EPISODE SIXTY FIVE&SIXTY SIX

153 19 0
                                    

EPISODE:65&66

Ihu gimbiya Acenath ta fasa a lokacin da ta ga mahaifin ta cikin wani irin hali dan bata san yadda aka yi ta tsinci kan ta gaban mahaifin nata ba tana faman faɗe faɗe haɗe da tsala ihu a duk ƙarshen maganar da zata yi dan kuwa idan da wanda ta fi shaƙuwa da shi a masarautar nan kaf toh mahaifin ta ne kuma bata son wani abu ya taɓa sa dan shine kaɗai ya damu da ita,daga shi sai ƴaruwar ta gimbiya Adriel that is in tana nan in bata nan kuwa haka take rungumar haƙuri tayi ta rarrashin kan ta in abu ya same ta..
Sarauniya Bayarma ce ta fashe da kuka ganin amintaccen Sultan kan sa ya ha'ince sa ya guje sa yana taya wasu waɗanda bai sani ba,toh a hakan ma wai an mai rangwame kenan dan ana ganin sauran mutuncin sa ba a mai yadda ake ma masu laifi ba...
Calva kuwa tashi tayi tana kalle kalle tana takawa har gaban su Irad wanda ke jiran Sultan Baal-Hamon ya farfaɗo da kyau dan ya amsa masu tambayar su,har su kan su media press members ɗin bin su da kallo suke yi dan kuwa yanzu suke tantance maganar nan ta wata miyar sai a maƙota..
Daidai gaban Irad Calva ta tsaya ta kalle sa tana mai yin ƙasa da murya,ko me ta ce da shi sai kawai cikin fushi Irad ya ɗago ya kalle ta,ita kan ta sai da ta firgita..
Cikin ɗacin rai ya rinƙa magana kaar zai ari baki sannan ya ɗora da
"A yau ba sai gobe ba Calva,a yau nake so kiyi revealing ma masarautar nan ainihin ko ke ɗin wacece kuma bana son ɓoye ɓoye dan ba zai min wuya ba in hukunta ki"!!ya ida maganar yana mai nuno mata takobin hannun sa da ya firgita ta sai ta kalli Sultan dake ƙoƙarin tashi ya zauna yana kallon ƙasa sakamakon jirin da yake ji da yanayin da kan sa ke juya masa..
Bai jira ta tayi maganar ba shi ya yi cikin tsawa da gadara..
"Sultan Baal-Hamon ina jaririya aka ce,kar fah ka tsaya yin gardama da mu dan ka ji na maka rantsuwa,sai ka yi daka sanin yin gardama da ni,ina jaririyar take"?
Cikin haki Sultan Baal-Hamon ya buɗi baki yana magana cikin kaƙarewar murya ya ce
"Irad...Ira...aaaddd...Iradddd...ni ne fah...ni fah Sultan Baal-Hamon wanda ya kawo ka nan,,ka tuna"..cikin fushi Irad ya ce
"Kai Sultan kar ka raina mana hankali,me ruwar mu da wani dalilin ka,ko kai ka kawo ni sai me?tambaya aka maka kana nemar ka raina mana hankali sai me dan kai ka kawo ni?albishirin ka Sultan Baal-Hamon,ni Irad Al-Riaz ban zo masarautar ka ba sai da na shirya,kafin in zo masarautar nan dan haka ka ga kenan nayi bincike mai tsauri akan masarautar nan kafin in taho,ban amshi gayyatar ka kai tsaye ba sai da na nemi hanyoyi kuma na taho da nufi na haɗe da ƙudiri na kuma nayi nasarar samin abin da nake so a cikin masarautar nan kuma yanzu ni da sauran al'uma zamu yi determining abin da ya dace da kai,an so a maka cikin mutunci da mutuntaka amma ka ƙi,toh za a fito maka a yadda ka saba a yadda ka gane"!
Calva ce ta buɗi baki cikin rawar jiki tana faɗin
"Sultan ka yi wa kan ka rai ka faɗi abin da zai ceto ka daga kaidin mutani,ka ma ahalin ka mutunci ka faɗi amsar tambayoyin da aka maka ka ji"!?kallon Calva Sultan yayi yana jinjina lamarin dan shi dai bai san ta ya zai fara amsa waɗannan tambayoyi..
