EPISODE TWENTY FIVE&TWENTY SIX

204 25 3
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-      
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:25&26

  Yaƙi ne sosai ya kaure tsakanin Juda da Cahal wanda ya saka su canza wurin damben suka koma ta bayan harabar da suka fara yaƙin,sosai suke dambacewa da takubban su kowa na nuna irin tasa bajintar da fasahar a ɓangaren yaƙi,shi bai gaji ba haka itama Juda bata nuna alamun gajiwa ba dan haka suka rinƙa yaƙar juna har sai da suka iso wata bishiya inda Juda ta kaɓar mai da takobin sa ta haɗa sa da bishiyar,.
  Tana haki ta shiga tambayar sa kamar zata doke sa dan haushi
"Ina Balik yayan Berenice?da wa kuke tare a kasuwar nan"?shima hakin yake yi sannan ya ce da ita
  "Ban sani ba kuma ba zaki taɓa samin amsar tambayar da kika min ba"murmushin gefen baki Juda tayi sai muryar Berenice ta karaɗe wurin tana faɗin
  "Muddin baka faɗa ba toh alhakin ran gimbiya Ondrea zai rataya a kan ka dan saura ƙiris in yanka ta,,sai ka zaɓa,ko ka bayyana inda yake ko a yanka gimbiya Ondrea sannan a ɗora alhakin kisar ta a kan ka,,wanne ka zaɓa"!??kallon Berenice yayi sannan ya kalli Juda dake riƙe da wuyar rigar sa ga takobin ta a wuyar sa sai ya juyar da kai ya shiga narrating masu ainihin abin da ya faru wanda yayi sanadiyar fitowar su har suka zo wannan ƙauye,..
  Ba ƙaramnin mamaki ne ya kama Juda ba sai dai bata nuna a fuskar ta ba dan kar a gane karayar da zuciyar ta tayi.
  Berenice kuwa ihu ta saka tana mai furta
"Shikenan,,,shikenan na rasa yaya na har abada,dama barazana na so yiwa sarauniya Zinaida da ɗiyar ta gimbiya Ondrea idan muka doshi masarautar nan sai dai hakan ba abu mai yiwuwa bane ya zan yi Juda"!!da kuka ta ida maganar wanda ya saka Juda jin ta daɗa karaya da lamarin sai dai faɗin wani,tashin wani dan haka ta daka mata tsawa tana faɗin
  "Kul,,kar in kuma jin haka daga gare ki,iya abin da nake buƙata daga gare ki shine natsuwar ki dan muddin babu natsuwa tattare da ke toh lallai komai namu zai ɓaci dan haka ki daina hawayen nan"...juyowa tayi ta tsurawa Cahal ido tana mai ƙare mai kallo kafin ta mai magana
  "Ka haɗa hannu da mu mu fiddo ɗan uwan Berenice dan kai ma ka sami gimbiyar ka in ko ka ƙi yarda toh yanzu zan iya fille mata kai ban da damuwa da wannan,wanne ka zaɓa"??kallon cikin idon ta yayi,ba dan kwana biyu da yayi babu practice ba da ya san tuni ya gama da shafin Juda dan abin nata na so ya shammace sa amma yanzu da take mai baraza dole ya haƙura da burin sa akan ta dan ceto masoyiyar sa tunda dama can bai da matsala da Balik duk sharrin sarauniya Zinaida ne ya sa ya kasa ceton sa a sa'ilon da ta saka a yi garkuwa da shi...

  Iska mai huci ta huro mai a fuskar sasannan ta ce
  "Amsar ka nake jira"!!kallon ta yayi kafin ya kai duban sa ga Berenice dake tsaye tana kallon abin dake faruwa tsakanin su su biyun..
  Amsa ya bata ta hanyar saka idanun sa cikin nata idanun dake cike da masifa haɗe da tsanar da take yiwa sarauniyar da bata taɓa sanin ta ba..
"Na yarda sai dai ki sani,kuskure ɗaya,,am out"!!ingiza sa tayi sannan ta juya baya tana mai ce da Berenice ta kwance gimbiya Ondrea,komawa Berenice tayi ta kwance ɗaurin da ta mata sannan ta riƙe ta a hannu suka yi nufin tafiya...
Hanyar masarautar suka nufa wanda dama ba wata nisa ne da ita ba daga kasuwar da suka baro zuwa garin,sai dai kasancewar dare ya tsala sai suka raba daren a daji suka kwanta dan yin bacci akan washegari sai su ƙarasa zuwa masarautar...

°°°°°°°°°°°°°°°°°
Cikin baccin ta ta rinƙa jin iska na hurawa fiye da ƙima dan haka ta daɗa haɗe jikin ta wu ɗaya tana naɗe hannuwar ta daga ƙirjin ta zuwa bayan ta haɗe da daɗa naɗe ƙafafun ta tana mai gyara kan ta,sai dai kamar daɗa ƙarfin sanyin ake yi dan haka ta buɗe idanun ta sai dai bata ga sauran cikin yanayin gajiya da sanyin da ake yi ba,hakan sai ya ɗaure mata kai dan haka sai ta shiga tashi a hankali tana mai cigaba da kallon wurin,.
  Wani abu da ta lura da shi shine,yanayin ƙarfin wutan dake kamawa ya canza,dan yin sama yake yi sai yayi ƙasa da sauri wanda a zahirin gaskiya ba haka ya kamata wutar ya rinƙa kamawa ba..
  Wuf ta miƙe tsaye haɗe da fidda takobin ta tana mai nufar wutar da shi sai ta ji kamar an gudu ta bayan ta dan haka da sauri ta juya,kuma jin iskar mutum tayi a bayan ta sai ta kuma juyawa sai dai babu kowa hakan ya hazuƙa ta dan haka ta natsu ta tsaya shiru..
  Wasu abubuwan take yi a zuciyar ta wanda ita kaɗai ta san ko menene wannan abin,kamar ƙiftawar ido ta sari mutum,wanda ƙarar sarewar nan tayi daidai da tashin sauran abokan tafiyar nata..
  Kowa tashi yayi haɗe da fiddo takobin sa yana mai tambayar ko lafiya,gimbiya Ondrea dake maƙale bayan Cahal tana toshe kunnuwar ta dan tsoron da ke ɗibar ta sai ta riƙo rigar Cahal tana mai faɗin
  "Masoyi na ka zo mu gudu,,ni ban yarda da wannan yarinyar ba,hala ita ta haɗa wannan tarkon dan ta kashe mu,ni dai ka zo mu gudu"!!sarai Juda na jin ta sai dai yanzu ba lokacin biyewa shirmen ta bane sai ta yi kamar bata ji abin da gimbiya Ondrea ta faɗi ba ta maida hankalin ta ga son kamo mai yunƙurin kawo mata farmaƙi...

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now