EPISODE FOURTHY ONE&FOURTHY TWO

179 22 0
                                    

EPISODE:41&42
"Kin ce daga Babylon kika fito Callee"?gyaɗa mata kai Callee tayi tana mai jin nadamar ɓoye asalin ta da tayi tun fari sai Juda ta ɗan ji faɗuwar gaba kafin ta ce
"Ni ma..daga Babylon na fito sai dai yankin mu daban da naku dan ƴan yankin mu ba haka suke shiga ba"!cikin ɗar ɗar Callee ta ɗago idanun ta ta ɗora su bisa fuskar Juda sannan ta amsa mata da
"Eh,yankin da na fito ya yanka hanya ya shiga ta kudancin ainihin ƙasar Babylon kuma mu mutanin yankin mu da yawan su ƴan gudun hijira ne amma akwai ɗaiɗaiku da suke ainihin ƴan yankin"!!kallo ne ya dawo kan su,duk sai suka maida hankali kan su Juda da son gano wani abu game da Callee..
Ɗan kasaƙe Juda tayi kafin ta dubi Callee ta fara yi mata wasu tambayoyi
"Dama ke ƴar gidan mayaƙa ne ko kuma tsinto ki aka ui aka koya maki yaƙin sannan menene ainihin abin da ya fito da ke daga yankin ku zuwa nan Ottoman"?ɗan shiru Callee tayi kafin ta amsa tambayoyin Juda
"Eh,ni ƴar gidan mayaƙa me dan mahaifi na a yawon yaƙin sa ne ya haɗu da mahaifiya ta ya aure ta ya baro ta da yankin ta da ƴan uwan ta sannan abin da ya fito da ni daga yankin mu zuwa wannan yanki na Ottoman ba komai bane face fansa da ramuwar abin da sarkin wannan masarauta ya min dan ya cutar da ni da ahali na fiye da tunanin mutum"!muryar ta ne ya fara sarƙewa yayin da take maganar dan haka tayi shiru kawai ta bar maganar dan in ta cigaba toh tabbasa da kuka zata ƙarasa maganar haɗe da ɓacin zuciya..
Babu wanda bai fahimci shirun Callee ba dan kowa has a story to say amma na wani ya fi na wani shi yasa babu wanda ya takura mata akan sai ta kai ƙarshen batun ta dama iya tambayoyin da Juda ta mata kenan dan haka ta amsa su ko da ba cikakken amsa bane..
Ɗan share hawayenm tayi tana jan hanci ta cigaba da magana kamar haka
"Ban yi zaton sarki Sultan Baal-Hamon ya ƙwarai a zalunci da ƙeta har haka ba sai da na shirya fitowa farautar sa inda a nan na haɗu da wasu mutani biyu,mace da namiji..shi namijin ya taɓa taimaka min a wata rana da nayi dare na rasa wurin kwana sannan bana jin wani ƙarfi a jiki na sai da na tsaya a hanya na rage gajiya sannan wannan mutumin ya zo wucewa sai ya gan ni,a nan ya tambaye ni ko ɓatar hanya nayi na ce da shi a'a sai na mai bayanin abin da ya fito da ni,da fari kamar ba zai taimaka min ba sai kuma ya taimake ni har ya kai ni gidan sa sai na ga wata budurwa,a cewar sa ita ce matar da zai aura,a nan gidan na kwana sai a washegari ya rako ni hanya mafi sauƙin kawowa wannan masarauta sannan ya sanar da ni cewa duk wanda na gani a wannan hanyar toh in san da cewa gidan masarauta zai tafi kuma masarautar sarki Sultan Baal-Hamon dan haka in bin shi mu tara hanya amma kar in yarda in bayyana abin da zai kai ni masarautar illa in an tambaye ni in ce ai abin da zai kai mutumin shi zai kai ni".
"Ya ce da ni in yi wayo a tafiya ta sannan in yi abin da ya kamata dan shima yana nan a hanyar zuwa wannan masarauta domin ɗaukar fansar abin da aka mai shi da ahalin sa,abin da ya bani mamaki kenan na ga ba ni kaɗai wannan sarki ya zalunta ba kenan ashe har da wasu".
"Mun rabu bamu san sunan junan mu ba zan wuce na ɗaga murya na tambaye sa sunan sa sai ya amsa min da_'Cah'_ daga haka ban ƙarasa jin sunan ba sakamakon bige ni a kai da na ji an yi wanda ba kowa bane illa Fianna".tana kaiwa nan aka maido ido ga Fianna dake tsaye tana bin su da ido kamar marar gaskiya..
Cigaba da magana Callee tayi
"Ko da na buɗe ido na sai na gan ta a kai na tana tambaya na ina ma fito kuma ina zan tafi sai na rasa amsar bata sai na kawar da kai na.toh da yake ta girme ni kuma ta fini girman jiki sai tayi nasara akai na ta yaƙe ni,abin bai zo mana da sauƙi ba sai da muka yi sosai sannan na ce da ita masarautar Ottoman zan tafi sannan na ga ta ja baya,a ƙalla kwanakin mu uku tare a wannan jejin da na farka na tsinci kan mu a ciki,sai a rana na huɗu ne muka cigaba da tafiya sama sama mukan ɗan yi magana wanda a cikin maganan ne nake daɗa tantance baƙin hali irin na Sultan Baal-Hamon kuma a tare da ita na daɗa gano amfanin sirri dan Fianna bata da sirri komai faɗa min take yi ni ban san dalili ba".
"Wata rana mun yi dare sai muka dakata a wata mashaya dan rage gajiya sai muka sa aka kirawo mana mai mashayar dan mu mai bayanin saboda ya bar mu mu kwana a nan wurin,bayan an kirawo sa ne sai muka gan sa da shirin mayaƙa abin ya bamu mamaki muka rinƙa kallon sa sai ya ce da mu kar mu yi mamakin ganin sa a wannan suffar dan shi haka yake kullum cikin shirin ta kwana dan jiraye yake da mutanin masarauta Ottoman yana iya yiwuwa da haɗin bakin mu aka turo mu dan mu zo mu yaƙe sa ko mu kawo masa hari"
"Bayanin komai muka masa dangane da abin da muma ya kawo mu nan ɗin sai shima ya fara bamu labarin kan sa inda a nan yake nuna mana ai yanzu ba zamu taɓa samin galabar shiga masarautar ba dan an tsaface sa da baƙin sihiri babu mai iya shigar sa kai tsaye sai amintaccen ɗan gidan amma mu bari nan da kwanaki ashirin mu dawo gare sa zai taimaka mana mu shiga da sharaɗin muma zamu taimaka masa"
"Ko da muka kwana muka bar wurin ni da Fianna a nan muka bar mai shawarar sa dan gani muke surutu kawai yake yi saboda shekarun sa sun fara ja,a daren muka nufi masarautar sai abin da ya ce da mu ya faru muka gani da idanun mu,sai a sannan muka yarda da batun sa amma Fianna na ta ƙoƙarin goge min abin a kai na ni kuma na nuna mata mu koma gare sa dan sanin menene sihirin"
"Da muka koma bamu gan sa ba sai da dare dan haka muka mai bayanin komai sai ya mana dariya ya ce ai ya faɗa mana muka ƙi yarda ya ce da mu shekarun sa sama da ashirin da biyu yana harin masarautar nan amma bai taɓa yin galaba akan sa ba a cewar sa shi ɗin daga ƙasar Cyprus ya fito kuma abu mai muhimmanci ya fito da shi amma sakamakon rashin nasarar da yake ta samin sa dole ya haƙura ya kafa sansanin sa a nan Ottoman ya kuma kafa kasuwancin sa inda har baki ɗaya yankin Ottoman suka san sa da wannan sana'a tasa wato na saida giya(popular bear seller)ya kuma sanar da mu sunan sa wato Baccus".
"Alƙawari ya mana akan akwai abin da yake jira ya iso hannun sa dan ya shigo garin ko amma bai kamo hanyar zuwa gare sa ba amma yana shigowa zai warware wannan sihiri kuma komai zai zo ƙarshe dan haka muka yi da shi akan zamu rinƙa ziyartar sa lokaci zuwa lokaci dan jin ina aka kwana"..
"Tun bayan barin mu wurin sa bamu kuma komawa ba amma muka shirya cikin dare muka zo masarautar da kan mu a ranar ne muka haɗu da ku kuma ko a kwanakin da muka yi da ku muna fita nemo masanin sirrin sihirin nan duk muna sane kuma muna ankare akan cewa akwai mai taimakon mu amma ban san dalilin Fianna na hanawa mu je mu same sa ba"..