Kukan sarauniya Bayarma ne ya farkar da Sultan daga dogon tunaninnda ya faɗa..
"Sultan ka ba su amsa mana baka san mun damu da kai bane,so kake ɗiyar ka ta rasa mahaifin ta ta dalilin son duniyar sa?Sultan ka mana rai ka faɗi inda jaririyar nan take na roƙe ka"!!kallon ta Sultan yayi yana jujjuya kai yana mai jin zafi a ran sa dan bai san ta yaya zai fara tsage gaskiyar abin da ya shimfiɗa marar kyau ba..
Rai ɓace Balik ya miƙe ya matso gaban su Irad ya fizge takobin dake hannun Callee ya nuna sa daidai cikin Sultan yana faɗin
"Ko ka bada amsa,ko kuma ran ka Sultan dan ba zama sauraron ka muka zo yi a nan ba ka gane ai"?cikin firgici da tsoro ya ɗago duk da ya so yayi taurin kai amma haka yana ji yana gani ba zai bari yayi asarar rayuwar sa ba dole ya faɗi gaskiya dan sarai ya gane description da Callee tayi akan Juda..

Cikin rawar baki Sultan Baal-Hamon ya fara magana yana kallon jama'ar fadan cikin jin ƙasƙanci da takaici
"Na san na yi laifi amma bana jin na shirya bayyana inda wannan jaririyar take ku min rai amma ba zan iya ba"!!kanewa mutanin wurin suka yi ganin taurin kai irin na Sultan da kafiya..
Tsananin ɓacin rai haka Juda ta daka tsalle ta faɗo gaban Sultan tana haki tana faɗin
"Na rantse da wanda nake bautawa Sultan Baal-Hamon kake da suna ko wa,na daɗe ina farautar ka amma Allah bai ti zan far maka ba tun asali sai da na kuma yin karatu akan al'amarin duniya sannan Allah ya haɗa ni da kai,a dalilin ka na baro gida na na baro mahaifa ta na baro mahaifiya ta da ban san a wani hali take ba a yanzu na bar komai nawa na shiga yawo da garari a dajunan da bab san su ba ban taɓa shigar su ba na bi ruwa na bi rana na bi iska na haɗu da abubuwan al'ajabi fiye da misali duk akan ka,duk saboda kai duk dan in yi ido huɗu da kai in ƙwace ƙanwa ta da ka raba ta da mu tun tana jinjiran ta,yanzu an zo ana maka lallami har kana gayawa mutani kai baka shirya bayyana inda wannan jaririyar take ba?shin wani irin azzalumi ne kai?wani irin mugu ne kai?yaushe zaka gane cewa ƙetar ka ta kawo matsaya inda ba zata cigaba da hayayyafa ba kamar da?yaushe zaka san mugunta kan cinye mai shi ne?har sai yaushe zaka farka daga mummunar baccin da ka daɗe kana yi ba tare da ka juya ba bare ka farka ka san reality da nightmare defers?ka sani,ba zan bar masarautar nan ba sai da ƙanwa ta kuma babu wanda zai bar masarautar nan sai ya karɓi addini cikin biyu da ake gudanar da shi a faɗin duniyar nan wanda ra'ayin mutum ne ya zaɓi addinin da yake so dan na rantse ba zan baemr ka ka cigaba da shan iska a duniyar nan ba sai na ƙwaci ƴanci na,taimakon ka ɗaya,na daina kisa amma a baya na daɗe ina maka tanadin kisar nan kai kan ka ka san darajar aiki na ba sai an labarta maka ba kuma a yanzu hankali ne na yi ya sa na cire ra'ayi fighting justice kai tsaye,dan haka tun muna maka kallon mutunci Sultan Baal-Hamon,ka fiddo min da ƙanwa ta in ba haka ba"!!!...
Sosai kalaman Juda suka tsorata Sultan Baal-Hamon har ya ji kamar ba shi bane dan haka ya zaɓi faɗin gaskiya dan ko ma dai me zai faru ya san abin zai zo mai da sauƙi..
