EPISODE SIXTY NINE&SEVENTY

511 54 5
                                    


Ya Allah am deeply in love with the nature and kindness you spread that goes on simultaneously in our lives,your immersed love and affection can not be overemphasised,for your surprises and will alone,i say thank u,most blissful the life,thought&thoughts,the time and knowledge you wished to give on to me,is something that no one can give or do,for this alone ya Rabbil A'alamin,my unconditional appreciation and gratitude is always going to increase and never decrease,thank you for the knowledge you blessed me with am happy😊..

Appreciation to all of u for d kindness and uncertain love thank u for liking me,thank you for sharing ur tym to read my writing and thank u for ur prayers towards me am happy as well😊

EPISODE:69&70

  A ƙalla watannin su Juda biyar kenan da komawa ƙasar su kuma gidan su,farkon komawar su abin was like,wannan ita ce mahaifiyar tawa and wannan ita ce ɗiya ta..
  Ga Hadara,ganin abin da ta daɗe tana marari tana muradi tana kwaɗayin gani sai ta ji kamar ko a yanzu ta bar doron ƙasar ta cika kaso casa'in da tara da ɗiga tara cikin kaso ɗari na burin ta a rayuwa..
  Yadda mutum ke fargabar dodo haka gimbiya Acenath ta rinƙa fargaba haɗe da tsoron mahaifiyar nata,duk irin janyo ta jiki da Hadara ke yi haka gimbiya Acenath ta tuɓute ita sam ba zata zauna ba..
  Tun Hadara na kuka har ta zo ta saba da rashin jituwar da ɗiyar tata ke nuna mata ta zuba mata ido tana mu'ammalar ta da sauran..
  A ranar da suka dawo,Hadara ta ga ɗiyar tata da wasu mutanin sannan ta ga Bambancin a tattare da ita tun daga suturun ta har kama ɗabi'un ta,kaf sun canza..
  Bayan an gama murnar yaushe rabo ne Hadara ta fara tambayar ta shin ya tafiyar ta ta kasance,nan ta dai ta fara gabatar mata da abokan tafiyar nata da suka dawo tare sannan ta mata bayanin komai bata ɓoye mata komai ba a ƙarshe ta ɗora da cewa,Callee ɗiyar babar ta ce Daliya kuma a halin da ake ciki ma ita kan ta abin da ya fito da ita kenan wato nemar su sannan ta dau fansar abin da aka ma ahalin su dan sun ji labarin abin da ya faru da su..
  Sosai Hadara ta kaɗu jin yadda jini ya bayyana kan sa a lokaci guda,ta matuƙar yin farin ciki da ganin wannan kyakyawar al'amari kuma ta ma Callee alƙawarin bin ta gabaɗayan su su tafi yankin da iyayen Callee ke aure..
  Yayin da Hadara ta zamo kamar kaka ga ɗiyar Cahal da gimbiya Ondrea sakamakon jin tarihin su da kuma jin cewa jaririyar bata da mahaifiya,sosai Cahal ke mutunta Hadara ganin yadda take kular mai da ɗiyar sa,sai dai game da Juda bai san matsayin sa ba dan abin na mai sarƙaƙƙiya dan haka ya barwa kan sa sani akan ko ma dai menene wataran zai bayyana...
 
