EPISODE FIVE&SIX

353 47 1
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-       
               
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
Am proud of u and always will,the eyeliner of the media and online writers{Brilliant Writers Association pen of freedom,home of exceptional and magnificent writers]the media is ours.
EPISODE:5&6
LIFE HISTORY OF JUDA AND BABYLON EMPIRE IN BRIEF

Baadi Artemas shine cikakken sunan mahaifin Juda wanda ya kasance ɗa ga Artegal Ted shahararren ɗan kasuwa kuma babban mai siya da siyarwa kama daga ƙasar sa har zuwa ƙasashen ƙetare wanda wannan sana'a tasa ta janyo mai zama babban mai kula da harkokin shigi da ficin ƙasashen,wannan ɗaukaka na kakan Juda wato Artegal Ted ya janyo mai maƙiya marasa adadi dan kuwa ba sau ɗaya ba sau da dama manyan masu kuɗin ƙasar da garin na soj a basu wannan muƙami amma aka hana su sai suka ji labarin an ba wannan bawan da bai tako su a dukiya ba,karar tsana suka ɗorawa wannan mutumi abu kamar wasa sai gashi sun fito fili ƙarara sun nuna mai manufar su akan ko ya janye ya ce baya son muƙamin kokuma su aikasa inda ba'a dawowa dan su so suke su cigaba da harkar ha'incin su a ƙasar amma shi baya yarda da hanyar da suke kawo masa toh hakan ya sa suka haɗa gungu akan su zo su tsawatar mai in ya ƙi ji sai su ɗau mataki.
  Da suka tunkare sa da wannan zance ya nuna bai san da wannan zance tasu ba ai ko babu jimawa bayan sun bar gidan sa cikin dare suka aiko da sojojin su(Assassins)suka zo gidan Artegal Ted suka yanke sa har mutuwa sannan suka fara nemar sauran ahalin sa amma basu sami kowa ba dan dama tun bayan barin mutanin nan ya nemi shawarar matar sa dan ya san ruwa ba zata yi tsami banza ba doke suna da wata ɓoyayyiyar manufa akan sa tunda har suka bar gidan sa ba tare da sun nuna mai komai ba,,,shawara ya nema daga gare ta akan mafita a da so tayi su gudu tare amma ya ce a'a in har suka gudu tare toh ba zasu taɓa barin su su huta ba zasu cigaba da bibiyar su har sai sun same sa sun ƙarar da su dan haka ya canza shawara ya ce ita da ƴaƴan su uku wato Baadi Artemas(Artemas)kamar yadda suke kiran sa a sauƙaƙe mai kimanin shekaru goma sha biyar 15years)sai ƙannen sa biyu mata Yahaira da Daliyah Yahaira ƴar kimanin shekaru goma(10years) sai Daliyah ƴar kimanin shekaru bakwai(7years)su bar ƙasar baki ɗaya dan gudun kar a kawo masu farmaƙi a riske su su duka ko ba komai zai so a ce ƴaƴan sa sun ɗaukar mai fansar abin da za'a mashi da wannan shawarar Kiara matar Artegal Ted ta haɗa kawunan ƴaƴan ta suka bar gidan tana kuka ƴaƴan na kuka suna kallon mahaifin su..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now