Kuka sosai gimbiya Acenath ke yi tana jin zafi da rashin daɗi a ran ta akan irin cin fuskar da ake ma mahaifin ta..
Idanun sa sun kaɗa sun canza launi ya kalli su Irad ya juya ya kalli su Cahal sannan ya kalli matar sa kan sa a ƙasa ya ɗaga yatsar hannun sa yayi pointing a direction ɗin da gimbiya Acenath take cikin karyewar murya ya ce
"Ga....ga..ga ta...nannnn..."ras gaban gimbiya Acenath ya bayar yayin da hawayen fuskar sarauniya Bayarma ya ƙafe ƙaf kamar ba ita ke kukan ba,kaf fadar aka yi shiru ana kallon abin al'ajabi da mamaki a wun Sultan Baal-Hamon wasu ko cewa suke ƙarya yake yi gaskiya ce bai son faɗi shi ya sa yake nuna ɗiyar sa..
Yarima Ziyan ne ya miƙe tsaye yana mai ce da ƴan jaridun da ya taho tare da su cigaba da kwasar rahoto da tabbatar da accuracy na komai..
Zuwa yayi gaban Irad ya dafa kafaɗar sa yana ɗan girgiza sa haɗe da ɗan juyo sa kaɗan suka haɗa ido sai yarima Ziyan ya ce da shi
"Aikin ka yayi kyau aboki na kuma na ji daɗi da ka tsaftace shi ba a sami matsala ba,sai dai duk da hakan,na lura kamar sai an haɗa da na ƙarfi a ɗazu amma yanzu kamar ba sai an gwada ƙarfi ba,sauran bayanai duk na san yana wun ka"!kallon sanayya suka wa juna kafin daga bisani Irad ya kalli sarauniya Bayarma dake zaune a daskare kamar an dasa ta tana kallon Sultan Baal-Hamon da ya gama bata mamaki ya ɗaure mata kai ganin da gaske fah Sultan iya gaskiyar sa yayi maganar dan Sultan ba kasafai yake ƙarya ba kenan ina wannan magana nasa ya nufa??
Tambayar dake ta kai kawo mata a rai kenan dan haka cikin ɓarin jiki ta tashi ta shiga takawa har gaban sa ta tsaya tana kallon sa yayin da shi kuma ya kasa kallon nata ya mayar da kan sa ƙasa,hakan ya tabbatar mata da cewa eh Sultan maganar da yayi gaske ne ba ƙarya ba..
Zaman diris tayi tana kuka mai cin rai,ga dai gimbiya Acenath nan zaune kamar an dasa ta komai ma kasa yi ta yi,ana haka ne Calva ta ta yi wani magana da ya janyo hankulan mutanin dake wurin dan da iya gaskiyar ta ta dage ta furta shi..
"Tabbas wannan ita ce ɗiyar da Sultan ya sa aka sata a lokacin da take jaririya ya raine ta har kawo yanzu,duk da na san kuna mamaki da zargin abubuwa daban daban na rashin yarda rmda tunanin ta yaya hakan ya faru,toh iya gaskiyar maganar kenan wannan"ta faɗi tana mai nuna gimbiya Acenath dake zaune kamar an dasa ta ta sake ido da baki tana kallon mamaki
"Ita ce jaririyar da Sultan Baal-Hamon ya sa aka sato aka kawo ta masarautar nan tun tana jinjiran ta har kawo yau"!!a nan tayi shiru..
Tuni mutani suka dawo da hankalin su gare ta ga dai Sultan nan zaune kai a ƙasa kamar marar lafiyar ƙwaƙwalwa..
Kallon wani ɗan saurayi tayi ta ce da shi
"Ina take"?nan take saurayin ya juya ya fit,jim kaɗan sai ga shi ya dawo da wata budurwa kan ta a ƙasa tana tafiyar a hankali kamar tana tsoron tafiyar,haka dai a hankali ta tako har inda su Sultan suke ta ja ta tsaya kan ta a ƙasa..
Magana Calva ta fara yi cikin rashin tsoro bare shakka..
