AUTHOR'S NOTE

655 74 2
                                    

AUTHOR'S NOTE{SHARHIN MARUBUCIYA}

  MashaAllah we are on the rigid line lol..am sure da yawan ku zasu rinƙa tunanin menene cikin wannan littafi?what is so special about it?why is it named BAMBANCIN ƘASA{Battle to reach}?well it's all over,the whole thoughts and imaginations are all over...

Mutani da yawa zasu fara wondering "oh Siyama daga ina kuma ta ƙaƙalo wannan suna?ya zata rubuta labarin sa?zai ma yi daɗi kuwa?toh muna dai biye da ita sai mun ga abin da ya turewa buzu naɗi",,hahh funny..

Toh Allah ya kawo ni na dawo maku da abin birgewa,actually na san many thoughts na ta running maku a brain ɗin ku dangane da wannan littafin,toh abin dai shi ne..

  Wannan littafi cikin kaso ɗari(100%) kaso hamsin(50%)true events ne da suka faru suka shuɗe shekaru da dama,kaso hamsin(50%)sune suka zama fiction wato ƙirƙirrare wanda dole in saka hakan dan gyara littafin da kuma ƙara mai garɗi sakamakon BAMBANCIN ƘASA da BAMBANCIN  al'adu da suka bambanta a jinsi daban daban especially jinsin waɗanda labarin ya faru a al'adar su...

Wannan labarin ku tuna,na ce da ku kaso hamsin(50%)true event ne sannan na ce da ku ya faru a shekaru da dama da suka shuɗe sannan na kuma cewa na canza wasu abunuwa sakamakon BAMBANCIN ƘASA da BAMBANCIN al'adu wanda in kuka lura da kyau,zaku san cewa kusan gabaɗaya littafin research work ne wato bincike mai zurfi wanda wannan dalilin ne ma ya sa ban fara rubuta shi da wuri ba sai da aka ɗau lokaci...
  Toh idan har zaku fahimta da kyau zaku fahimci labarin ba a iya nan ƙasar Nigeria ya ɗora akalar sa ba a'a hasalima a ƙasar Nigeria zai sauke akalar sa amma tun daga farawar sa har zuwa inda zai sauke akalar sa wato a nan Nigeria,gabaɗaya zagaye ne a ƙasashen da abubuwan suka faru..

Sakamaon tsarin littafin da ya kasance zai zo da yaren Hausa,zan yi iya ƙoƙari na dan in ga na yi translating nasa ya zo maku ta yadda zaku fahimta amma fah ku gane,kamar dai yadda na sanar da ku true event ne kuma ba a nan ƙasar tamu abin ya faru ba kawai,ya zaga zuwa ƙasashe wanda hakan ke nufin ba a hausance aka yi sa ba dole sai da wani yaren wanda ya haɗa da turanci {English},dan haka zan ƙoƙarta in kawo sa da Hausa amma dole akwai wuraren da ba zan iya tempering na su ba dole a yadda ya zo hakan zan kawo shi dan haka expect it in a mix way {EnglishHausa}da fatan kun fahimce ni..

Babu tabbas labarin zai zo maku a tsarin da litattafai na suka saba zuwar maku domin kuwa wannan true event ne hatta da mutani,sunaye,garurruka,al'adu,da kuma ɗabi'ar su ta BAMBANTA da sauran da kuka saba ji da gani a litattafai na...

  Duk waɗannan bayanai da na tsaya yi maku da sharhunan ba dan komai na yi su ba sai dan gudun kar sai mun tsunduma tsundum cikin labari a zo ana tambayar ina kuma wannan labarin ya dosa anya wannan labarin exist?well it does exist wanda shi ya sa ma na yanke shawarar kawo maku shi duk dan mu ƙaru mu san abin da ya faru a shekarun baya ba tare da mun zauna da ilimin mu na nan inda muka sani kawai ba...

Again wannan labarin ba ƙage bane (50%)gaske ne dan haka ku ƙarbe sa a yadda ya zo ba ni na ƙirƙiro sa ba haka ya faru kuma zan ji daɗi in kuka cigaba da bin labarin daki daki har kammalauwar sa...

AUTHOR'S NOTE{SHARHIN MARUBUCIYA}

IS SIYAIBRAHIM

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now