  Sai dai wani abin da Hadara ta kasa ganewa shine,ganin ɗiyar ta da abokan tafiyar ta na gudanar da wani irin abin da bata san me zata ce da shi,shin ibada ne ko me?..
  Rannan suna zaune bayan sun kammala ibadar sai Hadara ta ja ɗiyar ta suka shige ɗaki sai ta mata tambaya game da wannan abin da suke yi,babu nauyin baki Juda ta kuma ƙara mata haske haɗe da sanar da ita ummul aba'isin ɗin kafuwar su akan wannan addini kana ta ɗora da nuna mata falalar addinin haɗe da kwaɗaita mata addinin..
  Duk da kan Hadara ya ƙulle amma haka ta yi shiru tana sauraron ɗiyar tata ƙarshe dai da Juda ta fuskanci kamar ba yarda sosai mahaifiyar tata tayi da addinin ba sai ta ware lokaci ta zauna ta shiga fayyace mata komai akan addinin har sai da dare ya tsala sannan ta rabu da ita ta koma wun sauran inda ta ɗau jinjirar gimbiya Ondrea tana rarrashin ta sakamakon kukan da yarinyar ke yi ga kuma Cahal dake ta rarrashin yarinyar amma sai kuka take yi..
  Ita dai gimbiya Acenath na kallon su duk abin da suke yi amma bata ce da su ƙala ba dan ba ta su take ba kawai kewar mahaifin ta da iyayen ta take yi,dan har yanzu ba yarda tayi akan cewa wannan matar bace mahaifiyar ta..
  Sau da dama Hadara kan zauna ta yi kuka tayi takaici da baƙin cikin ƙiyayar ta da Sultan ya jefa a rai da zuciyar ɗiyar ta,dan gashi ɗiyar ta da ta daɗe tana mararin gani tana begen gani har ciwo ya kama ta akan ta tana gudun ta bata son zama inuwa ɗaya da ita duk dan bata yarda akan cewa ita ta haife ta ba..
  Haka lokaci ya cigaba da tafiya har tsawon wata guda zuwa lokacin sun saba da hallayar gimbiya Acenath kuma suma sun zuba mata ido tana abin da ran ta ya so,rashin kunya sai wanda ya ƙaru,sam bata zama inuwa ɗaya da su tsabar ƙiyayya da tsana..
  Ana haka ne aka shirya tafiya zuwa yankin su Callee dan a sada zumunci kana a dawo kamar ahali ɗaya tunda a baya ba a yi ba,sosai Callee tayi farinciki akan zata tafi gida ta ga iyayen ta dan ta yi kewar su sosai..
  Ko da ake haɗe haɗen kayan tafiya,haka gimbiya Acenath ta zauna tana kallon su kamar zombie,sau ba adadi takan yi shirin gudu amma sai ta rasa hanya ƙarshe dawowa take yi cikin baƙin cikin..
  Su kan su suna kewar Berenice,Balik da Fianna sosai sai dai sun sakawa ran su in da rai wataran za a gana..
  Da haka suka shirya suka kama hanya suka nufi yankin su Callee duk da an sami matsalar hanya dan da keken doki suka tafi hakan ya sa suka ga tafiyar ta masu tsayi..
  Abin farin ciki ne a ce bayan lokaci mai tsayi ahali guda sun haɗe wu ɗaya abin burgewa ne dan haka aka yi haba haba da juna,sun kasa nemar junan su amma ƴaƴa sun haɗa su,indeed sun ji mutuwar ɗan uwan su mahaifin Juda kuma sun tabbatar Juda mahaifin ta ta gado a ko ta ko ina,..
  Sosai suka sake jikin su a nan sai dai abin da yake damin su Juda shine yadda zasu masu bayanin su tattara ya nasu ya nasu su bar wannan daji da suke rayuwa in ya so sai su koma can ƙasar da Cahal ya kafa sansanin sa wato Turkey..
  Tun suna jan abin har dai wataran Callee ta fito gar da gar ta sanar da su manufar su da kuma dalilin su kana ta kuma nuna masu cewa a can an fi yin rayuwar cikakkun ƴan adam babu tsangwama sannan ta ce da su ko su zo su tafi ko su su wuce dan babu wani fa'ida zaman daji ana gudanar da rayuwar tumakai..
  At first iyayen sun so yin gardama amma ganin an ce da su an share tarihin Sultan Baal-Hamon duk da ba a gama tabbatarwa ko ya rasu ko a'a ba amma an sanar da su akan irin lahanin da aka masa da zai yi wuya ya farka da ran sa..
  Da haka fah ne suka kuma tattarawa suka bar yankin Babylon all those ideas and zeal to avenge Juda's grandfather's Empire were gone,dan kwata kwata ta cire sa a ran ta ta barwa Allah akan ya saka masu dan tauhidi ya ratsa ta ta san kyakyawa ko mummuna duk daga ubangiji ne dan haka ta barwa Allah komai haka ma iyayen nasu suka ɗau dangana suka barwa Allah..
  Duk da jan jikin da gimbiya Acenath ke yi da su sai da suka janyo ta jiki dole ta ɗan sassauto ba dan ta yi niya ba..
Tiryan tiryan suka kama hanya suka rinƙa sharara tafiya har suka kawo inda suka sami abin hawa na zamani,suka sallami mai keken dokin suka yi tafiyar su...

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now