EPISODE FIFTHY NINE&SIXTY

172 27 1
                                    

EPISODE:59&60

Babylon

  "Yura,ni kam kin san wani abu kuwa"?tambayar da Hadara mahaifiyar Juda ta ma aminiyar ta kenan..
  Kallon ta Yura tayi tana mai maida hankalin ta gabaɗaya ga Hadara sai ta cigaba da
  "Ina jin wani iri,kamar dai Juda bata cikin kwanciyar hankali,sai nake ganin kamar nayi son kai da yawa,a ce ɗiya ta ɗaya ƙwal,in bar ta ta tafi wata uwa duniya alhalin ban da tabbacin shin wacce ta tafi nemowar na raye ko a'a,ban ma Juda adalci ba Yura,ina son bin bayan ta"!!
  Kallon ta Yura tayi a yayin da ta ida maganar tana mai zubda hawaye dan ta matuƙar yin nadamar rabuwa da ɗiyar ta da tayi duk saboda wani dalili dan daga baya tazauna tayi nazari dan kan ta ta ga rashin dacewar abin da ta yi..
  Dafa kafaɗar ta Yura tayi tana bata magana mai sanyi haɗe da bata hope akan any moment soon Juda will be back kuma da positive result zata dawo masu..
  Sosai Hadara tayi zaman kaɗaici da zurfin tunani a wannan satin,sharewar shekara kenan babu ɗiyar ta babu labari sannan ga mugayen hannaye da ke burin ganij Juda ta zo gare su,abin dai ita ya zame mata gaba kura baya sayaki..
  Duk wasu hanyoyin bauta,Hadara na ƙoƙarin bi dan ta ga ta sami kwanciyar hankali dan ta san in har tayi addu'a toh zai isa wun ɗiyar ta,a kwanakin ta dage da zuwa wurin bauta tana addu'a akan yarinyar ta ta kasance cikin kariya da faɗawa hannu na gari..
  Damuwa sosai ke addabar ta,ba kullum take samin ikon fita kasuwa wun siya da siyarwar da take yi,lokuta da dama takan gwammaci zama a gidan ta rinƙa yiwa ɗiyar ta addu'ar nasara da kariya dan ta gane cewa,revenge,never pays instead,it ignites the calm situation into violence..

  Ko a yau ɗin nan shiryawa tayi cikin shigar mutunci daidai al'adar su ta can ta nufi wun shiga keken doki dan ya kai ta inda zata tafi bauta,sakamakon mummunar mafarkin da ta rinƙa yi a kwanakin bayan nan,bata gamsu da su ba hankalin ta kaf ya koma ga lafiyar ɗiyar ta tilo ɗaya..
  A ranar sai da Hadara ta kusan kwana tana addu'a akan ya isa ga ɗiyar ta tare da nemar mata kariya daga dukkan abin ƙi..

Ottoman Empire
  A yau ne aka rinƙa shirye shiryen tarbon baƙin ƙasar Oman dan haka tun safe aka rinƙa gyare gyare da sauye sauye dan baƙuntar ta yau,daban ne ya bambanta da na sauran ranakun kuma ana so a burge baƙon da zai iso masarautar a yau ɗin..
  Yayin da bayi da kuku ke faman safa da marwa dan ganin komai ya tsaru ya bada ma'ana da kyau,gimbiya Acenath na can ana mata gyaran jiki,irin gyaran da ba'a taɓa yi mata irin sa ba,gyara sosai,kama daga suman kan ta har zuwa ƙafafun ta sai da aka sillice ko ina tas komai ya fito tsaf tsaf,dan yau ɗin rana ce ta daban a rayuwar ta,hatta da masifar da take yi yau bata yi sa ba dan bata son fuskar ta ya nuna alamar ɓacin rai bare zuciyar ta ya ɓaci,a yau ɗin ma duk wanda ya nemi ɓata mata rai toh da gimbiya Adriel take barin sa dan ta yi alƙawari bata barin komai ya ɓata mata rai a yau ɗin..

