EPISODE ELEVEN&TWELVE

258 33 1
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:11&12

  Wata kyakyawar budurwa ce wacce ba zata yi ƙasa da shekaru ashirin da iku zuwa da huɗu ba kusan dai tsarar Juda sai dai kyawun wannam ƴar budurwar na daban ne dan har wani walwal take yi tsabar kyau da hasken ta ga wani irin naɗi da ke kan ta kamar sarauniya a masarautar farauta sai dai fuskar ta tamau take babu alamar wasa a tattare da ita wanda ya sa in ba kallon tsain ka mata ba baka gane cewa kyawun ta na iya ruɗar da maza..

Miƙar da hannun ta tayi da nufin tashi zaune sakamakon ganin irin kallon da Juda ke bin ta da shi wanda ya saka ta a duhu ta kasa tantance kallon tsoro Juda ke bin ta da shi ko kuma kallon farautar ta take yi.,
  Tana yunƙurawa zata tashi ta ji an kuma mai da ta ƙasa da matuƙar ƙarfi,jiyo nishi tayi gab da hancin ta wanda ya tsorata ta sai ta buɗe baki cikin masifa ta fara faɗa
  "Wannan wani irin rayuwa ne,ina zaman zama na ki shigo min rayuwa kina nemar yi min lahani akan me"?wani irin mugun kallo Juda ta bi ta da shi.
Lallai wannan ƴar rainin wayo ce da tunani,ta biyo ta har tantin ta tana nemar sace mata gadon ta sannan yanzu ta buɗi baki tana faɗin ita ce ta shigo mata rayuwa,ah lallai da alama wannan yarinyar bata san wacece ita ba sai ta gwada mata..
  Babu wani magana da ta bari ya shiga tsakanin ta da wannan budurwar,zaro takobin ta tayi wanda lokacin da ta tashi ta ɗan mayar gefen rigar ta,daidai saitin cikin ta ta kawo takobin da alamar daɓa mata shi take son yi..
  Ai kusmwa wannan budurwar na gani haka ta yi wani kukan kura ta hankaɗa Juda ta miƙe tsaye tare da zaro nata makamin mai ji kamar ƙahon dabba sai kaifi da haske,ta daidai wun ƙahon ta murza wani abu nan da nan ƙahon ya canza ya dawo takobi mai matsakaicin tsawo dan ya fi wuƙa tsayi sosai,kayan jikin ta ya dawo kamar jikin dodon koɗi(snail shell)zanen siffar dodon koɗin duk ya mamaye jikin ta sai ta nunawa Juda takobin tana haki tana kallon ƙwayar idanun Judan bakin ta na marmarin furta wata kalma amma ta kasa sakamakon fargabar da take ji..