"Wannan,ita ce ainihin gimbiyar wannan masarautar mai albarka a da,ita ce gimbiya wacce ya kamata a ce ta ɗanɗani jin daɗin wannan masarautar amma sakamakon halayyar mahaifin ta,sai ta taso cikin ƙunci da baƙin ciki"!!
Tun da ta fara wannan jawabin Sultan ya rinƙa kallon ta abin kamar a mafarki kamar ana ba shi labari haka ya rinƙa ganin abin..
Wai me ke faruwa ne haka shi bai fahimci komai ba kwata kwata,ta ya za'a kawo wannan yarinyar a ce shi ya haife ta..
Sarauniya Bayarma kuwa kallon Calva tayi cikin fargaba da tsoro ta ce
"Calva,,me kike faɗa ne haka ban fahimta,me wannan maganar taki ke nufi Calva"??
Nannauyar ajiyar zuciya Calva ta saki kafin ta fara narrating tushen labarin kamar haka..
"Suna na Calva Belington,ni ce ɗiya ta uku a cikin ahali ne,mu huɗu ne uku maza ni kaɗai mace,mahaifi na da mahaifiya ta sun zamo jajirtattun ƴan kasuwa masu siya da sayarwa kaf faɗin ƙasar mu,a lokacin da yayye na suka yi aure ina ƴar yarinya dan haka duk a gidan mu suka zauna da matayen su,ko da na kai yin aure haka aka saka biki na,aka rinƙa shirye shirye"
"Ana tsaka da shagalin biki na ni da ango na,sai muka ga abin mamaki,aka watse mana taro aka mana fata fata aka kashe mutani da dama aka rasa rayuka da yawa,a ƙarshe da abin ya lafa,sai na ga ashe wai ni kaɗai ce mai ran ciki duk sauran ahali na sun rasu babu mutum ko ɗaya da ya rayu cikin su duk sun mutu,ranar da ya kamata ya zamo rana mafi muhimmanci a rayuwa ta sai ya zamo rana mafi muni a gare ni,ko bayan wasu lokuta sai na gano daga inda aka turo mutanin da suka kashe min family,na gano daga masarautar nan aka turo su kuma Sultan Baal-Hamon ne ya aiko su,a kan wani dalili nasa na wai ya taɓa samin matsala da sarkin yankin akan wani sa'insa da suka samu sai ya aika akan a wargaza yankin mu kuma ko wa aka samu a illata sa shine ƙaddarar ta sauko mana"
"Tun daga wannan lokaci ni kuma nayi alƙawarin ganin bayan Sultan Baal-Hamon sai dai na rasa ta hanyar da zan shigo rayuwar sa kuma in saka mai yarda da ni a zuciyar sa,kwatsam ana haka sai ya kuma aikawa a zo a kwashi mata a wannan yanki nawa,jin wannan labari sai na bi hanyar da ake taruwa ana kwashe matan,sa'a ta ɗaya da aka zo kwashewa sai na faɗa cikin su aka kwashe mu zuwa wannan masarautar"
"Toh tun da na tsinci kai na a wannan masarautar nayi wa kaina alƙawarin sai na ga bayan Sultan Baal-Hamon,a haka nake cikin bursinar nan kullum cikin tunani mai zurfi da nemar mafita,kwatsam sai aka taho wani yaƙi aka kusa fasa bursinar dan a tozarta Sultan,ban san ya aka yi ba tunanin da nayi ya faɗo min ba,ni dai na san na ga wani ya nufo Sultan Baal-Hamon da nufin kai mai yanka a gefen hannun sa,ganin haka sai nayi amfani da damar na tare sai yankar ta same ni a madaɗin ta sami Sultan"
"Tun daga lokacin ne yarda ta fara shiga tsakani na da Sultan,toh bayan wasu lokuta sai matar Sultan sarauniya Bayarma ta fara laulayin ciki,abu na farko da ya zo kai na shine,in matsa kusa da ita tunda Sultan ya raba ni da wannan bursinar a cewar sa na taimake sa da ya rasa ran sa,tun lokacin da Sultan ya ga ina kular mai da matar sa sai ya saki jiki da ni ba tare da ya san cewa ni ɗin ina da nawa manufar akan sa ba"
