EPISODE THIRTY ONE&THIRTY TWO

215 26 0
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-     
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:31&32

"Kin cuce ni kin min zamba cikin aminci you made me to believe you,you used me you fooled me"haka ta rinƙa nanatawa cikin fusata da ɓacin rai mai nuna tsantsar baƙin ciki da ɓacin rai..
  A tare Berenice da Balik suka yi pulling nata back suna mai janye ta daga yunƙurin komawa kan Juda da ta rinƙa yi yayin da Juda ke ƙoƙarin tashi tsaye su kuma Berenice na tanƙwara ta..
  Tana gama miƙewa tsaye ta kalle ta ta kuma kallon ta ta ga yadda aka rirriƙe hannun ta sai kawai ta ɗauke ta da mari wanda yayi sanadiyar warwarewar sumar ta ya zubo a gefen fuskar ta da ta juya,kan ta a gefe ta ɗago ta zubawa Juda ido,ita kuma bata tsaya bata wata dama ba ta kuma ɗauke ta da wata marin ta gefen hagu tana faɗin
  "Ki dawo hayyacin ki Agneta,i never fooled you,you fooled yourself,just look at you,so beautiful and gentile,look i slapped you twice for you to come bacl to your senses and know your worth..you are fae beyond all these.matsayin me?muƙamin me?me zasu maki?ina zasu kai ki?you just wannan get the book and go away just because of the so called tittle and powers that was vowed to be given onto you?me zasu ƙare ki da shi?baki da buri ne?ko baki da mafarkin rayuwar da ta fi ta dajin da kika taso kika rayu cikin ta ne?don't you know?Berenice here,she told me,she told me that there is a good and sweet life out of this close place,baki so ki shiga wannan duniyar?baki so ki san me ke wajen wannan duniyar da muke rayuwa cikin ta?ko so kike ki ce da ni baki da masaniya akan ɗan sarki kuma magajin sarkin da kike kashe kan ki akan sa na nan a wancan duniyar?baki da masaniya?"
  Runtse idanu Juda tayi cikin takaici da baƙin ciki sannan ta buɗe idanun waɗanda suka koma ja jazir saboda ƙunci da takaicin da take ji a zuciyar ta,cigaba tayi da magana da murya mai nuna tsantsar haushi da daƙiƙancin Agneta..
  "Baki da wayo ne ko baki da hankali ne?faɗa min?shi yana can yana ɗora ɗan sa akan hanyar da ta dace yana inganta mai rayuwar sa sannan har sarkin da ya hana a gudanar da irin wannan ilimin na da masaniya akan duniyar da yake kuma ya lamunta da hakan dan ɗiyar sa ɗiyar zinarin sa na son sa,ke fah?an baki damar yin wani abu da zai kawo maki cigaba a rayuwar ki?sarkin da ya alƙawarta maki wannan kyautar kina da tabbacin eh zai baki muƙamin?kin tabbatar ba kashe ki zai yi ba bayan kin kai mai abin da yake buƙata?dan haka ki gane wani Bambanci i never fooled you,i never used you,ke ce daƙiƙiya marar wayo da kika yarda da sarkin ku yayi amfani da sanyin ki yayi amfani da ilimin ki da dabarar ki ya kusa cinma burin sa akan ki"
  "Dan haka ki sani BAMBANCI ƘASAR da ke tsakanin mu da ku ba zai taɓa bari na in mallaka maki wannan kundin ba haka zalika BAMBANCI Al'adu dake tsakanin mu da ku ba zai bar ni in zamo baiwar ku ko ahali na su zamo bayin ku ba dan akwai babbar taɓo da BAMBANCIN ƘASA ta janyowa ahali na sakamakon haka na zamo marainiya mahaifiya ta ta zamo marainiya saboda haka ki natsu ki san inda ke maki ciwo ki farka daga baccin da kike yi ki fuskanci gaskiya dan matuƙar kika cigaba da ɗora rayuwar ki bisa tafarkin da kika taso kika tsnici kan ki a kai toh akwai babbar matsala a nan gaba you either find your way out of that kingdom or you return back there"..
 
  Kaf jikin su yayi la'asar jin kalamab bakin Juda saboda duk mai hankali da sanin ya kamata zai gano cewa magana tayi daga ƙarƙashin zuciyar ta kuma magana ne mai zafi da ya fito da hucin sa tun daga zuciyar ta kuma babu shakka duk zantukar ta babu na yadawa a ciki dan gaskiya ta faɗi sai dai in son kai ake sai a yi wa zancen nata fahimta a kaikaice..

  Tun da ta fara zazzaga mata waɗannan zafafan zantuka babu abin da hankalin ta ke hasko mata sai rayuwar ta na baya a lokacin da kakar ta mahaifiyar baban ta ke nuna mata hanyar da ya dace amma saboda son zama jajirtacciya ta rufe kunnuwar ta ta cigaba da ɗaukar shawarwarin sarkin da take ma aiki,yanzu idan zantukar Juda suka zamo gaske fah?hakan na nufin ita bata da rayuwa mai inganci kenan kokuma ta zamo karya?idan kuma Judar ke mata wasa da kai fah?..
  Ɗagowa tayi ta kalli Juda da ke jiran response ɗin ta ran ta a matuƙar ɓace hakan ya nuna ƙarara a fuskar ta..
  Fizge hannun ta tayi daga riƙon da su Berenice suka mata ta naɗe hannuwar ta a ƙirjin ta tana ƙare ma Juda kallo wacce itama ita take kallo tana jiran ganin abin da zata yi..
  Sai da ta gama zaga Juda sannan ta dawo ta gaban ta ta tsaya tana mai yin ƙasa da murya ta ce
  "Kin san wani abu?ke ba mahaifiya ta ba ce haka ba ke kika haifi mahaifiya ta ba dan haka kin yi kuskure babba da kika yi wasa da ƙwaƙwalwa ta kika janyo min asarar matsayin da na daɗe ina mafarkin samu sai dai ki sani ba fah yafewa nayi ba,a'a zan rama ki tsaya ki gani"tana gama faɗin haka tayi wucewar ta sai Juda ta shiga duhu..
  Ba dai iska ta wa zantukar nan ba ganin tsawon lokacin da ta ɗauka tana ma Agneta magana amma tana gamawa Agneta tayi tafiyar ta,ina,bata gamsu ba dan haka ta wuce su Berenice ta bi bayan Agneta a guje sai su Berenice suka biyo ta suma suna kiran sunan ta..
  Duk gudun da take yi hakan bai saka ta yin katari da Agneta ba har ta cire rai sai ta hango wani tsuntsu babba a gefen ciyawa,ɗan baya ta dawo ta ƙurawa tsuntsun nan ido sai ta ga kamar ta taɓa ganin tsuntsun..
  Dawo mata yayi wato inda ta taɓa ganin tsuntsun mai siffar jemage,ai da sauri ta nufi inda tsuntsun yake tana zuwa ta hangi Agneta zaune tana wasa da tsinƙe idanun ta cikin ruwa tana danne hawayen dake son fito mata..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now