su ta yanke dan ta gano wani sirri nasa wanda bai kamata ta gano ba..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now