"Ana haka ne har cikin ta ya tsufa ta kai watar haihuwa wanda a daidai lokacin ne Sultan ya sa aka tafi har ƙasar Babylon dan a nemo masa kundin da yake so dan ya fara mallakar wasu sirrikan a kan koyarwar mai masa duba wato Aberald"
"Bayan an tafi yaƙin aka dawo babu nasara sai aka sanar da shi an gano wani ɓoyayyen sirri a wurin da aka tafi yin ɓarnar,sai Sultan ya sa aka koma aka binciko mai wannan ɓoyayyen sirrin wanda a daidai wannan lokaci kuma,matar sa sarauniya Bayarma na tsaka da wahalar naƙuda wanda sai da ta share sama da sati tana yin sa,duk hankalin Sultan ya gama tashi akan naƙudar ya kasa tsaye ya kasa zaune duk dan yana gudun rasa gudan jinin sa dan shi kam,ba ta kan sarauniya Bayarma yake ba ta kan magajin sa yake"
"Ranar da ta cika rana ta bakwai sarauniya Bayarma na naƙuda a wannan rana ce aka dawowa Sultan Baal-Hamon da ɓoyayyen sirrin nan wanda ya kasa gane ta ina zai warware wannan sirrin,dan haka ya sa aka ajiye mai sirrin a sashen sa ya nufi sashen sarauniya Bayarma da ke naƙuda kamar zata mutu,duk wasu kalamai masu daɗi da sanyaya rai sai da Sultan ya mata dan rabon sa da Dacey farkar sa sati ɗaya kenan sakamakon naƙudar da matar sa ke yi"
"A daidai wannan gaɓa ni kuma nayi wata tunani akan me zai hana in fanshe baƙin ciki na akan wannan magaji na Sultan dan haka sai na barwa kai na na cigaba da duba da lura da sarauniya Bayarma a yayin da take cikin azabar naƙudar"
"Bayan kamar wasu mintoci har Sultan ya bar ɗakin sai na ɗauko wani haɗin da nayi sa musamman dan sumar da jariri ko jaririyar da za a haifa,na dawo ɗakin na zauna ina ta yi ma sarauniya Bayarma tausa har dai lokacin da haihuwar ta zo mata,bata wani jima da haihuwa ba ta sume,toh dama haka jaririyar ta zo babu wani isasshen numfashi a tattare da ita dan haka bata yi kuka ba,ganin haka ni kuma kawai nayi amfani da damar nan na buɗe mata baki na tsiyaya mata wannan haɗin maganin haka jaririyar nan ta koma ta kwanta tana ta baccin wahala ga rashin lafiya dake addabar ta amma saboda ni in farantawa kai na sai na yi kamar abin bai dame ni ba"
"Ihu da kuka na na ya fargar da Sultan Baal-Hamon dake waje yana kai kawo,da saurin sa ya shigo ɗakin sarauniya Bayarma ya shiga tambaya na lafiya,sai na ce da shi ai abin da sarauniya Bayarma ta haifa ne ya koma,kasancewar duk cikin masu yi mata hidima tun da ta fara naƙudar nan an dakatar da su dan kar su cutar da ita sai ni kaɗai ke shigi da fici a sashen nata"
"Shiru Sultan yayi a tsaye yayin da ni kuma na ke kukan munafurci da kirsa,can kuma sai na ga Sultan ya fita,jim kaɗan sai ya dawo ya ce da ni ɗau jinjirar mu fito tare,hakan na yi sai muka nufi sashen sa inda ya ce da ni in ɗau jinjirar in kai ta in binne ta a kusa da maƙabartun kakannin ta kuma in bar maganar daga ni sai shi"
"Amsa mai na yi sai na fita na nufi inda ya aike ni ɗin sai dai fah ba binne jinjirar na yi ba binne banza kawai nayi na ɗau jinjirar na bi dare da ita na saci jiki na kai ta fannin da ake ajiye jarirai in an sato su,ban bar wurin ba sai da na tabbatar jinjiran ta farka sannan na saci jiki na bar wurin na dawo cikin gida"