  Mahaifiyar ta ma ba laifi ta kimtsa ko ina tsaf tsaf a sashen ta dan yau ɗin a shirye take da ta nunawa duniya ma gimbiya Acenath ɗiyar ta ce kuma ita ɗin ce dai matar gida ba mistress ɗin Sultan ba(Dacey)da a ko da yaushe in ma ziyara aka kawowa masarautar nasu toh fah Dacey ce akan gaba tsabar ta sami sake daga wun Sultan dan har nunawa take daga ita babu wata ita kaɗai ce matar sa kuma a hakan yake amsawa yana yaba ta dan ganin ta yake kamar numfashin sa yayin da matar sa kuma ke rungumar baƙin ciki..
  Toh a yau kam ta ma kan ta alƙawarin ba Dacey ba,ko shi kan sa Sultan ɗin zai nuna mata _Bambanci toh fah ba zata yarda ba dole yau ta ƙwace ragamar ta da damar ta a matsayin ta na mahaifiyar gimbiya Acenath kuma wacce zata aurar da ɗiyar ta ga yariman wata masarautar..

  Bayan wasu awanni

  Duk kowa yayi positioning kan sa yana tsaye a inda ya dace,gimbiya Acenath na daga ɗaƙin ta tana hange ta window,ta sha ado da kwalliya wasu jajayen kaya da ya ainihin fito da kyawun ta da hasken ta dan komai na jikin ta ja ne kuma mai ɗaukar ido,a hakan ma wai dan ta hana kar a mata mummunar adon da zai dusashe kyawun ta a idon mijin nata da zata aura kenan,..
  Muryar niece ɗin ta ta jiyo tana tsokanar ta
  "Can't wait to see the handsome husband to be,aren't you ashamed"!!!?juyowa gimbiya Acenath tayi da fara'a a fuskar ta ta amsa ma ƴaruwar tata
  "Adriel,am eager to see him,na zaƙu in ga irin halittar da yake da shi,na matsu in ga fuskar sa ko kyawun sa ya ɗare nawa kyawun,Adriel am shameless,yes i am shameless"da murmushi ta ida maganar wanda ya saka gimbiya Adriel murmusawa itama dan ita kan ta ba laifi akwai kyau kuma gashi yau ɗin ta cancaɗa ado daidai misali bai wani yi yawa ba dan dama bata cikin jerin ƴan mata masu son yawan kwaliyya da ado..
  Rungume gimbiya Acenath tayi tana zuzuta kwaliyyar ta da adon ta
  "Babu wani namiji da zai ga kyautar da kike da shi a tattare da ke ya juyar da fuskar sa gefe,dole sai ya yaba kuma ya bada tukwuci,dan haka ki kwantar da hankalin ki kamar kin hau gadon mulkin Ottoman kin zamo Sultanate na  masarautar Ottoman ƴaruwa ta,princes Ziyan Aman is all yours sister"!!farinciki ne ya lulluɓe gimbiya Acenath ganin tun bata haɗa ido da yariman nata ba har ƴaruwar ta ta bata ƙarfin gwiwar zata mallake sa..
  "Shi yasa nake son ki ƴaruwa ta kin maye min gurbin mahaifiya ta ta ko wani ɓarayi dan ita,bata da lokaci na she is always engaged in one thing or another her time is too precious to her to be shared with me,her only daughter"!!nan da nan yanayin ta ya canza sakamakon tuno rashin lokacin da mahaifiyar ta ke bata dan a kulluyaumi in har zata nemi spending lokaci da mahaifiyar ta toh  fah sai ta bata excuse kwata kwata babu wani sabo mai tsanani a tsakanin su..
  Ganin yadda farat ɗaya ta canza zata yi kuka sakamakon tuno rashin cikakkiyar rayuwar da ta samu daga wun mahaifiyar ta kamar dai yadda duk sauran ƴaƴa ke samu daga wun mahaifiyar su,sai kawai gimbiya Adriel ta shashantar da abin tana mai maida shi wasa da raha sai kawo mata abubuwan ban dariya ta rinƙa yi har dai ta sake jikin ta suka shiga hirar yarima Ziyan..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now