EPISODE FOURTHY FIVE&FOURTHY SIX

175 24 0
                                    

EPISODE:45&46

Babu inda suka dakata tun da suka ɗauko tafiyar nan sai a masarautar Sultan mai mulki da isa,haka duk suka diddiro daga dawakan su suka ja akalar su zuwa wani hanyar daban ta yadda babu wanda zai yi la'akari da su dan su sami damar shigar masarautar cikin kwanciyar hankali..
Baccus ne a gaba yayin da su kuma matan ke tsakiyan su sai Balik a bayan su dan gudun abin da ka kai dawo..
Tun da suka doshi babbar ƙofar masarautar da ya sha ado da kwalliyar zinari da azurfa gaban Juda ya rinƙa faɗi bata san dalili ba amma ta san ta tsinci kan ta awani yanayi da bata san dalili ba haka bata san mafarin sa ba..

Wani irin shararriyar tafiya suka rinƙa yi kamar dai ba wannan ƙofar da suke hanga zasu dosa ba dan kuwa tafiyar ya basu mamaki saboda a zahiri dai ga su ne ga ƙofar amma tafiyar sai ta ɗare yadda suka yi zato..
A haka sai da suka ɗan jigatu kafin su nufo ƙofar sai dai tsaro da sihirin da aka ma ƙofar duk ya saka su ruɗu in aka cire Baccus da zuciyar sa ta bushe sam baya ma jin wani shakka ko ɗar dan ya san dole wani rai ya bar jikin mammalakin sa toh yanzu shi a shirye yake ko nasa ran ne zai rasa ya aminta ya rasa in dai zai ga bayan wannan mugun Sultan..
Kallon su yayi yana tausaya masu dan dole wani a cikin su ya rasa rayuwar sa sai dai sanin wanda zai rasa rayuwar ne bai yi ba amma ya san da wuya su shiga dukkan su sannan su fito ƙalau da rayukan su babu wanda ya rasa..
Ɗan hasashe yayi sannan ya kalli Balik ya ce da shi
"Kai ne babba duk a cikin su haka kaine wanda ya fi cancanta ka fara shigewa gaba dan ganin komai ya tafi bisa tsari amma kasancewar na gano baka da wannan ɓoyayyen sihirin ƙanwar ka ce kaɗai mai ita toh ita zata jagoranci shigar yayin da Agneta kuma zata rufe shigar ita zata kasance a bayan mu mu duka"..ɗan shiru yayi kafin ya cigaba
"Sai dai kamar yadda na faɗa maku ne a baya ba dole yadda kuka shiga da rayukan ku ku fito duka da rayukan ku ba dole ayi asarar wani dan a ceto wani wannan ƙa'ida ce da haka take ko a da tun zamanin mayaƙan mu da mazan fama saboda kuna da damar yi wa kan ku bankwanan ƙarshe dan baku san ya yaƙin zai kasance ba"..
Wannan ƴar tunatarwar da ya masu ya jijjiga su haka ya sanya su jin shakkar fuskantar masarautar amma da yake Agneta akwai zuciya dan ta fi ita kanta jagoran yaƙin zuciya(Juda)sai ta basar da shakkun nata kawai ta ce
"Kawu Baccus kar ka damu kar ka yi shakka in dai zamu sami abin da muke buƙata mu kuma ƙasƙantar da wannan azzalumin Sultan,,,toh gare mu ko da rayuka sama da ɗaya zasu salwanta,,ba damuwa ba ce dan biyan buƙata ya fi dogon buri"..
Gyaɗa kai kawai suka rinƙa yi dan confidence ɗin ta da iya tsara maganar ta ya sa suka sami ƙwarin gwiwa akan duk wani tsanani na tare da sauƙi..

Gaba Baccus yayi yana mai riƙo hannun Berenice yayin da sauran suka biyo sa a baya,shi yayi leading suna hango masu tsaron ya rinƙa karanto wasu abunuwa yana umartar Berenice da ta nanata haka ta rinƙa nanatawa sai can ya janye ya koma baya ita kuma ta matso gaba..
Waɗannan kalamai ta rinƙa nanatawa sai kamar a mafarki ƙofar ta ɗan buɗu suka zazzaro idanun su waje sai Berenice ta shige Baccus ya biyo ta sai sauran ma suka biyo a ƙarshe Balik ne ke gaban Agneta wacce ita ce ta rufe shigar da wasu siddabarun ta..

Abin mamaki babu wanda yayi la'akari da shigar su wannan masarautar sai su abin su dan ba pure natural entry suka yi ba an yi ne ta burga da sihiri..
Tun da suka shiga wannan masarautar Fianna ke bin sa da kallo a haka ma wai basu ƙarasa cikin masarautar ba kenan nan a bakin hanya ce da ta raba masarautar kashi kashi dan haka ba lallai bane su gano ainihin hanyar sashin Dacey wato karuwar Sultan Baal-Hamon..
Wata dabara ce ta faɗowa Callee akan me zai hana su raba jiki tunda suna da yawa sai kowa ya nufi sashi daban daban dan rage yawan lokacin da zasu ɗauka a bincike mai dogon zango..
Duk sun yi na'am da wamnan shawara nata sai dai Baccus na tausaya masu dan za'a rasa rai amma bai nuna masu tsaurin abin ba..
Da haka ne suka rarraba kawunan su suka bazama shiga cikin wannan babbar masarautar suna bincike wanda babu wani a cikin wannan masarautar da yayi la'akari da su dan sam babu mai ganin su sakamakon ɓace ma ganin mutum da Baccus yayi amfani da shi dan ganin sun yi nasara a abin da ya kawo su..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now