EPISODE TWENTY SEVEN&TWENTY EIGHT

245 28 2
                                    

BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-        
               
 https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
   BAMBANCIN ƘASA
  {Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
  WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:27&28

LADY WITH THE EAGLE WARRIOR AGNETA   Ƙamshi da sanyin da ya doki hancunan su ne ya saka su daɗa maida hankalin su ga ƙofar dan son ganin mai fitowar,da fari wasu bayi ne biyu suka fito kafin su hango riga mai jan ƙasa  a buɗe,takun ta na tafiya da...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

LADY WITH THE EAGLE WARRIOR AGNETA
  Ƙamshi da sanyin da ya doki hancunan su ne ya saka su daɗa maida hankalin su ga ƙofar dan son ganin mai fitowar,da fari wasu bayi ne biyu suka fito kafin su hango riga mai jan ƙasa  a buɗe,takun ta na tafiya daidai da saukar rigar ta matakala,ɗaya bayan ɗaya a tsanake take takun nata har ta ƙarasa saukowa inda suka shagala suna kallon ta har ta iso kan kujerar ta na mulki da isa kuma na ganin baƙi..
 Zaman ta yayi daidai da bugun ƙirjin gimbiya Ondrea dan gani take mahaifiyar ta na iya gane ta,hakan ya sa ta daɗa shigewa jikin Cahal wanda duka tsarguwar ta a idanun Juda dan tana ankare da duk wani motsin ta sai dai tayi kamar bata gani dan kar shirin su ya lalace..

  Cikin ƙasaita ta masu maraba haɗe da tambayar su ko abubuwan da aka kawo masu yayi ko kuma a ƙaro wasu suka amsa mata da yayi kuma jun daɗin su ne tarbar da ta masu,wannan abin ya daɗaɗa zuciyar sarauniya Zinaida dan ta yi farinciki.
Juda ce ta jagoranci jawabin kamar haka
  "Sarauniya Zinaida,ni sunana gimbiya Zarine amma zan fi jin daɗi in kika kira ni da Zarina sakamakon sunan da mahaifi na ya bani kenan,wannan"ta faɗi tana mai nuna Berenice kafin ta cigaba"sunan ta Alyna,ƙanwata ce daga masarauta ɗaya muka fito kuma babbar abu ya kawo mu masarautar ki da fatan zamu yi komai cikin aminci"..
   Gyaɗa kai sarauniya Zinaida tayi jin sigar maganar Juda da bata da maraba da ta gidan sarauta sai ta tuno da yanayin da ɗiyar ta ke magana dan haka ta ce da Juda
  "Na ji daɗin wannan gabatarwar taku sai kika tuno min da ɗiya ta da ta ɓace kimanin sati biyu da suka wuce sakamakon shigo min masarauta da mutanin sarki Sultan Baal-Hamon suka yi,sun kwashe min bayi sannan suka ɗauke min ɗiya ta,my princess"tayi maganar ƙarshe da alamar disappointment ƙarara irin an zalince ta ɗin nan..
Riƙo hannun gimbiya Ondrea Agneta tayi ganin zata fallasa su tun basu taka kashi kwata cikin shirin nasu ba sai ta daɗa yin lamo jikin Cahal tana mai runtse idanun ta har dai ta sami natsuwa..
  Ajiyar zuciya Juda tayi cikin ƙasaita tana mai girgiza kai alamun tausayawa ga sarauniya Zinaida kafin ta yi magana
  "Am sorry and i apology for making you to recall the hard past two weeks"saurin girgiza kai sarauniya Zinaida tayi tana faɗin
  "Kar ki damu dama haka rayuwa take"sai suka gyaɗa kai gabaɗayan su sai Juda ta tambaye ta
  "Toh yanzu ya ake ciki da batun nemo ɗiyar taki"?ɗan murmushin yaƙe tayi kafin ta amsa mata da
  "Babu,,.na bar ta dan na san ganin ta yanzu zai min wahala gashi ban iya rashin adalci ba,ba zan iya farma sarki Baal-Hamon ba da na rama abin da ya min sai dai na saka addu'a a gaba na akan wataran,ɗiya ta ta dawo min"..
  Lallai wannan mata hatsabibiyar kan ta ne ta iya shirya zance,wannan tunani ne da ya faru a zukatan mutani uku wato Berenice gimbiya Ondrea da Cahal yayin da Juda kuwa ta jinjina wa tsari irin nata..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now