EPISODE TWENTY NINE&THIRTEY

190 23 3
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
BAMBANCIN ƘASA
{Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:29&30

A fusace gimbiya Ondrea ta ɗaga murya tana faɗin
"Kamar ya babu wanda zai bar nan me kike nufi"?ci kan ki Juda bata ce da ita ba ta mata banza tayi tafiyar ta.
Rai a ɓace ta juyo ta kalli Cahal tana aika mai da kallon ɓacin rai dan in ba saboda dalili ba Juda bata kai matsayin yi mata yadda ran ta ke so ba dan bata fi ƙarfin zamowa mai kula da ruwan wankar ta ba amma ji yadda take mata abu kai tsaye isa isa babu ladabi..
"Cahal,ni zan tafi,in ka so kayi ta zama kana taka rawar gangar ta amma ni kam,ka ga tafiya ta"tana gama faɗar hakan ta hau gyara mayafin ta da take lulluɓe fuskar ta da shi.
Ganin haka ya sa Cahal ya fuskanci eh lallai da gaske ran ta ya ɓaci kuma bai kamata ta kama hanya ita kaɗai ba amma ayar tambayar a nan shine,idan ta fita daga ayarin su Juda ya zata tsira da rayuwar ta,idan sarauniya Zinaida ta aiko a biyo bayan su fah ya zata yi?wannan tunanin ya saka sa fasa yarda su bar wun su juda dan haka shima cikin maida murya irin ta manya ya ce
"Masoyiya ta ki yi haƙuri har gari ya waye in ba haka ba za'a sami matsala in kika fita ke kaɗai sarauniya na iya aikowa a biyo mu dan ni da ke mun san cewa sarauniya akwai wayo da fasaha,yana iya kasancewa yanzu ma ta rigada ta aika a biyo mu dan haka kawai ki haƙura har zuwa wayewar gari in ya so sai mu bar nan kin ji"?ya faɗi yana mai maida hankalin sa gabaɗaya gare ta dan ta yarda da shi..

Kallon sa tayi tana mamakin ba dai tsaface sa Juda tayi ba dan in ba haka ba ya za'a ce mutum da hankalin sa da idanun sa biyu masu aiki da amfani ya ga abu ƙarara haka sannan ya ce ba zai gudu ya tsira da kan sa ba..
Girgiza kai ta shiga yi tana kallon sa cikin ƙwayar ido ta ce
"Cahal ni zan tafi amma ba zan tilasta maka ba,ka sani,in har ka zaɓi zama da waɗannan mutanin toh ni ba zan hana ka ba amma ba zan cigaba da zama da ƴar daba ba"juyawa tayi zata wuce ya riƙo hannun ta ya dawo da ita,ko kafin ta mai magana har ya rufe bakin maganar da nasa bakin maganar..
A tankaɗe Agneta ta kalle su dan tun ɗazu take kallon wasar kwaikwayon da suke yi saboda ita bata ɗau hakan a matsayin kulawar da ɗa namiji ke ba ɗiya mace ba sakamakon tasowa da tayi gidan mata tsantsar halayya da koyarwar ta akan rayuwar yaƙi irin ta mata ya ta'allaƙa bata san wani abu wai so ba haka bata fatan yin gamdakatar da shi dan tun yarintar ta a nan gidan sarkin Oman ta taso haka tun tana ƴar ficikar ta aka fidda mata da zuciya akan so irin son ɗa namiji da ɗiya mace ta hanyar Exorcism..
Wannan dalili ya sa Agneta ta zamo wata irin mace da bata san komai a rayuwa ba bayan cikar burin ta da na mai gidan ta sarkin ta wato sarkin Oman,bayan wannan,so,shirme ne a gare ta..
Wato an cire mata abu mafi muhimmanci a rayuwar ta abun da ko wace mace ke alfahari da shi wanda wannan abin shi ke kai masoya izuwa matakin aure,gabaɗaya aka yaye mata ɗison so a zuciyar ta aka dasa tsanar sa tsana ƙarara ta yadda ko gani tayi ana yi sai ta ji kamar ta kashe masu yin sa,a lokuta da dama takan zauna tayi tunanin anya lafiyar ƙalau,dan takan ɗan ji abin ya bijiro mata sai dai namiji na taɓa ta hannun sa ya daina amfanar sa dan sai ta tabbatar ta yanke hannun nan sai daga baya in ta natsu sai ta ga kamar abin da take yi akwai ayar tambaya cikin ta but sakamakon mugun ritualistic act da aka yi a jikin ta ya sa ko da tayi tunanin baya wani tasiri sai ya kau ya fita a kan ta..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now