EPISODE TWENTY THREE&TWENTY FOUR

226 29 1
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-       
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:23&24

A firgice sarauniya Zinaida ta koma ta ƙofar ɗakin haɗe da hankaɗa shi tana mai fidda numfashi mai nuna tsantsar ɓacin ran ta haɗe da fusatar ta,..
Tana shiga ta nufi kan gadon haɗe riƙo hannun gimbiya Ondrea ta janyo ta ta sauko daga saman gadon sannan ta bi wannan saurayi da ƙazantaccen kallo tana mai tofar da yawu kafin ta fuskanci gimbiya Ondrea cikin ɓacin rai ta shiga yi mata magana
  "Kin haukace ne Ondrea??ina tambayar ki ki bani amsa baki da lafiya ne?ki rasa da wa zaki haɗa jiki sai da wannan bawan?tukunna ma yaushe kika yi girman haɗa jiki da ɗa namiji?cikin masarauta na kike wannan abin?asiri ya maki ne?iyee?ki amsa min"?cikin ɗagin murya ta mata tambayar ƙarshen tana mai yi kamar zakanya dan saura kaɗan ta ɗauke ta da mari..
  Hawaye ne ke bin fuskar gimbiya Ondrea tana mai yin tir da halin mahaifiyar ta a ce uwa na haɗa shimfiɗa da wasu mazajen da bata san asalin su ba sannan ita dan ta yi hakan da wanda kowa ya san sa ya san tarihin sa shine zata tada hankalin ta akai in ba dai manufar ta take son isarwa akan sa ba me zai sa hankalin ta ya tashi sannan ta razana haka..
  Tana tunanin ne yayin da shi kuma wannan saurayin ya nemi wandon sa ya suturta jikin sa yana mai yunƙurin saka rigar sa ta leda mai gauraye da fata,ai kuwa fauce rigar sarauniya Zinaida tayi ta ɗaga hannun ta ta yanke mai maruka har biyu tsabar takaici da baƙin ciki,..
  Gimbiya Ondrea bata san lokacin da tayi tsalle ta faɗa jikin saurayin nan ba ta fashe da kuka tana mai yi wa mahaifiyar ta wasu irin maganganu masu razanarwa.
  "Na rantse maki in kika kuma ɗaga hannun ki akan masoyi na zan manta cewa ke kika haife ni in yanke hukuncin da ya zo min rai na sannan in baki sani ba yau ki sani ni da Cahal mun zama ɗaya a yau ɗin nan ɗazu ɗazun nan ba da jimawa ba saboda haka ki cire idanun ki daga gare mu in ba haka ba zan ɓace maki ɓacewa ta har abada"!..da kuka ta ida maganar wanda ya birkita sarauniya Zinaida ta kasa haɗa kan ta wu ɗaya dan haka ta kalli saurayin da gimbiya Ondrea ta kira da Cahal tana mai wani irin mugun kallo mai ɗauke da harara
  "Ka yarda ka san ɗiya ta?ka yarda ka haɗa jiki da ita?toh bara na sanar da kai ka tafka babbar kuskure a rayuwar ka wanda ya janyo maka yin rayuwa gidan horo rayuwa ta har abada"!!sai ta juya ga ɗiyar ta tana kallon ta sannan ta ce
  "Ke kuma mu zuba ni da ke cikin masarautar nan tunda kin kwaɗaitawa kan ki abin da ya fi ƙarfin ki"tana kaiwa nan ta fita fuuu tana tafe kamar tayi fiffike ta miƙe sama ta tsinci kan ta a ɗakin ta,..
A yayin tafiyar ta mutani sama da takwas sun amshi maruka daga gare ta sannan mutani biyar sun sami hukuncin shekaru biyar gidan horon ta..
  Tana shiga ɗakin ta bata tsaya ko ina ba sai cikin ɗakin ta mai tsananin duhun gaske,tana shiga ta hankaɗa labulen wani gefen ɗakin ta shige ciki sai gata tsaye gaban wani irin kyakyawar gunki da aka ajiye shi kamar an zana da hannu,tana zuwa ta faɗi gaban gunkin nan ta hau faɗe faɗe tana iface iface kafim ta dawo ta faɗi ƙasa warwas ta shiga shesheƙa tana tambayar gunkin kamar haka
"Kai ka ce min duk abin da nake buƙata kuma na gan sa a gaba na in yi yadda nake so da shi,me ya sa yau na buƙaci haɗa shimfiɗa da wannan bawa amma ɗiya ta ta min shigar sauri bayan ta sanar da ni tana son sa na hana ta yin wata alaƙa da shi sai ta yi mai gabaɗaya ta haɗa jiki da shi sannan bata ji shakka ta ba?me ya sa hakan ya kasance?me hakan ke nufi"?wani guguwa ne ya taso ya lulluɓe ta kafin murya ya biyo baya cikin isa aka fara yi bata amsar tambayoyin ta
  "Dalilin faruwar hakan shine kundin da kike buƙata na nan zuwar maki dan a halin yanzu kundin na nan ƙasar ki kuma nan ba da jimawa ba zai shigo masarautar ki amma kar ki manta na sanar da ke muddin kika riƙe wannan kundi a hannun ki,,kaf asirin da kika ma ahalin masarautar ki ciki har da ɗiyar ki zai warware sai kin ɗora wata sabuwa ta yadda zaki mulki duniyar baki ɗayan ta saboda ki sani kina iya fuskantar abubuwan al'ajabi iri daban daban wannan kaɗan ne daga irin abubuwan al'ajabi da ban mamaki da zaki fuskanta kafin kundin nan ya shigo hannun ki,dan haka ki sani baki da ikon haɗa shimfiɗa da wannan saurayi dan ƴar ki ta gama amincewa da shi a zuciyar ta saboda ta mallaka mai jikin ta da tunanin ta kuma matuƙar kika tsananta akan sai ta rabu da shi toh zaki rasa ta rasawa ta har abada,ki tuna rasa gimbiya Ondrea na daidai da rasa komai naki a duniyar nan,rasa ta na daidai da rugujewar gwamnatin ki ko da kin mallaki kundin nan dan haka ki yi azamar gyara tunanin ta kafin ta ƙubce maki"!!!ana gama faɗin haka guguwar ya ɗauke sai ta miƙe wuf ta fito ta koma kan gadon ta tayi kwanciyar ta tana mai baƙin cikin hana ta kusantar wannan saurayi da ta gama ƙudirin kasancewa da shi a ɓangare ɗaya kuma tana murna da farinciki kundin da zai shigo hannun ta kenan mayaƙiya Berenice bata mutu ba ta tsaya tsayin daka dan ta kawo mata kundin nan saboda ta sakar mata ɗan uwa,lallai akwai shaƙuwa ta musamman tsakanin Berenice da ɗan uwan ta...

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now