EPISODE FIFTHY SEVEN&FIFTHY EIGHT

160 22 0
                                    

EPISODE:57&58
 
ONE MONTH LATER
 
  Turkey
  Rayuwa tayi sauƙi a wun su Juda dan ba laifi suna kan koyar abubuwa da dama a fannin addinin su wanda suka aminta da shi kuma abin na masu daɗi,ana mutunta juna sosai ana daraja decision ɗin kowa da opinion nasa babu hantara bare nuna halin ko in kula ga maganar wani ko wata.
  A yayin da gimbiya Ondrea ta ke renon cikin ta tana kaf kaf da lafiyar cikin nata duk wani abu na sha'awa da zata ce tana so toh mijin ta is ever ready ya mata hakan na daɗa ƙara danƙon yarda da amincin dake tsakanin su da shi..
  Kwata kwata bai wuce kwanaki uku ba da zasu tafi yin binciken su a inda zasu fara da masarautar Ottoman,duk wasu shirye shirye da ya dace ya kamata sun yi sa kawai jiran ranar tafiyar suke yi,already Juda ta matsu ta haɗa idanu da mahaifiyar ta dan tayi kewar ta matuƙa kuma ta matsu ta nuna mata Callee da haɗuwar su ta zamo alkhairi,sannan tana son ganawa da ƙanwar ta dan ya zuwa yanzu,an nuna mata haramcin ɗaukar hukunci a hannu ta an nuna mata ta kai ƙara ga hukuma dan su yanke hukunci daidai laifin wanda ya aikata laifi..
  Abu ɗaya ke ɗawainiya da Juda a rayuwar ta,wannan abin ba komai bane illah fargaba,dan sai dai in bata haɗa ido da Cahal ba,muddin ta haɗa ido da shi toh dole ne ranar a suƙuƙu zata wuni bata san dalili ba,sau da dama tana gwada son tunkarar Callee da Berenice da batun amma tana jin wani iri duk tsoro da shakkar hakan na damin ta,a kullum in zata gan sa da matar sa toh sai fah ta ji babu daɗi a ran ta wanda bata san dalili ba..
  Bata sani ba,Fianna na ankare da duk moves ɗin ta dan yarinyar akwai lura da saurin ɗago abu,toh da yake tun lokacin da wannan abin kunyar da ya faru tsakanin ta da Balik wato ranar da suka yi clashing da shi yana wanka,toh bata ƙara sake jiki da shi ba abin mamaki har yanzu bata sake sosai ba tana ɗar ɗar da shi bata son zama wuri ɗaya da shi.
  Toh ta fara fuskantar wani hali da take tsintar kan ta a ciki a duk sadda suka haɗu wannan abin bata san menene ba haka bata san yaushe abin zai rabu da ita ba,ta so sanar da Callee amma itama haka abin sai ya rinƙa ƙaƙare mata sai ta fasa,toh lokacin da ta fara lura da Juda sai ta saka mata ido sosai dan sanin me ke damin ta,tun daga lokacin take bin diddigi tana saka ma Juda ido dan ganin ina zurfin cikin nata zai kai ta ya tsaya..

  Fitowar Agneta kenan daga wanka tana goge jikin ta tana tambayar Callee
  "Callee,yaushe wai kika ce an maki dole akan ki aminta a lalata maki rayuwa"!?kallon ta Callee tayi sai ta ɗan yi ƙasa da ido tana faɗin
  "When i was sixteen"!!ɗan dakatawa Agneta tayi daga goge jikin ta ta zo ta zauna gab da Callee sai ta kuma tambayar ta
  "Kin sanar da yayar ki"?(wato Juda kenan dan tun lokacin da Yaya take referring nata kasancewar duk cikin su ita kaɗai ce ƙarama ƴar kimanin shekaru ashirin da ɗaya)..
Girgiza kai Callee tayi tana faɗin
"Ban sanar da ita ba dan bana son mu kuma aikata jahilcim da muka yi a baya,kawai tunda babu abin da ya faru mu bar shi kawai,let's focus on the future kawai Agneta"gyaɗa kai Agneta tayi tana jimamin dalilin da ya sa ita dai har wa yau bata fara jin wani feelings akan wani ɗa namiji ba sai dai tayi mutunci da su amma batun soyayya kam,babu shi,ba wai dan babu masu nuna interest akan ta bane a'a kawai dai soyayyar ce bata ɗaɗa ta da ƙasa kawai..
  Tare suka fito dan yin breakfast a inda su Fianna suka riga su zuwa dan yanzu kamar family suke,a duk sadda Cahal ya tuno abin arziƙin da suka mai a baya na taimakon sa da matar sa sai ya ji wannan kaɗai da yake masu isn't enough,wannan dalili ya sa kawai ya yanke shawarar taimaka masu samo sauƙin rayuwar su duk da ya san matar sa ta kusa haihuwa amma a kullum yana nuna mata farin cikin da zasu yi in suka sami justice da haka ita kan ta gimbiya Ondrea ke sakawa tan ta taimako zata yi kuma lada zata samu..

  Da suka kammala cin abincin ne aka fara teasing juna kamar dai yadda suke yi a kullum,sukan tuno rayuwar su ta baya sukan yi alhinin jahilcin da suka tafka,one thing for sure they know is that sun tsallake wannan rayuwar babu maimaitawa kuma Juda ta san tarihin ta dake cikin kundin nan nata,shall always be her family legacy but the delusional illusions,are no where accommodated in her life anymore wanda a rayuwar sauran ma haka ne sun yaye wannan abubuean believes ɗin dan sun fahimci duk sihirin nasu a iya nan yankin nasu ya tsaya kuma an nuna masu hakan na faruwa ne due to meditation da delusional believe da suke yi a duk sadda abin zai faru ko zasu gudanar da wani abu,dan haka suka yi ƙoƙarin share wannan abin a rayuwar su..
  Pertaining their horses kam tuntuni Balik ya basu shawarar su sayar da su kawai su yi amfani da kuɗin su kafa wata sana'a,shawarar ya karɓu dan tun asali Juda sana'ar nasu kenan siya da sayarwa toh da wannan shawarar suka kafa sana'ar su ba tare da sun yarda da facts ɗin da Cahal ya rinƙa kawo masu na su bar wani sana'a shi zai na sponsoring nasu ba,da haka suma suka kuma wayewa dan sana'ar da Balik ke yi ya sa ya daɗa wayewa haka su Juda akan ɗan fita tare da su time to time dan yawon buɗe ido saboda duk su cire wannan mentality dake tattare da su,kuma ba laifi a yanzu duk ya tafi dan har waya suka fara riƙewa gimbiya Ondrea ce ke koya masu,abin dai kamar a mafarki rayuwa ta rinƙa sauya masu..
  Duk da wannan jin daɗin tunanin su gabaɗaya yakan ta'alaƙa akan komawa gida wun family nasu dan sukan ji kewar families nasu..
  Ko da ranakun tafiyar nasu ya matso,sai zumuɗin yayi yawa suka zaƙu su koma gidajen su though hidden facts are still hidden between Juda,Cahal,princess Ondrea,Fianna and Balik...

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now