  Ita kuwa Juda kallon iko take ta yi wa wannan budurwar ganin siddabarun(Magic)da tayi a gaban idon ta babu tsoro bare shakkar kar ta mata wani illah,kenan wannan ba da mugun nufi ta biyo ta ba dole wata dalili ko manufa tata ne ta kawo ta nan ɗin..
  Yin wannan tunani ya sa Juda maida takobin ta ma'adanar sa ta fuskanci budurwar ta ƙura mata ido tana ƙare mata kallo har sai da budurwar ta tsargu da kallon da Judan ke bin ta da shi
  "Why are you giving me that silent look"??cewar budurwar sai Juda ta girgiza mata kai tana mai cigaba da kallon ta kafin daga bisani ta buɗi baki ta ce
"Who send you here and why are you following me"?ɗan murmushin gefen baki tayi kafin ta bata amsa da
  "Am not out for your search"sai ta ɗan girgiza kai kafin ta cigaba"am out for a different purpose so i guess you are bluffing"!!!..murmushi ne ya kuɓcewa Juda dan budurwar ta bata dariya sai dai ita kuma dariya ba abin yin ta bane a gaban maƙiyin ta sai dai ta murmusa dan haka ta murmusan ta ƙure ta da ido sannan ta ce
  "Na ga alamar tsoro da fargaba da ɗawainiya da ke dan sam baki da wani ƙwarin gwiwa a yayin da kije magana da ni har kike musayar yawu da ni,,faɗa min,shin...daga ina kuma wacece ke dan na ga kamar you are lost"!!!banzan kallon budurwar ta ma Juda tana mata ƙasƙantacciyar duba mai kama da zanar guga kawai furtawar ce bata yi ba...
  Abin mamaki ita Juda dake  nemar masalaha da budurwar sai ga budurwar na nemar ɗaukar wata hanyar ta daban dan kuwa tsakanin ta kan gaskiya da gaskiya ta saka takobin ta saman wuyar Juda da nufin yaƙar ta..
  Da fari abin ya ɗan firgita Juda kafin daga bisani ta ce da budurwar
"Kar ki sake jini na ya fito ya sauka kan takobin nan naki in ba haka ba har mutuwar ki cikin jini zaki cigaba da kasancewa ban nufe ki da wata manufa ba dan haka tun kafin in rasa haƙuri na akan ki kiyi gaggawar rabar jiki na da takobin ki"!!!cikin hargagiya da hargowa budurwar ta ce
  "You are bluffing lady,,..sam ba zan cire ba sai kin sanar da ni me ke cikin wannan littafin da kike ɓoyewa,,yi sauri ki sanar da ni abin da ke ciki n shi"!!!...
  Shiru Juda tayi tana kallon ta ita ba tsoro budurwar ta bata ba mamakin ta take yi ganin irin rashin ta idon da take da shi ne ke ɗaure mata kai a ce wai da zafin ta da fushin ta ta sassautawa wannan budurwar amma ita kuma abin da zata saka mata da shi kenan..
  A zuciye Juda ta ingiza ta kafin wani abin ta nufo ta da takobin ta ta fara ƙoƙarin yaƙar ta ai kuwa faɗa ta kacame a tsakanin su yi suke yi kamar dama can da manufar faɗar suka zo dajin..
Abin yayi tsamari ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba faɗa sosai suka yi su da takubban su basu tsagaita ba sai da ɗaya ta kayar da takobin ɗaya sannan suka tsagaita inda cikin haki Juda ta fara magana
"Na nufe ki da lallami kar ki bari in ƙara tunzira in hukunta ki fiye da haka ina jin tausayin ki in ba dan haka ba da sai na kar ki...wacece ke sannan wa ya aiko ki gare ni"??kamar ƙiftawar ido wannan budurwar ta ture Juda daga saman ta ta cigaba da faɗa da ita suka sake komawa filin faɗar a karo na biyu wanda a wannan karon ba ƙaramin dambatuwa suka yi dan dukkan su sun ji a jikin su babu ciwo ko yanka ko ɗaya a jikin su amma kam jikin su ya amsa,share lokaci suka yi suna dambaruwa..
  Dan kan su suka dakata haɗe da wurgar da takubban su a gefen su suka tsaya kallon kallo ita dai Juda so take ta san wa ya aiko wannan budurwar dan bata gamsu da cewa nan ne ƙurewar ta ba,dan sun gwada yaƙi su biyu har suka kusa isa magajiyar juna hakan bai wani gamsar da ita ba haka bai birge ta ba...
  Ido cikin ido budurwar ke kallon Juda ganin tunda ta fito yawon farautar ta bata taɓa haɗuwa da mace ɗaya mai jin kan ta kamar doki sannan tana dambe kamar maza babu alamar gajiya tattare da ita ba kamar wannan budurwar dan haka take ganin me zai hana ta saukar da kai ta mata ladabin ƙarya dan ta ƙaru da ita dan ta lura zata matuƙar amfanar da ita dan cinma manufar ta in lokaci yayi. 
  Yanke wannan hukuncin tayi bayan ta gama shawartawa da zuciyar ta haɗe da yin na'am da wannan shawara tata..
  Idanun ta na cikin na Juda ta canza murya daga na ƴan farauta ta sassauta shi ta salamta shi zuwa na mutani masu galihu ta fara rero kalamai da zuciyar ta ta shimfiɗa mata kamar haka.
  "Na san kina da tambayoyi kala kala a zuciyar ki game da ni,wacece ni me kuma ya haɗa ni da ke da har nake kalle miki littafin da kika ɓoye cikin jakar ki,,.toh ni dai abu na fari da nake so da ke shine ki bani hankalin ki ki kuma yi ƙoƙarin fahimta ta in ya so bayan na gama baki labari na sai kiyi abin da kika ga ya dace zaɓi zai rage naki ba nawa ba"..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now