EPISODE SIXTY THREE&SIXTY FOUR

164 24 0
                                    

EPISODE:63&64

Sanar da Sultan Baal-Hamon aka yi akan ga fah baƙi sun zo kuma ga abin da ya kawo su,sai da ƙirjin sa ya buga dan dama ya san haka kawai yarima Ziyan ba zai kawo mai ziyarar wofi ba toh shi kam ya ya san zai yi da ɗan zamani,..
Ya dai yi alƙawari akan duk runtse ba zai yarda ya rasa mulki da ikon sa ba sai dai su ƙaraci rigimar su su tafi..
Da wannan tunani ya lallaɓa ya fito falon sa n karɓar baƙi ya hakimce bisa kujerar mulkin sa yana mai bada izinin a taho masa da baƙin..
Jim kaɗan sai ga su yarima Ziyan sun shigo,fuskar yarima Ziyan kaɗai da ya kalle sai da ya ji gaban sa ya faɗi,bai san dalili ba amma yana ji a jikin sa babu alkhairi a wannan ziyarar..
Bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da su Juda suka shigo da nasu jama'ar sannan ya gane kamar fah ƙullaliya aka mai,amma ya dai dake yana jiran jin ko da me suke tafe..

Bayan zaman su ne haɗe da ƴan jaridun da suka zo tare,Sultan ya sa aka kawo masu kayan motsa baki haɗe da abubuwan kore ƙishi..
Da yake dai su ba wannan ya kawo su ba,sai basu tsaya taɓa abin ba suka mai bayanin abin dake tafe da su kamar haka
"Sultan ba tare da mun ɓatawa kan mu lokaci ba ko mun ɓata maka naka lokacin ba,abu ne mai muhimmanci ke tafe da mu kuma kamar yadda idanunwar ka suka gani,jama'ane da suka ga ya kamata su shiga wannan abubuwa da ake tuhumar ka da shi,kuma ana so cikin daɗin rai a yi komai a gama ba tare da an yi hayaniya ba,amma in ka ƙi ka ɗaga mana murya,toh fah Sultan ka sani,wannan hukuma ce mai zaman kan ta da zata iya hukunta ka yadda ta so kuma daidai laifin ka,dan haka ka bamu haɗin kai mu yi abin nan cikin jin daɗi mu rabu lafiya dan ba zuwa muka yi da nufin kwana a masarautar ka ba"..wannan jawabi ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin media and press members da yarima Ziyan ya zo da su.
Tun da ya fara jawabin sa Sultan Baal-Hamon ya rinƙa kallon sa ganin ƙeƙe da ƙeƙe fah so ake a mai ɗibar albarka a masarautar sa,toh amma kuma ya rarrashi zuciyar sa akan ya ƙara haƙuri har ya gama ganin iya gudun ruwan su..
Amsa su yayi cikin gadara da hucin zazzaɓi da ya taso sa gaba
"Ina sauraron ku,da me kuke tafe"?abin ya ɗan ba yarima Ziyan dariya ganin rashin kunyar sa a fili haka,madaɗin yayi laƙwas amma sai ya rinƙa wani cin magani shi a dole sarki kuma mai burin mallakar duniya...

Ko kafin ɗaya daga cikin press members da yarima Ziyan ya zo da su yayi magan,tuni yarima Ziyan ɗin ya riga su yin maganar ta hanyar ce da Sultan
"Amma Sultan ai ka san ba mu kaɗai bane a nan ɗin,ga wasu nan da suka zo kuma alama ya nuna,tattare suke da zantuka da in bata zo daidai da tamu ba,toh ba zai rasa nasaba da tuhumar ka ba,baka son sanin ko da me suka zo ne"?wannan tambaya a wun Sultan Baal-Hamon daidai yake da irin tambayar rainin wayon nan da rainin hankali haɗe da rashin kunya,sai dai bai ce ƙala ba ya fuskanci su Cahal da ya mai kamar ya taɓa sanin sa a wani wuri sai dai ba zai iya cewa ga takamammen inda ya san sa ba..
Kallon sa shima Cahal yayi yana baƙin cikin abin da ya mai ya kuma yi wa iyayen sa,dan kuwa Sultan ya zamo azzalumin sarki da bai da tausayi bai da imani dan yawan mutanin da ya raba da ahalain su bai ƙirguwa..
"Sultan abu ɗaya ya kawo mu,mu da waɗannan mutani kuma justice,shi muke nema daga gare ka da sauran al'umar dake sauraro da kallon mu a wannan wuri,ba zuwa muka yi dan yin kace na ce ba,kai tsaye zaka amsa mana tuhumar mu"!!mamaki ne ya gama sandarar da Sultan a wurin ganin shi ne fah mai yanke hukunci mai yin isa da nuna isa a yadda ya so amma yau waɗansu ne suka shigo mai yanki har da nuna mai basu buƙatar ɓacin lokaci dan a uzurce suke..
Lallai yayi sake ɗan zaki ya girma a gaban sa sai dai in sun san wata,ai basu san wata ba...

Jinjina kai yayi cikin takaicin ama mai rashin mutuncin gaban al'umar sa,ga ɗiyar sa da ta kasa samin matsuwa ta kasa ta tsare ita dai burin ta ta sami yarima Ziyan ko zata ji sanyi.
Fanni guda kuma,gimbiya Ondrea ce zaune ta ɗan jingina da jikin mijin ta jin kamar zazzaɓi na nemar rufe ta,ga su Juda da tun da suka shigo,babu uhm bare uhmuhm,shiru suka yi tunowa da irin darun da suka sha a baya a lokacin da suka ci burin shigar masarautar sai dai duk hakan bai yiwu ba sannan da yake lokacin shigar nasu bai kai ba,haka suka shiga ba tare da sun tsinto komai ba suka fito,ashe jinkirin alkhairi ne a gare su dan gashi sun shiga wata duniyar wacce take daban da sauran duniyar da suka fito kuma basu yin da na sanin tafiya wannan duniyar dan gashi sun sami abokan taimakon su kuma sun gano ashe ba su kaɗai bane ke farautar Sultan Baal-Hamon ba ga sauran al'uma da dama dake farautar sa,su kam nasu buƙatar bai wuce ya fito ma Juda da ƙanwar ta ba sannan ya ga sakamakon mugayen halayyar sa da ya daɗe yana yi...

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now