"Abin mamaki shine,wai bayan na dawo sai na ga sarauniya Bayarma ta farka,hannun ta riƙe da jaririya tana ta murmushi,gefe ɗaya Sultan ne yake ta zuzuta kyawun jinjirar,sai abin ya ɗaure min kai amma na dai yi shiru na rinƙa farincikin ƙarya da yaƙe dan kar a gano ni,"
"Da Sultan zai fita ne ya kirawo ni ya sanar da ni komai sannan ya ɗora da cewa jaririyar zata zamo masa kariya a rayuwar sa ta yadda duk wani wanda zai yi galaba akan sa toh fah ba zai yi nasara ba sai dai ya rasa ran sa,muddin jinjirar ta rayu,ko da ya sanar da ni wannan labari sai nayi shiru ina kasaƙe amma na barwa zuciya ta abin yi da wannan shawara da tunani na Sultan"
"A haka Sultan ya kai jinjirar nan wun mai masa duba wato Aberald dan ya wanke ta tas da sihiri sannan ya raɗa mata sunar da babu wanda aka taɓa raɗawa a tarihin masarautar,nan dai aka raɗawa jaririyar Acenath a inda tun daga lokacin ake kiran ta da gimbiya Acenath kuma sunan ya bi ta"
"Shekaru da yawa ya shuɗe,nakan tafi in kaiwa ɗiyar Sultan ziyara a ɗakin bursinar nan,sosai yarinyar ta saba da ni a kullum in nayi tunanin hallaka ta sai in fasa dan so nake Sultan ya gani da idanun sa bayan ya gano ainihin ɗiyar sa na da rai sai in raba sa da ita,duk rayuwar da tayi ban taɓa yarda an mata fyaɗe ba dan ba shi ne ƙudiri na ba saboda ko ni babu wanda ya min a lokacin da ya turo a watsa yankin mu"
"Da haka rayuwa ta cigaba annamimanci na na yau daban nna gobe daban har aka gama yarda da ni a masarautar nan baki ɗaya,sirrin dake tsakani na da Sultan kuwa yana nan a ɓoye,yau da gobe bai bar komai ba,matsaloli ya ishi Sultan har dai ya kawo wannan mayaƙin wato Irad daga ƙasar Iran dan ya magance mai shi dai nashi matsalar,ya mulki duniya,toh da munafurci na na janyo ra'ayin Irad har ya biye min na rinƙa warware mai komai har dai shima ya sanar da ni cewa ga dalilin sa na karɓar gayyatar Sultan kuma ya ce da ni shi ɗin sahihin amimi ne ga ɗan sarkin Oman wato yarima Ziyan Aman"
"Shi ya sanar da ni yadda zan yi komai kuma ya sanar da ni cewa a yau wannan abin zai faru kuma kar in ɓoye komai in faɗi duk abin da za a yi a yi sa dan yau sai am ga bayan Sultan Baal-Hamon sannan ya ce da ni da hannu na zan raba kan Sultan da jikin sa,toh dama abin da nake muradi kenan kuma na samu,dan haka na ce zuwar Irad masarautar nan haske ne a gare ni kuma baƙin duhu ne ga Sultan sai dai bai sani ba"..

A yayin da ta dire wannan labari nata sarauniya Bayarma ta daɗe da sandarewa a zaune suma masu zaman fadar duk sun yi shiru,Sultan na zaune kamar sakarai babu magana,gimbiya Acenath na kallon bakin Calva kamar tana kallon wani abin al'ajabin da bata taɓa gani ba,ayarin su Berenice da su Cahal kam abin ba'a cewa komai sai shiru,Juda kam tun ɗazu take tuno irin abubuwan da suka faru a shekarun baya da wannan yaƙi ya kaure,dama ƙanwar ta suka taɓa yunƙurin sacewa a shekarar da ta gabata dama,amma saboda ƙarfin jini da nufin Allah sai hakan bai faru ba..
Kuka ne ya so cin ƙarfin ta amma ta danne tana ta son controlling kan ta amma ta kasa haka kawai ta fizge takobin hannun Irad ta kaiwa Sultan wani wawan soƙi a inda ta san ba lallai bane ya daɗe a raye in yayi wuta mintuna ashirin....

SIYAIBRAHIM

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now