EPISODE SIXTY ONE&SIXTY TWO

174 21 0
                                    

EPISODE:61&62

  Wani irin tsawa Sultan Baal-Hamon yayi cikin tsantsar ɓacin rai dan baya jin bayan wannan ɗibar albarkar da yarima Ziyan ya mai zai kuma bari ya fuskanci wata cin zarafin daga gare sa ta dalilin ta..
  Sarai tana jin muryar sa yana kiran ta amma ta ƙyale sa ta cigaba da kiran sunan yarima Ziyan dan a halin yanzu shi kaɗai take mararin gani dan ta nuna mai amintaccen soyayya da ƙaunar da take mai sannan ta tabbatar mai da cewa akan son sa tana iya yin komai ciki har da karɓar musulinci..
  Tana fitowa daidai step na ƙarshen matakalar da ya sada fadar da farfajiyar masarautar,ganin sa tayi yana yunƙurin shiga motar sa da ya taho da ita dan shi bai aminta da al'adar nan..
  Tsayawa tayi tana kallon sa hankali tashe cikin haki ta ja ta tsaya tana mai ƙare mai kallo idanun ta cike tam da hawaye ta fara mai magana
"Yarima Ziyan Aman,na san mahaifi na mai laifi ne kuma mai zunubi ne dan tun kwanakin baya na gano hakan sakamakon sabon baƙon mu da muka yi wanda mahaifi na ne ya kawo sa,mutumin ya koya min abubuwa masu kyau kuma na ƙaru sosai dan hakan ne ma ya sa da ka ce in baka kai na na ƙi kuma a yanzu da na ji kalaman ka ga mahaifi na akan addinin ka da kake yi sai na ji ni kaina ina sha'awar zamowa ɗaya daga cikin mabiya addinin nan naka kuma da zuciya ɗaya nake son zamowa ɗaya daga cikin ku ka yarda da ni,iya gaskiya ta kenan yarima Ziyan ni dai ka yarda ka aure ni kar laifin mahaifi na ya shafe ni,ka min rai"..
  Dakatawa yayi daga shiga motar da zai yi ya dawo ya tsaya haɗe da rufe murfin motar,tsayawa yayi a gaban ta ya naɗe hannayen sa a ƙirjin sa yana ƙare mata kallo dan gasgata zantukar ta in da gaske ne..
  Sai da ya ɗau lokaci mai tsawo yana ƙare mata kallo kafin yayi magana
"kina ganin ni zan yarda na aure ki ne"?nan da nan gaban ta ya faɗi dama mahaifin ta Sultan ya daɗe da fitowa kuma duk ƙasƙancin da ɗiyar sa ta yi a gaban idanun sa ta yi sa dan haka cikin fuƙula ya taho ya janyo ta ya juyo ta tana kallon sa,ko kafin ta ankara ta ji saukar marin sa ga kumatun ta abin da bai taɓa faruwa ba kenan tun da aka haife ta..
  Ba ita kaɗai ba,hatta da shi kan sa yariman sai da ya girgiza haka kaf mutanin wurin sai da abin ya kaɗa su,yayin da sarauniya Bayarma ta saka hannu a baki ta zazzaro idanu waje tana kallon Sultan Baal-Hamon ɗin da yayi extending hannun sa yana huci cikin tsantsar ɓacin rai,Calva kan ta sai da ta girgiza ganin abin da Sultan Baal-Hamon ya aikata..
  Cikin tsantsar mamaki da girgiza gimbiya Acenath ta ɗago idanun ta tana kallon mahaifin nata tana mai jin mamakin sa at the same time idanun ta ya kaɗa yayi jawur sai hawaye ya fara gangaro mata..
  Sai da farfajiyar masarautar nan ta ɗauke wuta na wasu lokuta kafin daga bisani cikin ɓacin rai Sultan Baal-Hamon ya nuna ta da hannu yana faɗin
  "Akan ki,ba zan rasa mutunci na ba sannan ki sanj,ko da mutuwa zaki yi ba zan aura maki wannan fanɗɗararren yaron ba dan dama na sani,tarayyar ku babu alkhairi a cikin ta sai sharri dan gashi nan tun yanzu na fara gani,dan haka sai dai ki mutu amma ba zan bada auren ki ga wannan marar kunyar yaron ba kuma ki wuce cikin gida yanzun nan tun kafin rai na ya ɓaci"!!!a tsawace ya ida maganar wanda ya kuma ɗaga hankalin sarauniya Bayarma a inda ta tako har gaban Sultan tana faɗin
  "Ka ji kunya Sultan,ka ji kunyar duniya Sultan,ɗiyar ka,ƙwara ɗaya da kake da ita,har ka iya ɗaga hannun ka ka mare ta ko nauyi da ɗar baka ji ba,duk saboda wani dalili naka,duk abin da yarima Ziyan ya faɗa maka sam babu shakka,hakan ne dan akan wannan son zuciya taka da son duniya da ka ɗorawa kan ka toh zaka rarumowa kan ka ne fitina kuma nutuwar wulaƙancin zaka yi Sultan dan haka ina shawartar ka da ka rufa mana asiri ka karɓi laifin ka kayi nadama ka tuba dan yanzu ba kamar da bane,kusan kowa ya san illar koyarwar ka Sultan kawai shiru aka yi dan ana shakkar ka ana gudun kar ran ka ya ɓaci amma batun gaskiya shine,wannan baƙo naka ya rigada ya gama nuna mana,dukkan mu,hanya me ɓillewa dan haka kai ma zai fiye maka alkhairi Sultan in ka rabu da son duniyar nan ka rungumi ƙaddarar da ubangiji ya maka,duk wannan faɗace faɗacen ba zai kawo mana hanya mai kyawu ba Sultan,ka duba irin wahalhalu da faɗi tashin da jajirtattun sarakuna da amintattun sojojin masarautar nan suka kashe rayuwar ka dan kafa kyakyawar tarihin masarautar nan amma haka ka saka ƙafa ka shure sa,Sultan,tun kana da iko ka tuba,ka karɓi defeat ɗin nan tun kana da dama,ka ji"??..
  Ƙala bai ce da ita ba dan ya san yayi ba daidai ba kuma ya san lokaci ya kawo mai da zai yi nadama ya kuma yar da makaman yaƙin sa ya fuskanci gaskiya dan ko a baya a sanar da shi kafin ya aiwatar da abin nan da ya aiwatar sai dai bai san ta yaya zai fuskanci hakan ba bai san ya zai yarda ya karɓi defeat ba..
  Ɗago kan sa yayi ya kalle ta sannan ya kalli tsibin mutanin dake tsaye waɗanda ke a ƙarƙashin sa yana mulkar su ta hanyar da bai dace ba shi kan sa ya sani sai dai baya jin yana iya yarda da defeat..
  Juyawa yayi yayi shigewar sa ko kallon su bai yi ba haka zuciyar sa ta rinƙa hasaso mai abubuwan da ya faru earlier,a yadda yayi tafiyar sa ba tare da ya tsaya amsa bayanan matar sa ba haka kuma babu wanda ya dakatar da shi wai dan ya tsaya ya amsa bayanin sarauniya Bayarma..
  Shi dai yarima Ziyan Aman haka yayi shigewar sa motar sa iyayen sa ma suka biyo sa suka shige sauran ƴan tsaron su suka hau dawakan su suka biyo su a baya,haka suka bar masarautar Ottoman suka kama hanya suka yi tafiyar su tare da barin ɗumbin abin mamaki a masarautar Sultan...

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now