EPISODE SEVENTEEN&EIGHTEEN

201 31 4
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-       
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:17&18

  CIKAKKEN TARIHIN SULTAN BAAL-HAMON SARKIN MASARAUTAR OTTOMAN DAKE KAN MULKI

Sarki sultan Baal-Hamon ya kasance ɗa ɗaya tilo wun marigayi sarki sultan Abdul-Hamid wanda ya rasu yana ɗan shekara tamanin(90years)kuma babu jimawa matar sa ta rasu itama suka bar ɗan su ƙwara ɗaya a duniya wanda a lokacin da iyayen sa suka haife sa girma ta zo masu dan kusa shekarar su arba'in da biyar lokacin har sun cire rai da tsammani sai Allah ya azurta su da ɗa wanda suka sakawa suna _Baal-Hamon mai jiran gado_ dan ita mahaifiyar sa ma so tayi a ɗora sa a karagar mulki tun ranar da aka haife sa saboda yanayi na rayuwa sai dai mahaifin sa bai bi hakan ba a madaɗin ya ɗau shawarar ta sai kawai ya tadi fadar masarautar sa ya sa aka tara mai jama'ar fada gabaɗaya,sai da suka taru sannan ya sabnar da su ko da zai faɗi ya mutu babu wani sarki da zai hau kan karagar mulkin nan kamar ɗan sa dan gado ne da iyaye d kakannin kakanni (Ancestors)suka hau suka bar wa ƴaƴa da jikokin su..

Bayan sati ɗaya da haihuwar sultan Baal-Hamon sai sarki ya kuma tara jama'a,amma a wannan karon,kaf jama'ar ƙasar Ottoman ya tara dan ya nuna masu baiwar da Allah ya mai bayan ya cire tsammani sannan ya sanar da su matsayin ɗan sa a wun sa haka a idanun su ma..
  Shagali aka yi sosai dan wannan rana ya zo ma sultan Abdul-Hamid ne a matsayin ranar bikin haihuwar ɗan sa ɗaya tilo shi yasa yayi amfani da damar ya rangaɗa masu dokoki da kuma biyayyar da ya kamata su ma ɗan sa ko da baya so..
  An rabu mutani na auna irin wannan so da ƙauna da sarki ke ma ɗan sa yarima Baal-Hamon dan abin kamar yayi tsauri da yawa,amma su a su wa da zasu ja da maganar sarki wanda yake nan kamar tambarin da aka yi da dalma ba'a isa a goge sa ba.. 

  Tun yarima sultan Baal-Hamon na ɗan shekara goma ya fara posessing qualities ɗin sarki ga mugun ɗaure fuska kamar sarki,ga jan aji da izza kamar dai shine sarkin sannan kaf abokan sa ƴaƴan manya ne baya kallon kowa da gashi a kai sam bai da tarbiya dan iyayen sa na ganin shine ɗaya Allah ya basu dan haka suka sakankance suna shagwaɓa shi suka sangarta shi ta yadda kowa a ƙasƙance yake kallon sa bai kai matsayin a bashi ƴanci ba. 
  Yana shekaru goma sha tara ya maye gurbin mahaifin sa ba wai dan ya rasu ba sai dan tsantsar so da ƙaunar da yake ma ɗan nasa..
  Baal-Hamon ya kasance yaro mai son kan sa da yawa haka zalika yana son rayuwa wato jin daɗin rayuwa haɗe da holewa,duk da iyayen sa su suka kafa tarihin zamani irin ta ƴan yanzu wato daga zamanin mahaifin sa ne boko ya samo asali kuma addini ya ɗarsu a zukatan mutanin yankin fiye da da da iyaye da kakanni suka kafa tarihi,a mulkin mahaifin sa ne komai ya hau kan tsari,amma abin mamaki babba shine,Baal-Hamon bai yarda ya lamunce da wannan tsarin na iyayen sa ba hatta da karatun gatar da ake ma a gida wato karatun boko,bai ɗaukar sa a matsayin komai ya fi ganin kamar tunanin sa da hasashen sa na kusan shekaru sama da ɗari uku da ɗoriya shi ya fi dacewa da shi haka wayon sa da dabarar sa yana nuna mai wataran shi zai mulki duniya muddin ya juya hannun agogo baya.wato dai ya maida yanzu ya koma gaba sai ya dawo da shekarun baya ya zo a yanzu dan tsarin sa kaf ya ta'allaƙa ne akan mulkin ancestors ɗin sa kuma ko da mahaifin sa na raye ne hakan zan yi dan shi bai yarda da tsarin mahaifin sa na zamanin nan ba wai an kawo ilimin zamani(westernization)..
  Kawai shi so yake yayi mulki da ƙarfin isa haɗe da ƙaurin suna kamar na kakannin kakannin sa sam bai son yayi mulki irin na yanzu..

Toh bayan hawan sa mulki da shekaru goma daidai ya kai shekara ashirin da tara yana gab da shiga talatin a lokacin yayi aure mahaifin sa ya aura masa ɗiyar amintaccen abokin sa wanda shima ɗin sarki ne daga ƙasar Baghdad kuma aƙidar su ta zo ɗaya,bayan an ɗaura masa aure da gimbiyar ne mai suna Gimbiya Bayarma Allah ya azurta su da ɗiya mace kyakyawar gaske murna kan murna abin ba'a cewa komai dan gatancin da yake ma ɗiyar nan tasa abin ya wuce tunanin mutum.so tsantsa yake wa yarinyar kuma ya ma kan sa alƙawarin har duniya ta naɗe ɗiyar sa ba zata ɗanɗani azabar karatun zamani ba dan shi gani yake kamar karatun ma azaba ce shi yasa yayi abolishing nasa gabaki ɗaya ya rinƙa ɗora ɗiyar sa akan turbar da ya taso har ma ya so ya fiye hakan..a haka ta ya rinƙa gudanar da mulkin sa wanda a daidai wannan lokacin ne mahaifin sa ya kamu da ciwo sosai dan girma ya rigada ya fara shigo mai kuma ya ɗan tsagaita da yaƙin da yake fita yi sai abin ya mai yawa iyakar sa zaman gida wanda bai saba ba,jikin sa ya saba da fita fafatawa amma yanzu dole ya haƙura ya bar wa ƴan baya da ɗan sa wanda ya kusan zame masa ciwon ido dan kuwa ya fara gane manufar ɗan nasa ya kuma gane illar gatancin da suka ba ɗan nasu dan gashi nan ya gama sakawa an canza tsati da launin masarautar da ya daɗe ana tsara sa da zinarai da yaƙuti da gwalagwalai duk dan a ƙawata shi..
  Kaf ya saka aka kwashe su aka kawo mai nasa ra'ayin sannan waɗannan ya saka aka karyar da su aka kawo mai maƙudan kudaɗe ya fantama da su ya kuma ƙawata tsarin masarautar sa ya mai da sa irin samfarin na mutanin da ya zuba dokoki masu tsauri haɗe da korar duk wasu masu ilimin zamani dake son kawo cigaba a yankin nasa,bai tsaya a iya nan ba daga baya ma daina korar ƴan bokon yayi ya koma sakawa a rinƙa garkuwa da su ana yanka su har mutuwa dan yana ganin in har ya bar su da rayukan su toh tsaf zasu iya zuwa su ɓarke mai wata ɓarakar ta yadda zai dawo ya ɓata mai aikin sa da yake ƙudirin yi..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now