EPISODE THIRTEEN&FOURTEEN

266 37 1
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}     
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:13&14

Cikin ƙaraje Berenice ta fara magana kamar haka
  "Kamar dai yadda na sanar da ke ainihin sunana Berenice sai dai ban faɗa maki sunan mahaifi na ba wanda sunan shi Habaccus ne kuma ya zamanto babban mayaƙi ne ba mai farauta ba kamar yadda na sanar da ke a baya ba,mahaifi na mu biyu kaɗai ya hafa ni da yaya na Habilah wanda ya ke nan ɗaure yanzu da haka sakamakon kama shi da aka yi yana hira da ɗiyar sarki gimbiya Ondrea wanda aka ce tsageranci ne kawai yake nunawa in ba haka ba ina shi ina gimbiya hakan ya sa aka kame shi mahaifin mu kuma dama yana ɗaya daga cikin jigajigan masu kula da masarautar Mughal(Mughal empire) wanda hakan ne ma ya sa ba'a yankewa yaya na hukunci ba dan girman mahaifin mu da ake gani,toh wannan abin ne ya sa mahaifin mu kasa riƙe baƙin cikin har ya faɗi ya mutu ba tare da an sani ba dama mahaifiyar mu ta daɗe da barin doron ƙasar nan mahaifin mu ne ke kula da mu shi ya koya mana yaƙi ya kuma sanya min sunan sarauniya"..
   "Kafin ya mutu ne ya saka ni ɗaukar mai wata babbar alƙawari akan duk runtsi kar in yarda in bar yaya na ya mutu cikin wannan kangon azabtarwar dan dama saboda yana raye ake rangwama mai yanzu da ya kusa barin duniyar dole komai ya dawo hannu na in zamewa yaya na komai in cika ma mahaifin mu burin sa"..
  "Sarauniyar farauta shi ya saka min,ya ce min in farauci masarautar Mughal in kuma cika mai burin sa dan sarkin masarautar Mughal ya cutar da shi cuta marar misali kafin ya bar duniya,matar shi sarauniya Zinaida da ke mulkar ƙasar ma ta cutar da shi dan tana sane ta tura ɗiyar ta gimbiya Ondrea tayi zance da yaya na dan a kame sa dama tsanar da take ma mahaifin mu ba kaɗan bane dan bai cika yarda da ƙudirin ta ba da zarar ta ɓullo mai ta nan sai ya kauce har so tayi ta kwanta da shi duk dan ya yarda da ƙudirin ta amma ya ƙi wannan dalilin ne ya janyo mai tsana ƙararar a idanun ta wanda ya zamo har take mai kirarin ko ya yarda da ita ko ɗan sa ya cigaba da zaman bursina".
"Wannan dalilin ne ya haddasawa mahaifi na baƙin cikin zuciya ya faɗi ya mutu ni kuma na nufi masarautar dan nemawa yaya na rangwami daga wun sarauniya Zinaida sai ta nuna min in na yarda na cika mata ƙudirin ta toh tabbas zata sakar min yaya na,toh ni ban san abin da take nema ba sai na nuna mata na yarda zan yi abin da take so"..
   "Ce min tayi zata nemo min hanya mafi sauƙi zuwa yankin Babylon dan in zo in yaƙi duk wasu abubuwan da suka hana a kawo mata wani littafin kundi zata min abin da nake so muddin na ɗauko mata wannan ɓoyayyen kundin wanda ta ce da ni ta gama tsara abubuwa ta kuma binciko inda kundin yake da kuma wanda kundin ke hannun shi nawa aikin kawai shine in zo in fuskanci duk wasu matsalolin da zan fuskanta in ɗauko mata kundin,a cewar ta muddin na mata wannan aiki toh zata sakar min yaya na mu bar ƙasar ta mu tafi mu cigaba da rayuwar mu ba tare da tsoro ba"..
  "A cikin ƴan kwanakin da suka gabata wanda yayi daidai da kwanaki aahirin da ɗaya da mutuwar mahaifin mu na amince da aikin da ta saka ni akan zan yi in ya so bayan na dawo sai in gudu da yaya na amma ni na san ba abu mai sauƙi bane in sato wannan littafin kundin ba dan na sha jin labarai akan wannan kundin da kuma tarihin duk wanda yayi yunƙurin ɗauke shi rasa rayuwar sa yake yi,dan haka amsa mata nayi da na amince ba dan na san zan koma da rai ba sai dan na san in ta ga haka tana iya rangwama wa yaya na amma na san in na fito mutuwa zan yi"..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now