A nan ta dasa aya wanda ya bar su Agneta da Berenice cikin duhu da tunanin wai halan Fianna wace irin mutum ce ita..
Balik ne yayi ƙarfin halin tambayar Fianna dalilin ta na yin hakan ita kuma bata ɓoye masu ba ta amsa mai
"Ban da wata dalili da ta wuce na son samo komai da kai na dan alƙawari sarki Malik ya min akan in har na iya sarrafa duk wata matsalar da zata tunkare ni da kai na ba tare da taimakon kowa ba toh zai naɗa ni a mulkin da bai taɓa naɗa kowa ba sannan yace da ni zai ɗaukaka daraja ta fiye da na matar sa ni kuma na ɗau wannan alƙawari nasa a kai na na bar wa kaina sirrin komai akan bayan maganar nemar mai sanin sirrin sihirin ya lafa sai in saci jiki in koma gare sa in mai bayanin komai in ya so sai ya bani sirrin,toh sai kuma na ga abin da ya faru ɗazu na ga kundin da sarki Malik ke ta kwatanta min da kuma siffanta min sai na ɗauke a nufi na in koma wun wannan mai siyar da giyar in nuna mai in ya so sai ya warware min ban san akwai ɓoyayyiya a ƙasa ba sai yanzu"!!ajiyar zuciya Juda ta sauke tana mamakin Fianna da rashin wayon ta da take ma kallon wayo ne ita ya ta san ko da gaske shi mai siyar da giyar ba cutan ta zai yi ba ya ƙwace kundin ya gudu ba sannan ita ya bar ta a tutan babu..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now